14

36 2 5
                                    

a gun su tsohon sarki Mai martaba da Kuma sulthana tunda suka iso London har yau Babu wani Shirin dake tsakanin su yarasa meh Yake damunta duk da Tana da tsanani Amma ai sun tattauna matsalar su and sun sasanta komai nasu a saninsa booking apartment Daya sukayi har da su waziri ganin Haka ya Kara kular da sulthana
Inspector kuwa rayuwan jail din Yake ba laifi Yana samun kulawa Kuma ba a hada shi da sauran mate idinsa ba wani daki dai Dan daidai aka kaisa su kawo masa abinci da ruwan Sha daidai duk zaman da Yake a prison daidai da Rana Daya kullum tunanin nihat yake da Yan biyunsa Yana kewan su sosai Yana Kuma son su Bai yarda ya kirata don yasan tada Masa hankali zata yi suna mgn da daddy da Kuma yareema sai barrister raheema sannan Ana kawo Masa lafiyayen abinci daga gidan daddy da Kuma yareema ..huccii ya sauke Yana Danna karamar wayar dake hannunsa ya Kara a kunne good evening sir aka Gaya a dayan gefe amsawa yayi how was ur journey ..........sun kusan 20 minute suna mgn daga Kai inspector yayi wato dai yanzu ya Gane ba makiya Daya zuwa biyu Yake da shi ba Don Haka dole yayi hattara ga Kuma pending case da za a fara na mahmud Haka jibi za a fara .
Summaya zubawa celling tayi ganin Kiran Samantha secetaryn momy ya sa ta amsa bayani da ta Mata yasa komai nata ya tsaya cakk mahaifiyarsa na ICU bayan harin da aka Kai Mata a gidan ta jiya Wanda an kashe bodyguard uku da gate man da sauri ta fito Bata ma lura da yanayin dressing idinta ta fice motar ta ta bawa wuta.atika dake boye ta Danna wayanta Tana murmushi boss ta fita mgn akayi sannan ta kashe wayan Tana dariya. direct asibitin ta nufa har an fita da mamanta kebewa sukayi da doctor Wanda ya Mata bayanin da coma da mamanta ta shiga break down summaya tayi she can't take it ban baki likita ta Bata sannan ta fice don Tana da sauran patient hannu na rawa ta Kira Jamila Amma Bata daga sake dannawa tayi aka ce Mata switch off hawaye na sauka Akan kumatun ta what is happening to her why now tayi Kuka harta godewa Allah a waje ta tsaya Tana kallon mahaifiyarta abun tausayi iman da yazo Yana lallashinta Yan uwanta Kuma duk suna hanya Amma ba Wanda ya iso .
Raudat ce zaune idonta yayi jajair fuskar ta ma hakan alamun ta ci kuka .tunda safe ta zo ta tadawa itayenta hankali Babu wani bayani shigowar Abdullah da daddy ya Kira gaida iyayensa yayi sannan ya juyo gun raudat ke lfy ya Zaki so kina sasu a gaba kina musu kuka ko baki San kin girma ba bana Kuma hanaki zuwa gidan Nan ba hawayenta nee ya tsaya cakk ya sakeni shine kawai kalamar da ta furta iyayensu Mata nee suka dau salati ummi nee tace saki Kuma raudat meh yayi zafi meh Kika Masa Babu ummi ba abun da na Masa tun lokacin da na bijirewa umarnin ku na fara tabewa ummi tunda na haifi Abdul Banda kwanciyar hankali yau muna wannan asibiti gobe muna wannan asibiti kasancewar sickler babansa ya fita harkar mu ya daina kulawa da mu Abu hanif sai ya tafi wata uwa duniya yayi wata daya Bai Kira Bai Kuma ajiye Mai duba lfyr mu nakan daure na shnaye in na tuna yanda nayi na aure sa bayan tfyrsa Russia ya dawo da wata baturiya wai ya auro ta acan Susan sunanta dagowa kowa yayi a parlour ban Fadi wa kowa na cigaba da zamana kasancewar ya raba Mana gida munyi tashin hankali Amma ganin da nayi Bai damu yasa na sauko kusan 1 year suka samu matsala da matan bayan 6 month Allah ya Mata rasuwa ya dawo zaman gidan mu ya cigaba da Zama tare da mu Abu hanif baya sauke hakkina dake kansa kawai In gari ya waye ya ajiye Mana kudin bukata ya fice Bai dawowwa sai karfe Sha Daya da farko na fara Kai Kara gidansu Amma da na lura da suna goyon bayansa yasa na hakura na daure na cigaba da Zama dashi ban Kuma taba gajiyawa ko nuna gajiyawa don Dana Abdul ,Abu hanif ya sakeni sakamakon neman saki da nayi don Bai wuci lokacin bikinsu ummul na Kama sa sa karuwa Kuma Yar uwarsa Akan gadon sunnah na nayi kuka da na Kai Kara aka ce ai sharri nake Masa Yan uwansa suka tura min maganganu marasa Dadi kullum in nazo da niyyar Gaya sai naji kunya in na tuna irin bijirewar da nayi a wancan lokacin shine dalilin da naki komawa gida sai da ya Abdullah ya koro ni na dawo yayi ta lalashina da min dadin baki bayan sati still na kamasa suna video call da wata jiya dai ya sake shigowa da wata Yar makwabciyar mu Maryam shine na tuburbure Akan banzan iya aurensa ya sakeni shine ya min saki uku bayan cin mutunci da yamin da Kuma Gori Akan na kasa yiwa iyayena biyyya nabi sa .. sunkuya tayi on her knees Tana rarrafe ta matso daddy kayi hakuri daddy na tuba na Gane ,nayi hankali bazan sake ba wallahi Koh Mai bola ka auro min zan zauna da shi zan masa biyyayya tausayin anee ya Kama su ya Isa Haka raudat dama ance u never learn a lesson sai kayi mistake din don Haka na yafe Haka Tana rarrafe ta nemi yafiyan kowa Abdullah Wanda ransa abace yace saki nawa ya Miki uku ta Gaya gyada Kai yayi Ina Abdul Yana gun nihat toh Allah yasa u have learn a very good lesson Sai ki fara iddanki da toh ta amsa sallamar a akayi sama ta hau ta dauka ita abar tausayi ce sai da ta shigo ta hango nihat a kwance akasa bakinta duk a bushe anty bilki tayi da ita taci abinci taki ga yaranta da suke bacci budewar kofar yasa hankalinsu ya dawo kanta gaida anty bilki tayi suka gaisa da nihat da kyar sannan ta wuce dakinta a shashin ummi Wanda tasa aka fara Mata gyara Abdul ya biyo ta Akan gado ta kwanta Tana shafa gadon bayan yaron har barrci yayi awon gaba da shi ba abun da take tunawa kamar shasha kawai ke raudat kin dauka Ina sonki ne toh Bari kiji da babban murya ada na soki shima bazai wuci na surar jikin ki Amma ko shaawar ki bana yi ba Kuma ba sai kin roke ni ba na sake ki don bana iya Zama da Wanda bana son ga danki if u like u leave him in kina so ki tafi da shi sannan ya Bata saki ukunta ....lallai ba duniya abun tsoro ce a yanzu zata iya bada labari Akan yaudara irin ta maza .
Zahra ma yau still bugar da ita yayi bayan fitarsa Mai gadi dai dake ankare da rashin fitowar matar gida kusan sati jikinsa a sanyaye da zaran ya nufi Mai gidan zai tambaya sai maganar ta subuce ai ko ba lafiya ya kamata yaji ya Kuma ga alaamun Haka don Haka yau bayan ya kulle kofar gate din ya nufi cikin gida sallama ya ringayi ba a amsa ba har ya juyo zai tafi wani zuci yace ya leko ya duba Yar mutane wanda take da mutunci don kullum in tayi girki sai ta sa Masa a kula Mai kyau Kama handle din kofar yayi Amma a rufe shifa tabass yasan madam na gidan kai dai akwai abun da Mai gidan ke boyewa komawa yayi filin zamansa yana yi Yana tunanin tuni ya fara zargi akan Muhammad dama kwanaki Kuma yakan kawo Yan Mata Wanda yasan ba dangi uwa bare uba .
Tunda akayi bude baki ta shirya kamar yanda ya Fadi Mata abaya golden ta saka Mai kwaliyan stone har kasa da hula baki da gyalen sai karami jaka da takalma sauka tayi yau daddy ya tafi kaduna duba matsala a construction idinsa momy ta tarar da shi suna mgn Akan zuwan afiya kanwarsa Yana kallonta ya fadada murmushi a fuskarsa momy tace ah,ah daughter har an shirya nee daga Kai tayi cikin kunya abinci ya Kara cokali uku akai yace ya koshi tare sa kurbar ruwa Bari naje na shirya Ina zuwa da toh ta amsa Hira suke da momy sauka yayi cikin light ash da royal half shoe ga fararen kafafunsa mun tafi momy toh ku gaida su duka Kuma samamin ki da toh ta amsa masarati suka hau ya Bata wuta slow music na korede romantic nee Yake tashi anguwansu Mami suka zo bude musu kofa Mai gadi yayi sannan sukayi shashin momy suka nufa ai da sauri ta tarbesu suka gaisa sannan suka wuce part din su Mami kwankwasa kofa sukayi Mami da ta tashi don dubawa mvn ya rada Mata Alan kayan jikinta wucewa tayi ya bude kofar mumusui a shimfide a fuskar sa ya musu iso barka dai ango da amarya murmushi sukayi hauwa na kunya tayi Zama sukayi a 2 seater ya manna Mata kamar cimgam Mami ta fito ga cikinta da ya fito rasa abunsa ganin su hauwa yasa farin cikinta karuwa gaisa sukayi da majah , mjin Mami da kansa ya kawo musu drinks da abun sarafawa don acewarsa ta gaji daga Kai majah yayi kawai Yana Masa kallon Dan iska kawai dakin rahima suka nufa anan suka sabon Hira Mai Cike da nishadi karfe Takwas sukayi sallama don zasu shiga cikin gari sallama sukayi ba Don sun so ba ,motar suka shiga Ina zamu ta fada don kawai ya Gaya Mata gun su Mami zasu je kawai murza stairy take hannu Daya hannu Daya Yana shafa sajensa sake tambayarsa yayi yace Zaki gani ai in mun iso anguwansu taga sun nufa daga Kai tayi parking yayi a kofar gidan Inna suka fito sallama tayi ta shigo Inna dake kallo Jin sallamar kamar ta hauwau yasa ta leko ganinta yasa ta tashi da sauri ah,ah lfy daddare Nan wani Abu nee ta faru murmushi kadan tayi Babu dama Mai gida nee yace mu zo gaida ke ai washe baki Inna tayi ,ah ah ki Masa iso izinin shiga ta basa gaisawa sukayi da Inna Wanda sai tambayoyi kawai take zuba da zasu tafi dubu goma ya ajiye Mata ai farin ciki taji har bakin motarsu ta rakasu sannan ta shige duk abun da tayi Bata burgeta ba a kofar gidansu sukayi parking suka shige shima an basa izinin gaisawa sukayi da mama itama ganin yanda Yar ta ta cika yasa taji farimciki sosai Yar Hira sukayi Tana tambayarsa ya momy amsawa yayi lfy sun Dan Dade suka Mata sallama Akan zasu shiga shashin Abba sallama sukayi a shashin Abba Wanda ya tasa hah hadiza Yana ciyar da ita abinci Jin kamar muryar jidda yasa ya amsa itama haj hadiza ta zubawa kofar Ido shigowa tayi Abba na ganinta tuni yaji wani faduwar gaba Kar dai an sakar Masa ynyr Amma da jidda ta cuci kanta ,gyaran murya tayi don yanayin zaman nasu ,Abba tare muke da bako toh ai sai ki Masa iso kofa ta Masa zare takalmansa yayi tare da sallama ya bude kofa Abba na ganinsa ya Kara gyara zamansa Haj hadiza zuba Masa Ido tayi wannan ba yaron da...Kuma ai Dan Haj zahrau nee ko meh ya hada su ooh gaida sa majah yayi sama ,sama sannan suka gaisa da Haj hadiza wacce Daya biyu sai ta sako bakinta Akan zance ganin time ya tafi suka musu sallama biyo su Abba yayi ya Kara musu nasiha sannan suka biya mama suka Mata sallama sannan suka fice tafiya suke yi ,duba time tayi 9:30 barrci nee a idonta ba har ya fara rufewa har ta Dan zame hulanta ma shima ya zame kallonta Yake cikin burgwea tuki Yake Yana kallonta har suka iso gida parking yayi ya ce to shige don sai da yayi sallama da masu gadi ya tabbatar komai a kulle sannan ya nufi cikin gida su daddy sun shiga don Haka kulle kofar yayi ya kashe wutar sannan ya nufi dakinsa wanka yayi sharp,sharp ya fito shiryawa yayi cikin wando three quarter Mara nauyi ya fess jikinsa da turare ya yafa jalabiyarsa a kafada wayansa Yana hannunsa Yana dannawa bakin kofarta ya bude a hankali ya shige ,duk hankalinta nakan kallon wani Nigeria film a Netflix sugar rush Bata ma ji karar hawansa kan gado sai Jin Ana Mata tafiyan tsutsa a wuyanta a tsorace ta Yar da wayan a kasa pass Kuma Babu tantama wayar ta phaseh zata Masa ihu da sauri yasa hannunsa ya rufe bakinta babe nine fa ya Gaya juyowa tayi Jin muryar majah a kulufe ta cire hannunsa daga bakinta ,ranta yayi baki ,hararsa tayi juyowa tayi ta sunkuya don daukar wayanta a zafafe taji ta fada kan jikinsa ja musu bargo yayi ya kashe wuta,yau dai ya rage zafi a cewarsa,hawwa dake gefe sai boron kunya take Masa nifa bana son iskanci ka tashi ka tafi kar momy tazo ta sameka a dakina ,gira Daya ya daga Mata Yana gyara kwanciyarsa matso ta yayi rada Mata yayi a kunne tuni ta zaro Ido kashe Mata Ido Daya yayi yace mu kwanta kinji in ba so kike na makara don ke Kam katuwa ce ana azumi kina zuba Loma cikin kunyar maganarsa ta rufe Ido eh Mana ni Kam bayan sallar da kwana biyu zan sa ranar tarewar mu in ba Haka ba sai dai aji kin haihu ya fada ko aikinsa buga chest idinsa tayi sai na gayawa momy yace kije Mana dama ai aka auramin ke Kam suna tsammani zan zuba maiki Ido nee they should stop dreaming tunda anyi babban dauri aure .ni dai sai da safe ta Gaya pecking ya Mata bayanin adduar da ya shafa musu asubah ta gari.
Tsalakowa tayi a hankali ta fito Mai mashin din tattarar a gun tfy suka Kama har suka iso destination idinsu masu gadi haska musu torchy sukayi fito da bindigarsusuna sukayi Mai mashin din ya janyo su gefe suka tattauna mgn suka Mika musu Abu a hannu sannan suka musu hanya har gaban wani daki bude sacatar sukayi Haj toh na gode ta Gaya bude kofar tayi . inspector Wanda Yake karatu littafin ahamdu Bello Jin karar bude sacatar yasa ya tsayar da karatunsa mgn da yaji Ana yi yasa ya taso cikin sanin yanayin Kare kansa ya tsaya a bayanta kofa bude kofar da akayi yasa ya saita mutumin tufafi mace ya hango Wanda Tana rufe kofar ta juyo gareshi bummm zuciyarsa ya bugu me ya kawo NIHAT jail ai Tana kallonsa da sauri ta rungumeta kamar zata maida shi cikinta tsayawa yayi kusan30 sec sannan ya farka zameta yayi daga jikinsa yace nihat meh ya kawo ki da wa Kika zo Ina Kika bar min yarana duka Yana tamabayarta a jere hawaye dake bibiyar fuskarta ta pale nayi kewan ka ta Gaya Kare Mata kallo yayi tabbas ta rame ta rage haske Jan hannunta yayi ya zaunar da ita Akan gadon yace Nima nayi kewar ki yanzu Gaya min dawa Kika zo Abdullah nee ya kawo ki ko muazzam girgiza kanta tayi toh da wa Kika zo wani nee na biyashi Akan ya kawo tuni yanayin fuskarsa ta canza kamar yah ki min bayani ,tuni taji tsoro ya darsu a ranta ganin yanda ya zubo Mata Ido yace ba..ba daddy nee mace ya kawo ni shine yaki nayi kuka jiya ma suka dura min allurar barrci wai bp na yayi sama ...shine yau Ina ....Kika yi meh nihat shine wani Wanda Yake kasan layin mu na mishi mgn yau zai kawo ni Nan Amma sai daddare zan basa dubu bakwai , uhmm nihat kin kashe ni Ina Kika baromin yarana da wannan uwar dare Zaki gudu daga gida don wannan guduwa kikayi daga ladder fa Kika fita baki tsoron wani Abu ya faru da ke jego fa kike yi iyee Yana daka Mata tsawa tsorota tayi Amma Bai Hana ta turo baki Amma ai jinin ya Dena zuba Kuma ai don anki Bari na ganka shiyasa fah ,naga kaikam bakayi kewata don baka Sona Koh don hada mu akayi Koh Ta fada hawaye na sauka a idonta Tana gogewa haba nihat yanzu dai were are my children suna gida suna barrci suna gun anty bilki da momy gyada kansa yayi ransa a hade sassauta murya yayi yace yanzu akwai Wanda ya San kin fita girgiza kanta tayi uhmmm nihat kenan har yanzu baki San kin girma ba Haka last year Kika dirka wai kinje ganin saurayi bazaki girma ba ur a mother right now na dauka in kinyi labour da kanki Zaki San zafin kanki ,toh shikenan Bari na koma gida mayar da ita yayi kan gado yace ba Haka nake nufi ba Yana shafa giararta da suke baki wuluk sorry kinji nine koh very soon zan fito ya babies idina ya fada suna nan kalau ta fada ta makalkalesa kamar mayya ,gyara zaman takardarsa yayi. Fita yayi can anjima ya dawo kulle kofar yayi da asubah mugu zai zo ya dauke ki and don't try any nonsense like Dix again in makiyana sukayi gamo dake fah meh kike tunanin illata ki zasuyi turo baki tayi Tana cire habban hijjabinta kayan barrgci robe nee a sama cire shi tayi Riga da wando nee a jikinta kanana tsura Mata Ido yayi Cike da mewar ta shima kan gadon ya hau labari take basa labari ya canza salo don cafke bakinta yayi suka faranta ransu Amma basuyi babban ba wanka sukayi sannan ta mayar da kayanta barrci yayi awon gaba da su .
Yauma sai da ya dandana Mata azaba sannan ya fito kusan karfe Daya don Kiran gaggawar da ogansu ya mass fita yayi da sauri ya manta ya bar key a kofar ya fice da motarsa Mai gadi da ya zuba Ido sai da ya tabbatar da yayi nisa sannan ya nufi cikin gidan zuciyarsa na wani bugawa tare da addua ya Kama handle din bayan ya dannan makuli kofar ta budu kunna wayarsa yayi don tun da dadewa ya fara zargin ogansa na wani aiki Wanda ba Mai kyau ba Amma sanin da yayi babu kyau zargi yasa ya share Amma yau ji yayi zuciyarsa a bushe Yana son ganin ko menene Yana bude kofar bayi ba komai daki na farko shima ba komai dakin hajjiya yayi ya dudduba komai ba kowa sannan ya nufi dakin alahji Wanda Yake a rufe har zai tafi ya hango kofar karshe ya nufi kofar tun daga Nan Yake Jin numfashin da karfi taba kofar yayi Amma a kulle dai numfashi nee na tashin hankali tuni ya rikice aljihun sa ya lalauba sai ga zaren dinkinsa na hula da sauri ya saka cikin sa'a kuwa ta budu bude kofar yayi zuciyarsa nee ta bugu hango mutum a owance mace Kuma kamar gawa ,zuciyarsa na rawa ya iso hango matar gidan a cikin wannan tashin hankali yasa zuciyarsa ta bugu da sauri ya sunkuya hajiya ,hajiya dakyar ta bude idonta Wanda suka kumbura ado ta fada naam hajiiya nine taimakamin mu gudu Muhammad mugu nee yanzu hajiya alhaji nee ya azabtar dake Haka daga Kai tayi Bismillah yayi ya taimaka Mata ta taso suka fito tfy take kafafunta na rawa kulle kofa sukayi adaidai shashinsa tace ka dauko kayanka mu tafi don nasan in ya dawo ya tarar da Kai Kuma bana Nan kashe ka zaiyi,ai tunda ado yaji batun kisa tuni ya shige da sauri ya dawo da Kullin kayansa sukayi waje gashi ba kowa a hanya tfy sukeyi dai har da Dan gudu Kar ya dawo ya samesu suna Shan kwanar karshen kwalatar fitar da su daga anguwa kenan motar Muhammad ta wuce ai hankali a tashe Mai gadi da ya hango wucewar mota yace Haj daure dai mu tafi da wuri kasawa tayi Haka ya daukota suna Tfy suka iso wani anguwa shima shiru a gajiye suka zauna kan dakalin wata shago hajiya lah Kinga na manta da abun turawan Nan kawo numbern Yan gida sai na Kira zuciyarta na Cike da wasiwasi tace Banda shi toh Haj baki da number wani kowata Wanda Kika sani akwai Danna number akayi ba adade aka dauka hello amsawa yayi ado sannan ya mikawa Zahra Wanda dakyar mgnr ke fita yanzu Ina kike suleja street toh Dan Allah karki tafi gani Nan zuwa da toh suka amsa zuciyarsa Bata daina duka ba in har Muhammad ya kamasu toh kashinsu ya bushel .
Gurin Muhammad Kuma mgn suka tattauna Akan business idinsu Wanda an kusan Kama su kusan hour Daya yayi sannan yayi hanya gida zuciyar sa na Masa DACi ya rasa Mai yasa isowa yayi horn yayi Amma ba abucd kusan sau biyar Yana yi ba amsa sauka yayi ransa na tafasa zai buga kofar sai gashi ta budu a hankali Yake tfy ado ,ado shiru Babu ado leka dakin yayi ba ado bayin ya leka shima ba ado da sauri ya nufi cikin gida hango key da yayi jikin kofar yasa yanzu ya tuna da ya bar key ajikin kofar budewa yayi ya kunna wuta ba abun da aka taba dakinsa ya nufa a kulle leko dakin mutt din can yayi shima ba a taba komai zuciyarsa na buga ya nufi dakin da yayi ajiya tun daga kofar da ya tarar a bude yasan akwai damuwa shiga yayi ba kowa leko bayi yayi babu ita da sauri ya fice dakin Mai gadi ya shiga gashi dai yasss Babu kayakinsa inalilahi shikenan asirinsa na gab da tonuwa hannu na rawa ya Rika wata lamba in ka gansu ka kashe shi ka kawo min ita na kashe ta da hannu na you oga sannan aka katse motarsa dake wake ya nufa bayan ya rufe gidan dudduba anguwan Yake Amma shiru Babu labarinsu . Mota baka ce tayi parking a gabansu namiji nee ya fito tuni wani fitsari ya Kama ado mu gudu hajiya ado ko yaji wannan matashin ya kirasa zuciyarsa na rawa yace eh turo ni akayi nazeefa ce ta turo ni Kiran layin yasa ya daga bayan tabbatar da ta turo yayanta yasa ya sauke ajiyar zucii toh hajiya Zaki iya tfy girgiza kanta Zahra tayi tayi weak Haka shima ado kallon matashin yayi yallabai ka taimaka Mana ba iya daga ta ba zanyi shiru suka ji sannan ya ce toh isota yayi sannan ya daga ta cakk kamar babyn roba yasa ta a baya ado na gaba sannan yabawa motar wuta a junction din fita suka kusan buguwa da wata mota masifar Mai mota yafara wa matashin Bai tanka ba yayi reversa ya wuce , Muhammad dake zaga anguwa Kuma ba labari kenan yazo junction din fita anguwa suleja suka hadu da wata mota Cike da masifa ya fara. Mgn Amma ba atanka ba illa reversa da akayi aka wuce da badon tashin hankali da Yake Cike da ya koyawa Wanda ke cikin motar hankali bari kawai shima ya nufi anguwa kalewar Haka ya ringa zaga anguwa har kusan 3 sannan ya nufi gidansa

magajin sarauta 2Where stories live. Discover now