16

70 13 0
                                    

KWANTACCIYA 16

(2nd Edition)
Pharty BB

Zaina buɗe idanuwanta ta jawo wayar da take ringing ta duba screen ɗin ta ga Musa. Ɗauka ta yi, da dishashshiyar muryarta ta ce. "Boyfriend."

"Girlfriend kina ganin wannan hukuncin shine dai-dai." Ya tambayeta ta ɓangaren shi.

Hawayenta da suka gangaro ta share tace. "Boyfriend ban samu wani mafitar ba sai shi, Boyfriend mu gudu, mu gudu a ɗaura mana aure shi ne kawai mafitar mu."

Shuru Musa ya yi don yadda yake son Zaina komai ake ce ya yi zai iya. A hankali ya ce. "Kina ganin hakan shine mai kyau."

"Shi ne Boyfriend." Ta faɗa cikin muryar kuka.
.

..

Har yamma Zaina tana ɗakin a kwance tana bacci bayan gama wayar su da Musa, ta samu baccin da yau kwana uku ya kauracewa idanuwanta ya ɗauketa.

Uku da rabi ta ji bugun ƙofa, ta buɗe idanunta da suka mata nauyi ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin taga matar Yaya Ado ne Surayya da wasu ƴan mata da basu kaita ba su biyu ƴan uwansu.

"Lafiya?" Zaina ta tambaye su tana ƙarewa ƴan matan kallo.

"Mun zo miki kitso da lalle ne." Ɗaya ta faɗi haka.

Zaina ta buga tsaki tana komawa ciki ta ce. "Dalla ku matsa ku bani guri ba za ayi ba."

Ciki Surayya ta shigo ƴan matan suka tsaya a waje, ta zauna kusa da Zaina tace. "Haƙuri za ki yi Zaina ki bari a miki ko don maganar mutane."
"Su yi mana, ni fa sun ishe ni komai abun magana, magana baya ƙare musu." Zaina tace tana fitar da hawaye, haushin kowa take ji a dangin su.

Roƙar duniyar nan Surayya ta yima Zaina akan ta tashi ta ƙi, ƙarshe ma da ta ishe ta miƙe a harzuƙe tace. "Wai ke ana dole ne ki rabu da ni mana, ina ganin girman ki kar kisa na faɗa miki magana."

Shuru Surayya ta yi ta miƙe ta ce. "Allah ba ki hakuri."
Daga haka ta fita tare da ƴan matan Zaina ta bisu da tsaki.

Da suka shiga wajen Inna suka sanar da ita, tace su rabu da ita kawai.

Ƙarfe takwas anyi sallar isha'i Zaina ta miƙe ta fita a ɗakin, ta shiga cikin gidan da yake cike da jama'a, hijabinta taja ta rufe rabin fuskarta don kar a ganta ta wuce ɗaki ta ɗauki abubuwan buƙata ta fito ta wuce bangida, jikinta ta kimtsa ta fito kasancewar ba ta sallah.

Ɗakin Tahiru ta shiga ta ɗauki wayarta ta fito, daga nan ba ta koma cikin gidan ba ta leƙa waje ta ga babu mai zuwa ta sa kai ta fita.

Tafiya kawai take kamar zata ari ƙafa, cikin sauri take yi ko duba bayanta ba ta yi don kar a ganeta, har sai da tasha kwanar da zai kaita layin bayan su kafin taji hankalinta ya kwanta taci gaba da tafiyarta a hankali, ta zaro wayarta ta ƙira Musa.

Bayan Musa ya amsa da da ma zaman jiran ƙiran ta yake, Zaina tace. "Boyfriend na kusa gurin ka zo za ka ganni jikin wani transformer, idan ka iso ka ƙirani."
...

Daga ɓangaren shi ya amsa mata ya kashe wayar, ya fita a ɗakinsa zuwan waje ya shiga motarsa ya kunna da sauri yana barin gidan su bai sanar da kowa ba ga inda zai je ya fita.

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now