happy

31 2 0
                                    

Haka suka nufi shashin bayi tun daga kofar shashin su zaka tabbatar da lalacewar hakan ta Sanya kafa babu wani kyankyami don ta San in ta biyewa kyankyami ta ba abun da zata yi, hango su tayi wasun au na wanki wasu na guga wasu Kuma na diban ruwa babu aikin da ba suyi tsumakra suke sawa ba dai Kaya kausar ta Gaya ganin yanda suka lalace Bata tabbatar da halin hakula e da suke ciki Sai Jin ihu ynyr da sukaji tuni ta bi inda ihun take zuwa mama hamdiya ta hango da wata bulalar rodi Tana shaudawa wata ynyr Mai shekara 15 duka wata Mai ciki itama ta zo Tana kareta yi hakuri mama hamdiya hakan bara ta sake faruwa Ina Sai Jin tayi an ja bulalar daga hannunta dagowa tayi da nufin masifa tayi gamo da gimbiyar matar yareema tuni tayi Tsit ido ya Rena fata wani kallon tsana kausar ta Mata mama,mama hankali ta mayar inda ake Kira mama hango matar tayi alamu Tana cikin azaba ga ruwan alamun her water has broken ba Wanda ya yunkuri taimaka Mata da sauri ta iso jakadiya na son mgn kausar ta daka Mata tsawa Mai kuka tsaya ku Kira likita kame kame take can taji jakadiya tace ke mama hamdiya Ina unguwar zoma kausar tace Ina likitan da yake kula da ku tuni mama hamdiya da jakadiya suka zaro Ido daka musu tsawa tayi ,muryar yarinya taji ai babu Mai kula da mu da sauri ta dau wayarta Kiran Ali tayi Amma d line ur calling x not available Isa ta Kira sukayi mgn cikin mintuna ashirin ya iso aka basa izinin shiga aka kawo sa har inda take su uku ne mace guda biyu da Shi isowa yayi gimbiya sun iso ,tun dazu suka shigar da ita Dan karamin dakinta ba abun da take ji Sai hakinta Mata guda biyu tuni suka shige daki bayan30 minutes kukan jinjiri ya Fara zuwar musu Sai da aka gyara sannan aka Basu izinin shigowa ai da sauri kausar ta shiga ta iso gurin jariryar Fara Kal mace in ka ganta zaka rantse ba Yar Nigeria karba tayi daa hannun nurse din ta ringumo ta sannan nurse tace a kawo Kaya anan ake drama don kuwa wani kayan suka kawo da Shi da babu duk daya ,kausar tace dama baki yiwa yaron tanadi ne sunkuyar da Kai uwar tayi tace ban da halin yi shiyasa wani barcin Rai yazo wa kausar iya wuya Kamar Yaya ,rashin biyan mu yasa na kasa siyawa diyata Kaya ta cire idonta daga mama hamdiya Wanda take Mata alamun da tayi shiru ,juyowa kausar tayi gurin jakadiya tace in na fahimta dai jakadiya baku biyan bayi ku ,na wani wata nee ba a baku bah shekara biyu Kenan ,biyuuu meh mama hamdiya tace keh harira Fadi gaskiya dai ba kwanaki fulani ta babba ku albashin ku tace ah,ah ba dai mu Kam , wani tsaki kasa kasa kausar tayi tace Ina mijin naki tace Yana gadi a kofan toh ba Sai ku je a Gaya Masa bah ynyr ta amsa ai baba baya dawowa Sai bayan kwana biyu Sai gobe zai dawo jinjina Kai tayi mgn sukayi da nurse ta fice Bata Dade ba ta dawo da leda daya babba irin na shopping bude kayan tayi kayan yara ne kala shidda socks Shima shidda da pampers ,hanky, power da showel guda biyu ai a take harira ta Kama kuka Tana Mai gode Mata sallama tayi bayan ta tabbatar an kawo Mata kunu Mai kyau da abinci ta fita tare da alkawarin dawowa sannan ta sallami Isa Shima shashin ta ta nufa wanka tayi sannan ta Shirya cikin Riga da wando da karamin mayafi ta zauna Akan dinning Sai da ta ci ta koshi ta tashi ta hau Danna computer hankali a kwance.

Jakadiya ne gaban fulani Fara wacce take Bata hakuri ,wlhi ban so taje Amma ta dage Sai taje in ba haka ai uwar gajiyata kinsan zan sanar dake bla bla bla sallamar ta fulani tayi bayan gargadi da ta Mata .
Mami kuwa tun da abun da ya faru ta daina Jin Dadin rayuwar Nan su ummi sun gane hatta da malamanta duk kowa ya tambayeta Sai da tace ba komai ya mlm Sadiq ya tare ta shine malamin da suke soyayya sama ,sama Shima bai wuce kamin sati faruwan haka ,nuni ya Mata da su shiga office idinsa Amma Ina taki shiga Sai da ya nuna Mata karkashin bishiya ta yarda ,gyaran murya yayi yace Mami meh yake faruwa ,akwai abun da na Miki ba daidai ba ,akwai abun da ke damunki tell me I will solve ur problem anything Dan Allah,juyar da fuskarta da ya cika da Hawaye tace ba abun da ke damuna mlm Sadiq yace ba ki Fadi gsky ba ya Zaki ce min ba abun da ke damunki bayan grades idinki sun yi kasa Kuma kallon ki kawai na tabbatar kina boye min Abu ,kayi hakuri babu yace shikenan mami Zaki iya komawa class da toh ta amsa ta Fara tfy wani hajijiya ta Fara ji kamin a Ankara ta Fadi a kasa Allah ya so ta filin yashi ta fada da sauri ya iso ta dago ta yayi cikin tashin hankali kawayen Mami da Suma suka hadu da Shi suka biyo bayansa da wata class mate motar sa ya hau Mai gadi ya bawa sako ya gayawa principal tuni suka nufi khamis hospital kasancewar antyn sa na aiki a filing karbarta akayi suka wuce da ita kusan 2hrs n hango muku mlm Sadiq ciki dai impossible anty Sai dai in kunyi misplacing da na wani tace kaga Sadiq tsaya kusan 2test nayi akanta sannan Kamal yayi ya fito postive don haka da ka yarda da Kar ka yarda x ur own problem ,yace Amma anty zan iya Miki rantsuwa na San Mami bara ta aikata irinin abun Nan and again Bata da aure Haba ai a kunne classmate dinta da kawaye suka hau Kan mgn ,Sadiq Dakyar ya lalubo wayansa ya dannawa Usman ya Kira Usman ya sanar Masa anyone admitting din kanwarsa zuwa asibiti,Usman dake tare da Yusuf suna tattauna ya Samu Kira daga manemin mami ai Yana Jin abun da ya fada ya tashi Yana Mai Masa sallama Yusuf ya tambayesa meh ke faruwa sannan ya sanar da komai toh ba damuwa muje suka iso asibiti Tana barrci a lokacin ba a bukatar a shigo Mata yasa Yusuf ya Masa sallama Shi Kuma ya nufi office din likita samun Sadiq yayi Yana Hawaye subuhanallah ya fada lfy share hawayensa Sadiq yayi ya Mika Masa littafin ji yayi zuciyar sa ta Fara bugawa bude wa yayi a hankali ba inda yake gani kamar 2weeks pregnant ,ai tuni ya yarda paper Yana salati yace Sadiq ka min bayani yanda zan gane Sadiq ya bayana Masa komai Jan kujera yayi Yana Mai furta inalilahi wa inailliahi rajiun Hawaye ya sauko Akan kumatunsa Karin bayani anty ta Masa ,tuni yaji kariyar zuci da wani barcin Rai har Mami ta San Dadin namiji da zai dirka Mata ciki,ciki,Wanda suka tafi asibiti suka dawo ai tuni mgn ta yadu mami tayi cikin shege Kuma ba a San uban habawa tuni mutane suka Kama comment abun ya dawo latest. Ummi tuni ya Usman ya Kira ya Mata kwatacen tunda ta fito anguwa ta lura da kallon da mutanen anguwa ke Mata Amma ta share bayaninsa da ya samu kafewa tayi na mintuna Sai da Usman ya zaunar da ita fashewa tayi da kuka tace Usman meh nayi meh na Gaza a tarbiya Mami ,mami har ta San ta tare a gun namiji har ya Mata ciki tashi tayi cikin zafin nama ta shigo dakin yayi daidai da farfadowar Mami haba nufarta tayi da nufi dukanta Usman nee ya riketa ah,ah ummi kiyi hakuri muji ta bakinta in Rai ya barci hankali Bata gushwa Dakyar ta lalabata Ido Mami ta zubo musu kamar doluwa can taji muryar Usman radau ya amsa dakin mami ,naam ta Gaya kasan muryan Ina son ki fada min gksyr ki tsakanin da Allah wa ya Miki ciki ,ciki ta furta Tana zaro Ido tace ai ciki na cin abinci ne ryt.shut up Ina nufi wani namiji Kika bawa kanki kuka yi Zina Wanda ya bada sakamakon ciki zaro idonta tayi Tana kallon jikinta ta taba inallilahi wallahi yaya banda ciki Yar Mata takardan yayi a fuskarta karantawa ayi Tana girgiza kanta na rantse ki min shiru Kar kisa in zo in Miki duka anan,Yaya kaji wallahi mistake ne ,ummi tace mistake fah Kika ce wallahi Mami in za Amin rantsuwa wannan ranan zata zo zan karya ta ke da nake gani ko na sa Miki hannu a baki bara ki ciza bah,wallahi Ina tirr daha....ah,ah ummi Kar ki Mata baki girgiza Kai ummi tayi Tana rike kanta Wanda ke Sara Mata yace tashi ummi in Kai ki gida sannan ki huta haka kuwa akayi suka barta ita daya cikin tashin hankali da kunci Sai da ya tabbatar ummi ta kwanta sannan ya komo hospital ,mami yanzu Kam kuka take kamar ranta zai fito,wallahi Ina Dana sanin wannan bakin dare da baran ta ba mantawa bah,a da tabo daya nee a gareni ya zu ta zamo biyu ya allah ka dauki Raina da gaggawa Tana fashewa da kuka Mai ban tausayi ,shigowa ya karasa yi dagowa tayi tace Yaya ka yarda wallahi baran taba aikata abunda kuke cewa ya e naji yanzu Ina son kiban labarin abun da yafaru a bakin darwn ,,bakinta rawa yake yace ki Gaya Koh so kike ummi ta Kara fushin da take da ke gigiza kanta tayi sannan ta sunkuyar labari ta Fara basa tun daga farko dawowarta daga asibiti da rapping idinta da yusuf yayi inalilahi ,ya fada ,yace meh yasa baki fada min we, cikin muryar kuka tace bana son hankalin ku ya tashi yace ai gashi Nan shafa sumar kansa yake Yana zagaye dakin ita kuwa ta rungume jikinta haka ya wuni da ita Yana neman mafita sannan ya tambayi sallama aka ce Sai tayi kwana uku don Tana bukatar bed rest Shima za ta yi sati2 a hakan .
Mutanen Singapore kuwa tuni sun iso karfe goma da rabi na dare suka sauka a hotel idinsu Wanda dama an Kama musu ,wanka yayi ya huta sannan ya duba time 4:30ne Kenan 10 yanzu gajiya yayi yasa yace zai Kira ta gobe bayani Rama salolinsa da yayi ya fara gyara kayansa idonsa ne ya sauka akan kayan dadi da ta masa murmushi yayi sannan ya girigza kai feidgw ya kai ya debo wanda zaici sanda ya koshi ya Lula barrci hankali kwance.ummul kuwa har karfe Tara da rabi baby na tare da ita sallama sukayi bayan tawa momy Sai da safe kule shashin ta tayi wanka tayi ta Sanya rigar ta cotton ba nauyi kwanciya tayi a bed idinta juyawa ta ringa yi daukan phone idinta tayi Tana dubawa Amma wani kewarsa ke damunta tun Tana duba wayan har tayi barrci dama ga gajiya ba ta tashi Sai bakwai da sauri ta sauko tayi wanka da brush tare da sallah ,shiri tayi cikin dogo Riga chiganvi ta Sha dinki dogon Riga ta sama yadan kamata kasa Sai ya sake shiryawa tayi ta yafa gylenta sannan ta fita dakin momy ta nufa sallama tayi aka Bata izinin shigowa momy da baby a zaune ah ah, daughter kin tashi tace eh mommy ta sunkuyar tare da gaida ta amsawa tayi Tana tambayar lfyr ta alhamdullah ta amsa tace toh yayi kyau breakfast suka je sukayi sannan momy ta musu sallama ta tuna musu yau suna da paper zasu Fara da marketing da toh suka amsa karfe goma suke da Shi don haka tara da rabi ta Gama shiri ta kulle shashin ta wayarta a jaka sannan suka fice suka bar sakina ,a skull din kuwa tun kab su shiga tuni kowa yasan da amsa bai bada wuya don haka sukai wannan a takardar su sukayi summitting, yau Maryam Bata zo bah don Bata subject din da aka Gama ko wani guntun Tom &Jerry na neman yiwa ummul mgn Amma ko ta kulasu mAh haka suka wuce ta kofar gidan su a hanyar dawowa kamar tace Mata ta ajiye ta Amma tasan Bata Isa hakan bah. Suna shiga gida parking sukayi karar music nee ke tashi ita da baby kallon kallon suke har suka shigo kawayen sakina ne Kuma su hudu Mata uku namiji dayaa cire Ido tayi tayi upstairs abunta Tana lura da kallon da namijin ke binta Koh a Taran ta a kasan ranta ta Fadi Dan iska kawai .wanka tayi tadebi samosan da tayi da sus ta ci ta koshi tare da hamdallah cire rigar tayi sa wando da singlet ta fada Kan gado Tana kunna wayarta Danna watssapp take Amma har yanzu bai yi mata mgn chatting take da Maryam Kira ya shigo ba lambar Nigeria ya tsinke Sai da yayi kamar 20 minutes Sai da ta kusan tsinkewa ta daga sallamu alaikum ,can shiru kamin a amsa wamin aliaikum salam yahabibaty ta gane muryarsa gyran kwanciya tayi Kan gadon sannan ta rungume pillow uhmm,yace uhmmm ka iso lfy a zaune yake Akan gadon gefensa ya ajiye laptop idinsa Yana gyra zaman wayan a kunne , meh kike yanzu ,uhmm Ina kwance kawai yace I'm missing you ,so do you miss me murmushi tayi Sai kace Tana gabansa tace kadan yace uhmm ai at least na samu gurbi kadan so Hawa ur exams tace alhamdullah meh kukayi yau marketing tambayoyi ya ringa Mata Yana Bata labarin seminar su kusan 30 minutes sannan sukayi sallama juna. Yusuf tun ranar yaje anyi arrangement rahma yasa aka ja ma Rebecca kunne ai tun antyn rahma ta gansa ta shigo taitayinta Bata manta Marin da ta Sha a gurin sa lokacin da ta daketa ta Kuma hanata xin abinci ta ai ranar taga azaba ,ai Yana tfy ta Kama jibgar Rebecca Tana ja Mata kunne ba ruwanta da rahma .
A gefen Yusuf kuwa tun ranar da abun ya faru yake Jin guilty ga abun da ke faruwa ko wani barrcin sa Sai yayi mafarkinta ya rasa ya zai yi da ransa dawowansa bayan ya sauke inspector Usman a asibiti gidansa ya nufa wanka yayi sannan ya sama waa cikinsa indomie ya ci yakoshi sannan ya hau aikinsa . Chatting tayi kadan da phone idnta sannan barrci ya kwashe ta Sai da Ana Kiran sallar asubah sannan ta tashi wanka tayi tayi sallah sannan ta koma barrci yau Bata da paper don haka tabi lfyr gado ba ita ta farka Sai 11 da sauri ta wanke bakinta talale fuskarta tare da gogewa.kiran sa ya shigo layinta wifey kin tashi lfy alhamdullah gyara zamansa yayi Yana Mai cire socks idinsa don dawowar sa Kenan daga meeting how are u doing alhamdullah da fatan there x no problem tace Masa eh babu ,Ina kake am hearing noise muna attending wani seminar kusa da hotel tace toh Allah ya bada saa abun da aka je nema ya su Mami they are fine shiru tayi Shima da ya rasa abun cewa ya kashe wayan kawai.shifa yana mamaki a da Yana kallonsa miskili Amma ya gane ummul ta fisa miskilanci. Kausar Kam da yamma kamar yanda ta fada ta dawo ta Dan Jima Tana lura da irin rayuwansu hatta filin da ake musu abinci duk ta je ta duba ba Kyan gani a gsky suna wannan masarauta ta Tara Amma ba dai adalci kam

magajin sarauta 2Where stories live. Discover now