2.

288 28 0
                                    

KWANTACCIYA 2
(2nd Edition)
Pharty BB

Baba ya kalli Innah ya ga tana murmushi tana kallon Hashim, ya mayar da kallonsa kan Hashim da ya ƙurawa jaririyar ido sannan ya ce."Na ba ka ita duniya da lahira."
"Nagode Baba." Hashim ya ce yana ci gaba da kallonta.
Ganin mata sun fara dawowa ya saka Baba karɓan jaririyar, ya mata huɗuba da addu'o'i sosai ya miƙawa Innah yana cewa.
"Allah ya raya Zaina, zamu koma sai zuwa safe, na ga mata sun fara dawowa."
"Ameen." Innah tace ta karɓi jaririyar, yaja hannun Hashim suka fita.
Ido Innah ta zubawa kyakkyawar ƴartan tana kallo, tsawon shekara uku ta ɗauka cikin cikinta. Tun da ta samu cikinta da yayi wata takwas ta fara shirye-shiryen haihuwarta, wanda har ya zo ya shiga wata goma sha biyu ba haihuwa ba labari, abin yayi mutukar girgiza su dukkan ahlin da suma jiran haihuwar ta suke suka ji shiru.
Babu inda basu shiga da Baba ba dan neman magani. Tun abin na damunta har tazo ta hakura, haka cikin ya shiga wata na ashirin ya zamto ya ƙi gaba ya ƙi baya ya daina motsi.
Tsawon shekara uku ta ɗauka ɗauke da cikin, wata rana ta je ganin likita bayan ya dubata yace.
"Mama wannan abun naki bana asibiti bane ku koma na sunnah, in sha Allah ana samun magani."
Da wannan abin da likitan ya faɗa mata ta faɗa Baba, wanda shi ma ya yi na'am da hakan ya samu mahaifiyarsa da maganar.
Taro aka yi tsakanin manya mazan ƴan uwansa, ɗaya daga cikinsu da ya zama Malami ya samu abokinsa da har aljanu yake cirewa suka same shi da maganar.
Addu'o'i ya bata tana yi tana shafawa ta shafa cikinta, cikin ikon Allah abin cikin ya fara motsi.
Duk sati take zuwa gurin shi karɓar addu'a har tayi wata biyu, ranar ƙarshe yace mata. "In sha Allah za ki haifi abin cikin ki, an kwantar miki da shi ne amma duk wanda yayi hakan shi da Allah, ana hakan ne ta hanyar surkulle ko asiri, ba zance komai ba tunda yanzu allahamdulillahi mun samu waraka daga ayoyin Allah da addu'o'i."
Kowa da ya ji maganganunsa ya girgiza, inda daga ranar suka laƙawa abin cikinta suna KWANTACCE da yau Allah ya kawota duniya.
Hayaniyar dawowar mutane ya saka Inna tashi ta shiga ɗaki, ta kwantarta ta zauna gefenta. Adda Aminatu ta shigo tare da mata suna mata barka.
Haka daren duk yawanci an shigo in ka cire mutum biyu Mama Hadizatu da Adda Adama da tun da Mama Hadizatu ta ji labarin haihuwar ta zari mayafinta sai gidan Adda Adama.
Kujerar tsugunno taja ta zauna bakin murhun da Adda Adama take zaune ta rafka tagumi.
Sai da Adda Adama ta gama kwashe tuwonta ta juya ta kalli Mama Hadizatu tace. "Ya aka yi mutumiyar?"
"Ba ki da labari? Ba ki da labarin Hamsatu ta haihu ta haifi abin da naƙi jinin gani." Ta faɗa da jimami da ɓacin rai.
Hannunta ta ɗaura a kai ta riƙe tace.
"Kar kice min mace ta haifa ni Adama, kin banu Hadizatu abin da ake gudu ya faru."
Kwafa Mama ta yi ta ce."Na rasa ya zan yi Adama, yanzu ma haka yana bibiyarta ina ga an haifi mace kin san ba abin da zai hana su Yaya Lamido haɗa su."
"Ni na rasa ma me zance miki." Adda Adama tace tana tagumin ita ma.
Shuru ne ya shuɗe tsakanin su kafin Adda Adam tace.
"Mu koma gurin mutumin kawai ya shiga tsakanin ɗanki da matar nan."
"Sau nawa? Na nawa kuma sanin kanki ne munyi munyi hakan ya ƙi aiki, kawai dai da karfi da yaji zan rabasu ko in turashi makarantar kwana na maza."
Girgiza kai Adda Adama tayi tace.
"Kin san dai su Yaya Lamido ba zasu amince ba kamar yadda ki ka faɗa, kawai ki rabasu da karfi da yaji."
"Hakan za ayi kawai." Mama Hadizatu tace tana miƙewa tsaye tace. "Bari in tafi gida dare ya fara shiga."
Rakiya ta mata zuwa kofar gida sai zugata take akan karta yarda ɗanta ya shiga gurin Inna Hamsatu, ita ma gashi ta ƙwace mata Yayanta ta raba shi dasu. Mama Hadizatu da wannan huɗubar kawarta kuma ƴar uwarta ta bata ta koma gida.
...
Cikin satin daga hidimar biki aka fara na suna inda kowa cikin dangin yayi ƙoƙarin kyautatawa ɗan uwansun da kuma ƴar uwarsu, daga masu bada tinkiya sai sabulu sai atamfa, haka suka tara musu kayan barka.
Ranar suna suka raɗa yarinya suna Zaina kamar yadda mahaifinta ya raɗa mata, wanda wasu suke ce mata kwantacciya.
Hashim kullum yana maƙale a gidan kusa da ita, idan ya zauna kawai idanu yake zuba mata yana kallo ko motsi ba ya yi sai an mishi magana.
Yau suka cika wata ɗaya da har Zaina ta fara buɗe idanunta. Karfe bakwai da rabi Hashim ya shigo gidan cikin shirin makaranta da suna ajin karshe na Firamare.
Cikin falon ya shiga da sallama ya samu Inna Hamsatu ta gama yiwa Zaina wanka tana saka mata kaya.
Har ƙasa ya durƙusa ya gaisheta, yana ƙarasa wajenta ya zauna yace.
"Inna ki ban ita mu gaisa zan tafi makaranta."
Murmushi tayi ta gama saka mata kaya, ta nannaɗeta a towel ta ɗaura masa saman cinyarsa.
Kamar kullum ido ya zuba mata yana kallon cikin kwayar idonta da baƙin yake brown, ita ma shi take kallo kamar ta sanshi sai kifta idon take. "Inna tana da kyau, idan an tashi zan sayo mata kayan wasa."
Hashim yace ya miƙa mata ita, ta karɓa ta kwantarta cikin gidanta tace.
"Ka kashe kuɗinka kamar sauran ƴan uwanka, ba abinda za ta yi dashi."
Bai ce mata komai ba ya fita taci gaba da aikinta.
Karfe sha biyu da rabi suka dawo gida bai shiga gidansu ba ya biyo su Ado da Tahiru suka shigo, bayan sun gaishe da Inna Hamsatu. Hashim ya ciro jakarshi ya ciro ƙaramin motar wasa ya nufi gurin Zaina dake bacci ya ajiye kusa da ita.
"Inna ga kayan wasanta, gobe zan ƙaro mata wasu, kuɗin Ashirin ne na kashe goma."
Murmushi tayi tace. "To ta gode, amma ai na ce ka kashe duka."
"Ina so itama ta fara wasa dashi."
Daga nan ya fita ya nufi gidansu, ya samu yayunsa maza ukun da a sakandare suke sun dawo har sun cire kayansu.
Mama Hadizatu sai tambayarsu take ina Hashim, suka ce suma basu sani ba.
Sallamar shi ya sata nufoshi ta kai kishi bugu, ya saka kuka sai bala'i take masa ina yaje.
"Gurin Kwantacciya naje."
Yace yana ci gaba da kuka.
Kunnenshi ta riƙo ta murɗa, ya fasa ihu yana bata hakuri tace.
"Bana hanaka zuwa gidansu ba, ka ƙara zuwa sai na cire ma kunne ɗaya."
"Ba zan ƙara ba kiyi hakuri Mama."
Yace yana rokarta, ta sakeshi sai bala'i take ya wuce ɗakinsu ya ci gaba da kukanshi, ya cire kayansa ya fita yayi alwala ya gabatar da sallah ya kwanta gurin, haka bacci ya kwashe sa.
Karfe huɗu da rabi ya tashi ya fita, ya samu Mama Hadizatu bakin barandarta ya ƙarasa wajenta ya zauna nesa da ita.
"Mama yunwa nake ji ba tuwo."
"Au da kaje gidan ƙanwar uwarkan bata ba ka ba." Ta faɗa tana harararsa.
Kai ya girgiza mata, ta jawo kwano gefenta ta miƙa masa, ya karɓa a inda yake ya fara ci, tas ya cinye yakai kwanon bakin murhu ya sha ruwa ya wanke hannunsa, ya koma gurin Mama yace.
"Mama zanje gidan su Adda Adama."
Kallonshi tayi ta ɗaga mishi kai, ya miƙe da saurinsa ya fita.
Maza iyayensan suna kallonshi daga inda suke zaune bakin ƙatuwar bishiyar dake ɗauke da ganyayyaki luf.
Leƙe leƙe yake yayi wuf ya faɗa gidan Inna Hamsatu da sallama, ya sameta bakin rijiya tana wanki ya zo kusa da ita.
"Inna kawo in miki shanya."
"Ba zaka iya ba."
Tace tana ɗauraye kayan Zaina, ya saka hannu ya ɗauka ya fara shanya mata tana ɗaurayewa, har ta gama na Zaina saura nata tace ya bari ya masa girma, yace to ya wuce falon ya samu Zaina ta farka tana ƙananan kuka, ya ƙarasa kusa da ita ya ɗauketa ya fito waje sai tangal tangal yake zasu faɗi, da sauri Inna ta tareshi ta karɓeta.
"Za ku faɗi ai Hashim."
"Inna kuka take son yi."
Yace yana turɓune fuska, ta dubeshi tana mamakin son da Hashim yake yiwa Zaina.
Abincinta ta bata tasha kafin ta koma falon ta kwantarta cikin gidanta, tace Hashim ya zauna ya lura da ita ta fita taci gaba da aikinta.
Da wuri Hashim ya koma gida don kar Mama Hadizatu ta nemeshi inda yaje.
Cikin sati biyun duk a ɓoye Hashim yake zuwa gidan Inna don ganin Zaina. Da safe idan zai wuce makaranta zai shigo ya gaisheta ya duba Zaina, haka da yamma idan sun dawo zai shiga ya ganta ya koma gida da wuri dan kar yayunsa su rigashi dawowa.
Kuɗin makarantar sa da ake basa naira ashirin zai raba goma ya sayawa Zaina kayan wasa wani ƙananan mota wani roba ya kawo mata, duk da Inna ta hanashi goma ya kashe.
Wata rana Inna ta shiga gidan Baba Fatime ya dawo daga makaranta ya samu bata nan ba Zaina, duk da yunwar da yake ji haka ya zauna jiranta har la'asar kafin ta shigo gida ta sameshi har yayi bacci a gurin.
Kwantar da Zaina tayi ta zo ta tashesa, yana jinta ya miƙe da sauri yana cewa.
"Inna ina Zain?"
"Tana bacci, ya ka zauna a anan ka ga ko kayan makaranta baka cire ba."
Cikin falon ya shiga ya buɗe jakan makarantarsa ya ciro sweet da ya saya Zaina, ya ajiye mata ya kalli Innah da ta shigo yace.
"Bari inje gida kar Mama ta nemeni."
Daga haka ya fita a ɗakin ta bishi da kallo.
A hankali ya buɗe kofar gidan sun ya shiga, bai gama shiga ba ya ji an cafkosa an hau dukanshi.
Mama ce ke dukan shi tana bala'i akan me yasa zai tafi gidan Hamsatu ko ya ga ita tana zuwa.
Kuka yake yana rokonta ta rabu da shi, Baba ya shigo gidan ganin abin da ke faruwa da saurinsa ya isa gurin ya hanata ya ƙwace Hashim hannunta yana cewa.
"Lafiyarki Hadizatu, me ya miki haka kike dukanshi kamar an aiko ki?
"Gidan Hamsatu yake zuwa, kuma na hana shi duk yaran dangi da suka cika unguwar nan bai ishesa su yi wasa ba sai gurin jaririyar yarinya." Ta faɗa da bala'i.
Ran Babane ya ɓaci da jin maganarta yace. "Ba zaki hana Hashimu zuwa gidan Hamsatu ba, sanin kanki ne maihaifiyar mijin Hamsatu Baba Fatime tamkar uwa take a guri domin ita ɗin kanwar mahaifanmu ne, ita ɗaya ta rage mana, to mai yasa zaki hanashi zuwa gurin ƴar uwarsa, ban yarda ba ki ji."
Daga haka Baba yaja hannun Hashim suka yi bakin rijiya ya wanke mishi fuska, ya karkaɗe masa jiki suka zauna a taburma da Mama Hadizatu ta shimfiɗa, ya zuba musu abinci su kaci tare.
Tun ranar Hashim ya samu abin da yake so, Baba ya barshi yana zuwa wajen Zaina.
Cikin haka Zaina ta shiga wata shida in da ta fara zama. Duk cikin yayunta tafi sabo da Hashim da shi kaɗai take gani kullum, wanda yake sata gaba ya baza mata kayan wasanta da ya tara mata, yayi ta mata wasa da shi tana dariya.
Idan yana son tsokanarta idan ya zo to ya ƙi kulata, tuni za ta dinga miƙa masa hannu kamar ta tashi don ya ɗauketa, idan kuma ya ƙi to za ta fashe da kukan da ko Inna ta lallasheta bata shuru, sai shi ɗin ya ɗauketa yana lallashinta kafin tayi shuru.
A cikin watanni shidan su Hashim suka rubuta jarabawar gama Firamare, ya shiga aji ɗaya na sakandare inda yayunsa suke da sauran ƴan uwasa, wasu sun kusa gamawa wasu suna tsakiya wasu yanzu suka fara.
Zaina shekararta ɗaya da watanni uku ta fara takawa ga hakora da ta fara, ranar da Hashim ya dawo yaga ta taka tsalle da murna yayi tayi ya ɗauketa tana wangale masa baki yana mata wasa.
Shekaran Zaina huɗu a duniya inda Hashim ya shiga aji uku na Sakandire, ya girma yayi wayo shekarunsa goma sha uku a duniya, tsakanin sa da Zaina sai shaƙuwa mai ƙarfi da ya ƙara shiga tsakaninsu, sosai take son yayantan shi ma kuma hakane cikin zuciyarshi da idan ya fara kallonta baya kiftawa wanda tun tana ƙarama ta lura da hakan.
Duk yanda Mama Hadizatu tayi don raba Hashim da Zaina tayi amma bata samun riba ba, don Baba ya hanata yin komai wanda ta haƙura ta zauna amma ƙasan ranta lokaci take jira yazo da za ta rabasu.
Hashim kullum idan zai wuce makarantar boko sai ya biya yaga Zaina, wanda da kuka suke rabuwa don cewa take sai ta bishi yayi ta lallashinta.
Yau tun safe ta zauna jiranshi, bayan ya shigo ya iso gurinta yace zai wuce makaranta me zai kawo mata.
Murmushinta mai kyau ta yi tace."Sweet nake so yau."
"An gama Zain." Ya ce yana murmushi ya miƙe ya fita don bai ga Inna ba bare ya gaisheta.
Yana fita ta saka takalminta, kanta da hula dama, ta bi bayanshi bata ganshi waje ba sai masu irin uniform dinsa data gani ta dinga bi har kofar makarantar, ta shiga cikin makarantar ta fara kalle kalle, ga yara maza da mata manya da yara sai shawagi suke cikin makarantar gwanin sha'awa
Wani mugun son shiga cikinsu ne ya kamata da son kasancewa cikinsu, ta fara bin ƙananan yaran da kallo.
Kamar daga sama taji muryar Hashim yace."Zain!"
...
Comments
Share


KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now