falalar yawan ambaton Allah

129 18 0
                                    

Falalar yawan ambaton Allah (azhkar)
Imam Ahmad bin Hambal Rahimahullah, a tafiye tafiyen shi na neman Ilimi dare yayi mishi a wani gari sai ya yada zango a masallaci da nufin ya kwana a nan sai washe gari ya cigaba da tafiyar shi. To su garin ba a kwana musu a masallaci, bayan sallar isha'i kowa ya watse sai Imam Ahmad kadai, me rufe masallaci ya masa magana akan ya fita za a rufe, yace mishi shi bashi da masauki a nan zai kwana sukai ta ja in ja dai har Imam Ahmad ya juya ma mutuminnan baya yayi kwanciyar shi abin sa. Bai farga ba sai ji yayi mutuminnan ya Kama qafar shi yana ja har sai da ya fitar da shi daga masallacin nan yayi rufewar sa.

Ya rufe masallaci ya tafi abin sa. To a kusa da masallaci akwai shagon wani me sai da biredi, shi ne ya nunawa imam Ahmad benci a shagon yace yazo ya kwana a nan. Imam Ahmad ya kwanta sai ya kula da mutumin nan yana ta kwabin bredin shi amman bakin shi yana ta ambaton Allah ne, SubhanAllahi, Alhamdulillah, Allahu Akbar, La haula wa laa quwwata Illa billah, HazbunAllahu wa ni'imal wakil. Har ya gama ya fara gasawa bakin shi yana ambaton Allah.

Sai imam Ahmad yace "Kai Ko a rayuwar ka ka taba neman wani abu a wajen Allah baka samu ba?
Mutum yace "tun da nake a rayuwa ta duk abin da na roqi Allah na same shi banda abu daya, ina son inga Imam Ahmad bin Hambal ido da ido.
Imam Ahmad ya yiwa Allah takbir yace "To yau gashi nan Allah Ya sa an jawo kafar Ahmad bin Hambal har kofar shagon ka!!!!

Aure bautar UbangijiWhere stories live. Discover now