15.

261 31 2
                                    

KWANTACCIYA 15
(2nd Edition)
Pharty BB

Bisa rashin ji na da ku ka yi ina rubuta sabon littafina ne GOBE DA NISA. In sha Allah duk weekend za ina yin posting page biyu zuwa uku. Masu son su karanta littafin ku duba account nawa na ArewaBook https://arewabooks.com/u/phartybb
Ko ku min magana ta WhatsApp 07037487278.
...

"Ka turo gidan mu ayi maganar aurenmu." Zaina tace tana mayar da hankalin ta titi.
Da mamaki Musa ya kalla Zaina, kafin ya mayar da hankalinshi kan titi yace. "Are you serious Girlfriend?"
Kai ta ɗaga mishi. Cike da farin ciki yace. "Thank you so much Girlfriend, ashe surprise ɗina za ki yi."
Murmushin ƙarfin hali Zaina ta yi ba tace komai ba. Musa sai zuba mata surutu yake da godiya.
A ƙofar gidan su ya ajiyeta, ba ta ji tsoro ko ɗar cikin ranta ba don wani ya gansu so take ma a ganta da shi a san shi ne take so.
Fitowarta daga motar bayan ta mishi sai anjima ta juya suka yi ido biyu da Hashim da yake zaune cikin motarshi, ya buɗe ƙofar motar kafarshi ɗaya a waje ɗaya a ciki yana kallonta, ranshi a haɗe irin wanda ba ta taɓa gani ba.
Kanta ta ɗauke ta nufi cikin gida, ya fita a motar ya rufe ya bi bayanta.
Bai sameta a tsakar gida ba sai Inna, ya gaisheta ya ce. "Inna ina Zaina."
Inna ta ce. "Yanzu ta shigo tana falo."
Cikin falon ya shiga, ta ajiye jakarta kenan a ɗaki ta fito ta ganshi ya shigo, cikin sauri tana shirin komawa ya cafkota, ta fara mutsu-mutsu za ta kwace jikinta ya riƙeta sosai ya zaunarta saman kujera ya hanata wucewa.
Kanta ƙasa ta kasa kallon cikin idonshi, duk da yanda take jin idanuwansa ke yawo a jikinta.
"Zaina!" Ya ƙirata da sunan da ta jima ba ta jishi a bakinsa ba.
Da ƙyar ta iya buɗe baki ta amsa ta ce. "Na'am."
Yana ci gaba da kallonta ya ce mata. "Shi ne wanda ki ke son?"
Kai ta ɗaga mishi alamar eh, wanda ya ƙara sosa ranshi ya yi murmushin taƙaici yace. "To ni kuma fa?"
Sai lokacin ta ɗago idanuwanta ta kalle shi, idonsa cikin nata tar ta yi ƙasa da kanta murya ƙasa-ƙasa tace. "Kai yayana ne ai."
"Don ina yayanki sai aka ce miki bana sonki? Ko ba sonki nake ba." Ya faɗa mata. Shuru tayi tana wasa da yatsunta, ya ci gaba da cewa.
"Ni ma ai ina sonki, kuma aurenki zan yi, ke ma kin sani furtawa ne kawai ban yi ba."
"To ai kai son yaya da ƙanwa ne." Ta ce tana ɓata murya kamar ta mishi kuka.
Ya ce mata. "Waya faɗa miki? Ke ki ka kallon haka amma ni son aure nake miki."
Kallon shi tayi da sauri, ya ɗaga mata gira ta mayar kanta ƙasa da sauri ta kasa cewa komai, hakan yasa ya ci gaba da cewa. "Da sonki na taso cikin zuciyata wanda nake ganin son yaya da ƙanwa ne tsakanin mu, ban san haka ba sai da naga zanyi nesa da ke na ji bana son hakan, sai kuma lokacin da kika ƙirani cewa za ki fara fita makaranta a nan na ji wani mugun kishin ki da ban taɓa tsammani ba, idan za ki tuna na taɓa ce miki ki riƙe godiyar ki zan nema abu a wajenki idan na dawo? To soyayyarki zan nema idan har kin amince na samu iyaye da maganar aurenmu, sai aka samu akasin haka na samu ƙiran Baba Lamiɗo shekaran jiya."
Shuru yayi bayan ya gama faɗar haka, falon ya ɗauki shuru na tsawon mintuna kafin yace. "To yanzu ya za'a yi Zayn? Ni ina sonki ke kina son wani."
Zaina ɓata rai ta yi don ita fa ba ta son wannan son da yake ƙira tsakanin su, har abada kallon yaya take mishi. Haka yasa ya ce.
"Ni ma ban sani ba, ka samu su Baba Fatime da maganar a raba kawai tun da bana so."
Kalmar bana so shi yafi ƙona ranshi, yarinyar da ya taso da sonta cikin ranshi da jinin jikinshi, rabuwa da ita abu ne mai wahala a tare da shi don ita ce rayuwarshi.
Miƙewa tsaye yayi ya ce. "Zamu samu mafita, amma ki sani Hashim ba zai taɓa fasa auren Zaina ba sai idan har ƙaddarar Allah ta hana."
Kallonshi tayi da sauri ya juya ya fita, ta fashe da kuka tana cewa. "Wallahi ba zan aure ka ba akan me, tun yaushe aka daina auren dole."
Kuka tayi tai da maganganun da ita kanta bata san su ba zuciyarta tana zafi, zuciyarta tana son yayantan amma haushinsa yafi rinjaye da ya ƙi barinta ta auri wanda take so.
Tunawa da ta yi ta sanar da Musa ya turo iyayen shi ta ji hankalinta ya kwanta, ko ba komai idan suka zo ba zasu hanata aurenshi ba.
...
Bangaren Musa yana komawa gida ya sanar da Momy, tayi farin ciki sosai ta ce ya samu ƴan uwan mahaifinshi suyi magana ya ce to ya wuce ɗakinshi.
Bayan sallar magriba da yayi a masallaci ya wuce gidan yayan babansa ya sanar mishi. Yayi murna sosai, ya ce in sha Allah nan da kwana biyu zai sanar da ƴan uwa sai a haɗu a je.
Godiya ya mishi kafin ya miƙe ya mishi sallama ya tafi.
...
Da safe Zaina ta tashi da ciwon kai don kukan da ta kwana tana yi. Shirin makaranta tayi ta fito tsakar gidan za ta wuce Inna tace mata. "Abincin ki."
"Na ƙoshi." Ta ce tana shirin fita Baba ya dakatar da ita. "Dawo maza ki ci ko ki fasa zuwa makarantar."
Sum ta dawo ta ɗauki plate ta zuba jellof ɗin macaroni ne, ta saka fork ta koma bakin baranda ta zauna ta fara ci.
Tana cikin ci taji sallamar Hashim, ko kallon inda yake ba ta yi ba ta ci gaba da cin abincin ta.
Hashim bayan ya gaishe da Baba da Inna ya ƙarasa wajen Zaina ya zauna kusa da ita, har lokacin bata ɗago ta kalle shi ba, ya yi murmushi ya saka hannu ya ɗauke fork ɗinta ya debi abincin ya kai bakinsa.
Tashi ta fara ƙoƙarin yi, ya saka hannuwansa ya danne hannunta ya ce. "Zauna ki ci abincin ki."
Komawa ta yi ta zauna tana ƙwace hannunta ta haɗa rai, ya miƙa mata fork ɗin ta karɓa ta fara ci.
Idanu kawai ya zubawa ƙaramin bakinta yadda take tauna abincin a hankali ya ji ya burge shi.
Haka ya sakata gaba ta ci abincin kaɗan tace ta ƙoshi ta miƙe, ta kai Plate ɗin bakin murhu ta yima Inna da Baba sai anjima ta fita.
Shima Hashim tashi yayi ya musu sallama ya bi bayanta. Ganin ta yi nisa motar shi ya shiga ya bi bayanta ya danna mata hon, tana juyawa ya mata alamar ta zo ya kaita, ta ƙi ta ɗauke kanta.
Fitowa yayi ya isa wajenta ya fizgo hannunta ya sakata motar, kafin ya zagaya ya shiga ya ja motar.
Tafe suke babu wanda ya yima wani magana, har cikin makarantar ya ajiyeta bakin department ɗinsu ta sauƙa ba ta tsaya mishi godiya ba.
Girgiza kai yayi yana cewa .'lallai akwai aiki a gabanshi.'
Ƙin tafiya yayi ya gyara kujeran motar ya kwanta don jiranta.
Kusan awa ɗaya da rabi mota ta yi parking kusa da nashi, ya buɗe idanuwansa jin dirin mota ya kalla mai shi lokacin da yake fitowa, matashin saurayi ne da in har zai fishi bai fi shekara biyu ba.
Saman boat ɗin motarshi ya hau ya zauna, ya ciro wayarshi yayi ƙira kafin ya kashe ya maida aljihunsa ya sauƙa.
Fitowar Zaina ya hango ta nufo wajen su, hakan yasa ya gyara kujeran motarshi ya kunna motar, ya ga ta nufi gurin saurayin da murmushi ɗauke saman fuskarta shi ma murmushin ne a fuskarshi suna magana da ba ji yake ba.
Zaina tana kallon motar Hashim ta nuna tamkar ba ta ganshi ba ta wuce wajen Musa, bayan sun gaisa ta shiga motarshi shi ma ya zagaya ya shiga suna barin harabar makarantar.
Idan ran Hashim yayi dubu ya ɓaci, wani mugun kishin Zaina ya kama shi, da har tana nuna son wani sama da shi. Shine fa Ya Hash ɗinta da take so sama da kowa cikin yayunta.
Motarshi ya ja ya bar cikin makarantar yana bin bayansu, lokacin da ya isa ya samu ta sauƙa sunyi sallama Musa yana barin gurin.
Bai iya bin bayan Zaina ba, bayan ya parker motarshi ya shige gidansu. Har dare bai shiga ba wanda hakan ya yi ma Zaina daɗi.
...
Washegari lahadi Zaina ba ta da lecture tana gida, wankin kayanta tayi, tare da aikace-aikacen gida ta ɗaura abincin, bayan ta gama ta yi wanka wajen ƙarfe uku tana hutawa ta ji sallamar Baba.
Amsawa tayi da mamakin me ya dawo da shi yanzu, ta fito waje yana bakin bishiyar  su zaune saman kujeran roba fari, ta ƙarasa wajensa ta zauna a ƙasa ta ce. "Baba kana buƙatar wani abu."
Kai ya girgiza mata yana binta da kallon da ta ji ƴaƴan cikinta sun motsa. Inna ta shigo gidan tare da Ado da Tahiru, Hashim yana bin bayansu. Ganin su tare dukka sai taji tsoro ya kamata.
"Zaina!" Ta ji Baba ya ƙirata da ɓacin rai, ta amsa kanta ƙasa zuciyarta tana bugawa.
Cikin ɓacin rai ya ci gaba da cewa. "Kwantacciya ke kika fara karya mana dokan fara karatun ƴa mace cikin ahlinmu, wanda mun ɗauki shekaru sama da ɗari muna bi. Shin ke ba kya jin magana ne tamkar ƴan uwanki ko don kin zama KWANTACCIYA tsawon shekaru uku kin fito duniya za ki zo mana da banbance-banbance  ra'ayi? To ba zai yiwu ba, aurenki da ɗan uwanki Hashim tamkar anyi."
Zaina ba ta san lokacin da ta ɗago kanta ba a tsorace ta ce. "Kar ku min haka Baba, tsawon shekaru an daina auren dole? Shin bakwa tsoron haƙƙin Musa ya kama ni?"
"Ahlul Khitab ɗin?" Baba ya faɗa a tsawa ce.
"Baba ya Musulunta fa..." Shi ne furucin da Zaina ta faɗa da ba ta ƙarasa ba taji sauƙar mari ta riƙe kumatunta, ta kalla Ado da ya watsa mata mari rai haɗe.
Baba ya ci gaba da cewa. "Har ke zamu yi magana da yayuna da mahaifiyata ki ƙi bi, ki saka wancan yaron ya turo iyayenshi. Zaina yaushe ki ka zama haka ko don kinga an bar ki kina yin abin da kike so shine kike mana haka."
Girgiza kai tayi hawaye na bin fuskarta ta kasa magana.
Ya buga tsaki ya ce. "To ki sani ke kika fara karatun boko, ba kuma za ki fara auren bare ba, duk maganganun da ake a cikin dangi akan ki ina ji kawai kawar da kai nake na toshe kunnuwana, don haka ba zan ƙara jawo wa kaina wani maganar ba, an saka ranar aurenki da ɗan uwanki wata biyu mai zuwa amma abin da kika aikata yasa sun janye sun mayar da sati biyu."
Daga haka Baba ya tashi ya fita, Zaina ta rushe da kuka ta lallaɓa wajen Inna tace. "Don Allah Inna ki musu magana su janye bana son auren nan, wallahi idan ba ku aura min Musa ba mutuwa zanyi."
Tsaki Inna taja tana barin gurin bayan tace.."To ki mutu mana Zaina, idan aka kai ki gidan Hashim ki ɗauki wuka ki kashe kanki."
Wani kukan ta sake kamar mahaukaciya a gurin, kowa ya bar mata gurin banda Hashim da yake jin kukanta har cikin ranshi.
Taku ɗaya ya yi zai ƙarasa wajenta ta miƙe a fusace tace. "Kar ka yarda ka ƙaraso wajena."
Dakatawa yayi ya bita da kallo har ta shige ɗaki, ya jima tsaye wajen kafin ya juya fita a gidan.
Can cikin ɗaki ta shiga ta faɗa saman gado ta dinga rusar kuka kamar zata mutu, har taji kanta ya fara ciwo. Kafin wani lokaci zazzaɓi ne ya rufeta mai zafi harda rufuwarta, sannan lokacin ruwan hawaye bai daina zuba a idonta ba.
Magriba Inna ta ga ba ta fito ba, ya sakata leƙawa ta hangota kwance ta duƙunƙune guri ɗaya, ta ƙarasa wajenta. Abin ƴa da uwa sai taji tausayinta ya kamata, ta taɓa jikinta ta ji da zafi ta tashi ta fita.
Tahiru ta sanarwa ya ce bari ya faɗawa Hashim su kaita pharmacy, tace to ta koma ɗakin ta ɗago Zaina zaune, ta buɗe idanunta da sun sauya kala suka fito waje.
Fitowar su kenan Tahiru da Hashim suka shigo gidan suka ƙarasa wajenta, Hashim ya riƙeta tana son ƙwacewa ya hanata suka fita tare da Tahiru. Bayan motarshi ya kwantarta ya zaga ya shiga shi ma, ya kunna motar suna barin gurin.
A bakin Pharmacy ya faka motarshi suka fito ya buɗe inda Zaina take kwance ya fito da ita.
Yana riƙe da ita suka shiga ciki, ya zaunarta ya zauna gefenta yana jera mata sannu.
Magunguna aka rubuta mata da allura da za'a mata bayan an tabbatar da zazzaɓi ne kawai yake damunta. Hashim ya ce a mata alluran maganin sai sun je gida.
Alluran aka haɗa aka nufo wajenta don yi mata. Zaina ta kalla Hashim murya ƙasa-ƙasa tace. "Kasan dai Ya Hash bana son allura."
"To ai ba ki da lafiya ne, ki tsaya a miki kawai guda ɗaya ne." Ya ce cikin lallashi.
Ƙin tsayawa ta yi, ta tashi jiri ya ɗauketa ya riƙota suka zauna ya riƙeta jikinshi ya gyara mata zama, ya ɗaga hijab ɗinta tare da sauƙe skirt nata ƙasa ya runtse idanuwansa, haka aka soka mata alluran da ya sakata riƙoshi da ƙarfi ta runtse idanunta.
"An gama alluran matsorata." Mai Pharmacy ya faɗa yana musu dariya ganin yadda suka riƙe junan su.
Ido Hashim ya buɗe yaga har an gama, ya sauƙe mata hijab ɗinta jin haka ya saka Zaina zare jikinta a nashi.
"Amma waɗannan sabin aure ne?" Mai Pharmacy ya tambayi Tahiru.
Murmushi yayi yace. "An kusa dai auren su cousin ne."
Hashim ya miƙe tare da taimakawa Zaina ta miƙe, bayan ya biya shi suka fita.
A hanya Hashim ya sayawa Zaina abinci, kafin su ƙarasa gida har ta fara jin dama dama. Suna isa ta fita ta wuce ciki ko ta kan abin da ya saya mata ba ta bi ba.
Shi ya ɗauka ya shiga da shi ciki, ya ba Tahiru ya ba ta kafin ya musu sai da safe ya fita.
Zaina tana shiga ɗaki ta laliɓo wayarta dake cikin jakarta, ta duba ta ga ƙiran Musa sama da goma banda saƙonnin. Ƙiran shi tayi cikin sauri.
Musa ya ɗauka dama zaman jiran ƙiranta yake tun da iyayensa suka dawo masa da labarin cewa an bada auren Zaina ga ɗan uwanta, har an yanke ranar biki, hankalin shi ya tashi duk da ya tuna kalamanta cewa dangin su ba'a auren bare amma ya tabbatar Zaina tana sonshi ba zata amince da zaɓin su ba.
Bayan ya ɗauka Zaina tace. "Boyfriend."
"Girlfriend." Ya amsa yana sauƙe ajiyar zuciya bayan jin muryarta.
Kuka Zaina ta saka tana cewa. "Wallahi Boyfriend bana sonshi dole aka min, kasan dai kai nake so kuma zan bi duk ta yadda zanyi inga an fasa auren nan."
"Girlfriend ina sonki sosai, idan na rasaki rayuwata za ta tangarɗa ke ce cikon rayuwata." Ya ce mata a hankali cikin tausayin kan su.
"Na sani Boyfriend." Zaina tace tana sakin wani kukan.
Wayar da suka gabatar tsakaninsu duk bayyanawa juna irin son da sukewa juna suka yi, inda Zaina tace ya bata nan da kwana biyu idan har ba'a fasa auren ba za ta nema musu wani hanyar kafin suka kashe wayar.
...
Washegari ranar Litinin Zaina ta shirya za ta wuce makarantar Inna ta dubeta. "Kina tsammanin ina za ki je."
Zaina ta ce. "Makaranta mana Inna."
Inna ta harareta ta ce. "Ai karatu ya ƙare, wato kin mayar da mu marasa hankali ki je ku haɗu da shi yaci gaba da hure miki kunne ko, to a gidan nan karatunki ya ƙare, in anyi auren idan Hashim ɗin ya yarda sai ki ci gaba da zuwa. Ki koma ciki dalla."
"Inna ni ba da shi zan haɗu ba karatu zai kai ni." Zaina tace alamar roƙo.
A tsawa ce Inna ta ce. "Rufe min baki ki wuce ɗaki."
Shigewa ɗaki Zaina ta yi cikin fushi an hanata zuwa karatun da take mutuƙar so, tasan dai in har shi Hashim ɗin ya ji zai barta taje don shi ma yana so.
...
Wasa wasa cikin satin Zaina ba ta fita ko ƙofa Inna ta hanata, ta yi roƙon ta yi har ta gaji, ta yi kukan ta yi har ta gaji. Wayarta kullum yana maƙale da ita suna waya da Musa tana ƙara jaddada mishi cewa tana sonshi ya bata lokaci.
Hashim kam Kaduna ya wuce wajen aikinsa, don neman hutu ya dawo a shiga hidimar biki.
Satin shi ɗaya da kwana uku, ranar Alhamis ya dawo da gobe Jumma'ah asabar ɗaurin auren su.
Tunda Zaina ta tabbatar yau Alhamis, gobe juma'a jibi asabar ɗaurin aure hankalinta ya tashi sosai kuka take ba ji ba gani, ta kasa nutsar da hankalinta duk ta fita hayyacinta. Ɗakin Tahiru ta shiga ta kulle kanta ta ci gaba da kukanta wunin ranar.
Mama Hadizatu tun da ta ji ita ma ta yi faɗan ta yi bala'i duk a banza, ta saka Hashim a gaba akan yaje ya samu iyaye yace ya fasa auren, amma ya ba ta haƙuri ya ce bai zai iya ƙin bin umarnin su ba, don dole ta bari ayi auren da ta ɗauki alƙawarin Zaina ba za ta taɓa jin daɗin shi ba.
Gidan su Zaina duk ya cika da ƴan uwa ana ta hada hadar ɗaurin aure.
...
Zaina kumburarrun idanunta ta buɗe bayan tunowa da rayuwar su, ta jawo wayarta ta tura Musa saƙon da yake cike da hukuncin da ta yanke, wanda take ganin shi ne mafitar su da shi da ita.
...

Ga Hashim ga Musa.

Ko wa Zaina zata zaɓa 🤔
Musa da take mutuƙar so iyayenta basa son shi.
Ko Hashim da yake sonta mahaifiyar shi ba ta son Zaina.

#phartybb

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now