13.

140 31 6
                                    

KWANTACCIYA (2nd Edition):: https://arewabooks.com/book?id=627cdadb445c25b2bb950eff

KWANTACCIYA 13
(2nd Edition)
Pharty BB

Cikin sati ɗaya tsakanin Musa da Zaina wata soyayyace ta shiga tsakani su da basa wuni basu ga juna ba, ko jin muryar juna.
Kullum yamma shi yake maidata gida, a bakin titi yake ajiyeta duk da yana son ƴan gida su san da zamanshi, tace masa za ta sanar da shi in lokacin yayi don ba ta san ta ina za ta fara sanar dasu cewa ta samu wanda za ta aura ba.
Zasu karɓe shi? Zasu bata zaɓin ta? Ko shin za su bi ra'ayinta?
Ire iren waɗannan tambayoyin da take yi ma kanta su suke sakata damuwa, amma ta kudurta a ranta duk lokacin da suka mata maganar aure tsayawa za ta yi sai inda ƙarfinta ya ƙare ta auri wanda take so.
...
Sati biyu da faruwar haka wataranar alhamis Zaina ta fito a test misalin 2 za ta tafi gida don bata da lecture da yamma.
Kamar kullum Musa ne yazo ɗaukarta don tana fitowa ta ƙirashi ta sanar da shi, abinda yake yi ya bari ya zo ɗaukarta.
Tafe suke suna hiran saurayi da budurwa, ta ga ya canza hanya ta dubeshi tace. "Boyfriend ina za muje."
"Sai dake zanyi."Yace yana murmushi.
Ita ma murmushin tayi kafin ta haɗa rai tace. "Maganar gaskiya ina za ka kai ni."
"Maganar gaskiya sai dake zanyi."
Ganin ya maida abin wasa ya sa Zaina yin shuru ta zuba idanu tana bin cikin unguwar da suka shiga da kallo, manyan gidajene masu kyau.
Bakin wani gida yayi parking tare da danna horn aka wangale get ɗin gidan ya shiga yayi parking harabar gidan, ya kashe motar yana fita yace. "Fito muje ki gaishe da Momy."
Idanuwanta ta zaro tana kallonshi ya ɗaga mata kai. "Ba kullum nace zan kawo ki kina ƙi ba."
"Amma baka kyauta min ba." Zaina tace kamar za tayi kuka tana fitowa, yayi gaba yana murmushi, tabi bayanshi a nutse tare da kimtsa jikinta da tafiyarta.
A kofar falon suka yi sallama, ya shiga kafin ita ma tayi tana shiga cikin kunya, ba kowa falon sai Esther da Jawad da shi kaɗai ne ya amsa ya taho gurin Zaina yace. "Girlfriend."
Kunya ne ya kama Zaina, ya riƙo hannuwanta ya jata saman kujera ta zauna, yayi ciki da gudu yana kwalawa Momy ƙira ga Girlfriend tazo.
Ganin Jawad ya tafi ƙiran Momy yasa Musa zama d'ayan kujera.
"Ina wuni." Zaina ta faɗawa Esther, ta ɗago idanuwanta ta dubeta ta amsa da lafiya.
Tare Momy da Jawad suka shigo falon, ya sake hannuwanta ya zauna kusa da Zaina yace. "Momy ga Girlfriend kin ganta kyakkyawa."
"Ina wuni Momy." Zaina tace cike da kunya bayan ta sauƙa ƙasa ta zauna.
"Lafiya lau ya mutanen gidan su Mama da Baba." Momy ta tambayeta.
"Duk lafiyarsu ƙalau." Zaina ta amsa kunyar matar ya kamata.
Gaisuwa suka yi cikin mutumci duk Zaina ta kasa sakewa, kusan mintunan su talatin mai aikinsu matashiyar budurwa ta kawo mata ruwa da abin sha, kasa taɓa komai Zaina tayi ganin haka ya saka Momy tashi ta bar musu falon.
"Mu tafi." Zaina ta faɗawa Musa ƙasa ƙasa-ƙasa, ya tashi ya buɗe bottle na ruwa ya tsiyaya a cup ya miƙa mata yana zama gefenta. "Sai kinsha ruwan gidanmu, haka za ki zo ba ki sha komai ba."
Girgiza kai tayi tace. "Na ƙoshi."
"To ko za ki wuni a nan yau." Yace yana gyara zamansa, ganin haka ya sakata karɓa tasha rabi ta ajiye sauran tana miƙewa, shi ma ya miƙe ya wuce ciki mintuna uku ya fito tare da Momy.
Fita suka yi har harabar gidan, ya shiga ya kunne motar Zaina ta shiga Momy ta ajiye mata ƙaramin kwali saman cinyarta tace. "Mun gode sosai ƴata ki gaishe da mutanen gida."
A kunyace Zaina ta ce. "Za su ji, Nagode."
Daga haka Momy ta matsa Musa ya ja motar suna barin harabar gidan.
"Zan rama." Zaina tace bayan sun hau kan titi. Ya juya ya kalleta ta ɗauke kanta yayi murmushi yace. "Da kin burge ni na matsu iyaye su shiga maganarmu."
Shuru ta mishi ta ƙi mishi magana, yaci gaba da tuƙin shi yana murmushi lokaci zuwa lokaci yana kallon Zaina da ta haɗa rai.
Maimakon ta ga ya sauƙeta in da ya saba ta ga ya nufi cikin unguwar su da ita, hakan ya haddasa mata bugun zuciya ta kasa mishi magana.
Har kofar gidansu yayi parking ya dubeta. "Zamu shiga in gaishe da Mama."
"Ka rufamin asiri ba yanzu ba." Zaina tace tana waro ido.
"Sai yaushe?" Ya faɗa yana kallon cikin idanuwanta.
"In lokacin yayi zan sanar da kai." Ta ce ta ɗauke idanuwanta.
Shuru yayi kullum maganarta ɗaya kenan, lock ya cire mata ta fita suka yi ido biyu da Ado da yayi parking ɗin motarshi, ya nufo wajen mai motar da yake neman ƙarin bayani akanshi ganin sabuwar mota kofar gidansu ya sauƙe Zaina.
Zaina tana ganin ya nufo gurin ta kwasa da gudu tayi cikin gida, ya ƙarasa wajen motar Musa yana shirin barin gurin ya ƙwanƙwasa gilashin motar, ya dakata ya buɗe tare da fitowa ya miƙa masa hannu don musbaha.
Hannu Ado ma ya miƙa masa suka yi musabaha ya ƙara da cewa. "Waye kai?"
A kunyace Musa ya sanar da shi alaƙarshi da Zaina. Ado ya jinjina kai yace. "Amma Zaina ba ta sanar da kai komai game da ahlinmu ba ko?"
"Ta sanar dani komai." Ya faɗa kai tsaye.
"Kasan komai." Ado ya maimaita.
Kai Musa ya ɗaga mishi. Ado murmushin taƙaici yayi ya wuce ciki ya bar Musa tsaye yana mamakin ko me yasa suke haka?.
Ba shi da mai ba shi amsa ya sa shi komawa motarshi yana barin gurin.
...
Zaina tana tsaye Inna na tambayarta lafiya ta shigo mata gida a guje ta ga shigowar Ado, da sauri ta shiga ɗaki zuciyarta na bugawa tasan shikenan yau kam abinda take ɓoyewa zai tonu.
Ganin shuru yasa ta ajiye jakarta tare da saka kwalin da Momy ta ba ta a jaka, ta cire hijabinta tana linkewa Inna ta shigo ɗakin da ya saka cikin Zaina murdawa, ta kalla Inna da ta tsaya a kanta fuskarta haɗe.
Idanuwanta ta sauƙe ƙasa zuciyarta tana bugawa, taji Inna ta watsa mata tambaya. "Waya sauƙe ki a mota?"
Shuru tayi ta kasa ba ta amsa, ya saka Inna buga mata tsawa tace. "Ba dake nake magana ba, waya sauƙe ki a mota?"
"Ɗan ajinmu ne." Zaina tace cikin rawar murya.
"Ɗan ajinku shi ne zai kawoki har kofar gida, ki sanar da ni gaskiya ko in ɓata miki rai." Inna ta ce cikin ɓacin rai.
Shurun da Zaina tayi shi ya saka Inna yarda da abin da take zargi, da mugun mamaki tace. "Saurayinki ne?"
Kai Zaina ta ɗaga, ba ta gama tantancewa ba Inna ta kwasheta da mari tace. "Ba ki isa ba, ba ki isa ki jawo min abin magana ba cikin dangi banda wanda ake min kullum, ke ko kunya bakya ji Zaina, kar ki manta ke ce mace ta farko da ta fara karya dokar fara karatun ƴa mace cikin dangi kuma tun bayanki ba wanda ya saka ƴarsa, yanzu kuma ki zo min da maganar wani namiji, to wallahi ba ki isa ba kinji na faɗa miki."
Kuka Zaina take kamar ranta zai fita, tana sauraron maganganun Inna har ta gama da kyar tace. "Inna don Allah kar ki rabani da shi, ina sonshi."
Inna ta tareta ta ce. "Rufe min baki bari shi babankin ya dawo idan shi ya zuba miki ido sai kin ƙare boko to Baba Fatime zan haɗa ki da ita ta cire miki mijin aure cikin ƴan uwanki."
Jin kalaman Inna ya saka Zaina ƙara rushewa da kuka tace. "Wallahi Inna bana son kowa kuma ba zan auri kowa ba sai shi, wannan wani irin abu ne an fa daina auren dole."
Wani marin Inna ta kai mata tana cewa. "Dalla rufemin baki ko in mugun ɓata miki rai sai dai ki mutu."
Daga haka Inna ta fita cikin jin haushinta jin tana neman jawo musu wani abin magana.
Kuka Zaina tayi sosai har kanta ya fara ciwo, kafin ta jawo wayarta ta ƙira Hashim tasan shi kaɗai ne zai iya magana Inna ta fasa haɗata da Baba Fatime.
Ringing ɗaya ya ɗauka duk da yana aiki amma ya ragu, ta ɓangaren shi yace. "Hello My Zayn."
Kuka ta fashe dashi tace. "Ya Hash."
Rikicewa yayi mata jin kukanta, cikin lallashi yace. "Me ya faru My? Waya taɓa min ke? Ki bar kukan nan kin san yana ɓata min rai."
Kukan ta tsagaita ta ce. "Ni dai ka ƙira Inna ka ba ta hakuri."
"Kinyi laifi kenan." Ya tambayeta cikin kwantar da murya.
Hawayenta ta share wani na zuba tace. "Ni dai kawai ka ƙirata ka bata hakuri."
"To na ji share hawayenki, kin san bana son zubarsu tsada ne da su." Ya ce yana sake kwantar da murya cikin zolaya.
"Na share." Tace tana gogewa kamar yana ganinta.
Murmushi ya yi da ta ji sautin shi ya ce. "To yi mini dariya na ji."
"Ni dai ka bari ba yanzu ba." Tace tana turo baki.
Haka yayi ta lallashinta har ya sakata yin murmushi, sannan ya rabu da ita yana mamakinta ita da laifi ita da kuka, duk da ba ta sanar dashi ba yasan itace da laifi.
Kwanciya Zaina tayi ko ta kan abinci ba tabi ba, a haka bacci ya ɗauketa a gurin. Inna ta shigo ta ganta ta ɗauke kanta don haushinta take ji.
Har bayan la'asar kafin Zaina ta farka ta fita ta ɗaura alwala ta koma ɗaki ta yi azahar da la'asar, ta fito don neman abinci ta samu babu, ta isa wajen Inna dake bakin bishiya tace. "Inna abinci na?"
"Na ba almajirai." Tace taci gaba da aikinta.
Zaina ta zauna idonta na cika da hawaye, me laifin abin da ta aikata da za'a mata horon hanata abinci.
Ganin zaman ba zai mata ba ya sakata tashi ta haɗa wuta Inna tana kallonta.
Abincin dare ta hau dafawa har karfe biyar kafin ta haɗa tuwo da miya, ta gama ta zuba nata a tray ta ɗauka ta koma saman baranda.
Haka ta gama cin abincinta da taci sosai, ta tashi ta ɗauke tray ta kai bakin murhu ta wanke hannunta ta ɗaura alwala ta shige ɗaki sallar magriba. Bayan tayi ta jawo wayarta ta tarar missed call ɗin Musa ta ƙirashi.
"Girlfriend ina kika shiga ne." Ya faɗa bayan ya ɗauka.
A sanyaye ta ce."Ina aiki ne Boyfriend."
A hankali ya ce. "Girlfriend Momy ta yaba da hankalin ki sosai har tana tambayana yaushe za'a so min tambaya, a bani izinin zuwa hira wajenki."
Abin da ya wuce ne ya dawo mata, hawaye ya taru a idonta tace.
"In sha Allah zuwa nan da ƙanƙanin lokaci ka taya mu da addu'a Boyfriend."
Jikin shine ya ji yayi sanyi jin muryarta ya karaya, ya ce. "Da izinin Allah Girlfriend, an miki wani abun ne a gida."
Girgiza kai tayi tace. "A'a kawai kaina ne yake ciwo."
"Sorry kisha magani ki kwanta kinji Allah kawo sauki." Ya ce cike da damuwa.
"Ameen. Ta ce ta kashe wayarta ta gwada ƙiran layin Hashim, yana ta ringing bai ɗauka ba haka ta hakura da ma ta ƙira taji ko ya ƙira Inna ce.
Ganin har dare Baba bai aika ƙiranta ba taji daɗi a ranta, tana godewa Hashim tasan sun gama magana da Inna ta hakura.
Da safe sai sha ɗaya ta wuce makaranta, da ta gaishe Inna ta amsa da lafiya kawai har Baba ba wanda ya nuna mata komai bayan tai karin kumullo ta wuce.
Sai karfe huɗu ta dawo Musa ne ya kawota kamar jiya har kofar gidan su kusa da sabuwar motar da ta gani yana kyalli, yayi parking ta sauƙa don ba ta ga abin da ya rage kuma ba, gwara kowa ya sani a barta ta auri wanda take so.
Da ya sauƙeta ta wuce ciki ya ja motarshi yana barin gurin. Da sallama ta shiga cikin gidan, ba kowa a filin, nan ta ga sabon takalmi kofar falonsu. A hankali ta nufi nan ta saka kanta ciki tana sake yin wani sallamar da ya tsaya a makogoronta dan ido biyu da suka yi da Hashim, wanda ya ƙara cika ya zama cikakken saurayi mai ji da kwalisa ga wani saje da ya ajiye, ya ƙara haske da kibar da bai masa muni ba sai ma kyau da ya ƙara mishi.
Shi ma ya bita da wani kallo da shi kaɗai yasan ma'anarahi, ganin Zayn nashi ta canza ta sake girma da cika a ɗan watannin da ya barta.

To fa ga Hashim ya dawo🤔

Keep liking and commenting ❤️
Pharty BB

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now