3.

232 26 2
                                    

  KWANTACCIYA 3
(2nd Edition)
  Pharty BB

Da sauri Hashim ya ƙarasa wajen Zaina yana cewa."Me ya kawo ki? Ke dawa ku ka zo? Me kike yi anan?"
"Gurinka na zo." Zaina tace tana kifta masa ido kamar za ta yi kuka.
"Inna ta sani?" Ya tambayeta yana ɓata rai.
Girgiza masa kai tayi, yaja hannunta suka nufi hanyar fita. Tana ganin haka ta fara turjewa tana fashewa da kuka.
"Mene ne kuma? "Yace yana tsayawa.
"Nima ina son makaranta." Ta ce kamar ta yi kuka.
  Da mamaki yake kallonta, sai kuma ya ja hannunta suka nufi wajen Sargent bai ce mata komai ba, Sargent ya bishi da kallo yace. "Ina zuwa za'a shiga aji."
"Don Allah ƙanwata zan maida gida ta biyoni." Hashim ya faɗawa Sargent.
"Lokacin shiga aji yayi babu inda za ka je, ta zauna ta jiraka a kofar ajinku." Faɗin Sargent yana ɓata rai.
Jin abinda ya faɗa yasa Hashim kama hannun Zaina suka nufi ajinsu, ya zaunarta waje bakin baranda ya ce."Ki zauna anan yanzu zamu fito kar kije ko'ina."
  Kai ta ɗaga mishi ya wuce cikin aji ya zauna, anan malami ya shigo ya fara musu karatu.
  Zaina tana jin sabuwar karatu da yaren da bata taɓa ji ba ta miƙe tsaya ta tsaya daf da window, tana hango duk abin da malamin yake koyarwa, da sun haɗa ido da Hashim ta mishi murmushi shi kuma ya ɗauke kai yana mata alama ta zauna sai ta make kafaɗa.
  Haka har aka fita break. Hashim da saurinsa ya fito ya sameta ya ce.
"Ba nace ki zauna ba."
  Zaina wiki wiki ta yi da ido ta ce.
"To ai ina son nima na koya abin da ake koya muku."
  Hararta ya yi ya ce."Ba za ki iya ba kuma ba za'a barki a gida ba, zo muje in saya miki abu."
Daga nan ya ja hannunta suka nufi gurin saida sweet, ya saya mata na goma ya sayi na goma, anan suka haɗu da yayunshi da kuma su Ado.
Muhktar da yake babban cikinsu da yaga Zaina yafi kowa mamaki, don sanin ahlinsu da mace ba ta zuwa makarantar boko ga Zaina ta zo.
Hakan yasa ya ce. "Ke Zaina waye ya kawo ki? Hashim kai ne?"
  Da sauri Hashim ya girgiza kai ya ce. "Biyo ni tayi ni ma ban sani ba."
  "To wallahi ana tashi ka san yadda za tayi ta koma gida ba wanda ya ganta." Mukhtar ya faɗawa Hashim, ya juya gurin sauran ƙannensu ya ce. "Kar kowa ya faɗa a gida, kun ga dai ita ta zo da kanta."
Kai suka ɗaga mishi, ya juya ya kalli Zaina da ta shanye sweet nata ta karɓi na hannun Hashim tana sha ya ce."Ke kuma na ƙara ganin kafarki cikin makarantar nan sai na karyashi, wuce ki bani guri."
Ganin yana shirin kai mata duka ta shige bayan Hashim ta ɓuya, sosai Muhktar yama Hashim faɗa kafin a koma aji.
  Hashim yaja hannunta suka nufi ƙofar ajinsu ya ce ta zauna a waje ta jirashi. Ƙin zama tayi ta tsaya ta window tana leƙan mai ake koyar musu, duk da ba ganewa take ba amma haka kawai take jin daɗin yaren.
....
  Can gida hankalin Inna duk ya tashi ganin kusan awa biyu ba Zaina ba labarinta, mayafinta ta ɗauka ta shiga cikin gidan ƴan uwa ko ta zo, amma ba ita ba alamarta haka ta dawo gida cikin tashin hankali, ta zauna jiran Baba ya dawo ta sanar da shi asan abin yi.
Ƙarfe ɗaya aka tashi su Hashim, ya fito ya riƙe hannun Zaina suka kama hanyar gida.
  Zaina kamar ta yi kuka ta ce. "Ya Hash yunwa nake ji?"
Hashim ya ce mata. "Ki yi hakuri mun kusa isa gida."
  Kai ta ɗaga mishi su kaci gaba da tafiya har cikin unguwarsu, sai binsu da kallo ake musamman ƴan matan da suka san ana neman Zaina.
Gidansu Zaina suka shiga tare da sallama. Inna ta ji muryar Hashim ta tashi da sauri ta nufe shi tana faɗin.
"Hashim ina Zaina?"
  Ganinta bayan Hashim yasa ta fincikota ta kai mata bugu, wanda zafin shi ya saka Zaina sakin kuka da ƙarfi. Hashim yana ƙoƙarin tareta Inna ta hanashi ta kwakkwaɗa mata mari sai kuka take.
"Na ƙara ganin kin fita ba ki tambayeni ba, ina kika je ma?" Ta watsa mata tambaya.
"Gurin Ya Hash." Zaina ta ce tana kukan da taɓa zuciyar Hashim yake ba kaɗan ba.
"Ki ka je yin me?" Inna ta tambayeta da tsawa.
Hawayenta ta share ta ce. "Koyan abin da ake koya musu."
  Da mugun mamaki Inna ta kalleta, kafin ta riƙo kunnuwanta ta murɗa ta ce.
"Bari ki ji na faɗa miki, ba ƴa mace da ta taɓa karatun boko duk ahlinmu ko kinga sauran matan suna zuwa? To ba za'a fara akan ki ba, abin magana za ki jawo min Zaina tun kina ƙaramar ki? To ba ki isa ba kinji ko ba ki ji ba?"
"Na ji." Zaina tace tana runtse idanunta don zafi.
Inna ta saketa ta koma kan Hashim, shi ma faɗa ta mishi sosai kafin ta barsu nan gurin ta shige falo tana juya maganganun ƴarta.
Hashim kusa da Zaina ya matsa ya riƙo hannunta, ta kwace ta ce.
"Ka rabu dani, kana gani ai Inna tana dukana ba ka ba ta hakuri ba."
"Kina gani nima faɗan ta min Zaina." Ya faɗa cikin kwantar murya.
Ƙin kulashi tayi ta zauna bakin baranda, ya zauna kusa da ita ya yi ta lallashinta har ta sauƙa kafin ta ce. "Yunwa nake ji har yanzu."
Tashi ya yi ya duba bakin murhu ya ga babu abinci. Ya ce mata. "Ina zuwa."
  Ya fita da sauri, gidansu ya shiga ya haɗu da Mama, da ya gaisheta ta amsa taci gaba da aikinta don tasan daga inda yake.
  Ɗakinsu ya shiga ya canza kaya ya fito, ya ga kwanon abincin sa da su Muhktar suka ci sun ajiye mishi, ya ɗauka ya fita da sauri sai gidan su Zaina, ya sameta har ta fara hawayen yunwa Inna na jinta ta ƙi kulata.
Kusa da ita ya ajiye kwanon yace. "Dai na kuka ga abincin ki ci."
Hawayenta ta share taja kwanon abinci ta buɗe ta fara ci.
Shi ko Hashim ya zuba mata ido yana murmushi, har ta kusa cinyewa ta miƙa masa sauran.
"Kai ma ka ci na ƙoshi."
Babu musu ya karɓa sauran, ya cinye tas, suka je bakin randa ya zuba musu ruwa suka wanke hannunsu kafin yayi alwala ita ma yana nuna mata ta yi, yace ta ɗauko hijabinta suyi sallah.
  Ɗaki ta shiga ta ɗauko ta fito, ya tayar kabbara ya fara yi, yana yi tana binshi har suka idar, lokacin makarantar islamiyya ya yi suka tafi.
Da suka taso ya mata rakiya har ƙofar gidansu kafin ya shiga nasu gidan. Sai dare ya dawo suka ci tuwon dare da Baba kamar yadda suka saba.
Washegari Hashim ƙin biyawa gidan Inna yayi don kar Zaina ta bishi, haka ya wuce makaranta.
Zaina tun da ta tabbatar lokacin tafiyar shi ya yi ta zauna jiran shi, duk Inna ba ta lura da ita ba don tasan faɗar da ta mata jiya ba zai sa taje ba.
Aiko Zaina na ganin wucewar Inna ɗaki ta fita da gudunta, gudu take har bakin makarantar da an kusa shiga aji, ta fakin idon Sargent ta shige da sauri, ba ta nufi ko'ina ba sai bakin ajin su Hashim, tana fara ƙoƙarin shiga ya hangota ya fito da sauri.
"Me kuma ya kawo ki? Ba Inna ta hanaki ba? Ba kya tsoron duka?"
"Ni ma so nake na koya abin da ake koya muku." Zaina tace tana ɓata fuska.
"Ki je gida za ina koya miki." Ya faɗa cikin ɓacin rai.
Ita ma ɓata rai ta yi ta ce. "Ni ba zan je ba anan nake son yi."
Rai ya ɓata cikin faɗa yace."Ki tafi gida nace."
Ƙin mishi magana ta yi ta zauna bakin barandar ajinsu, aji ya koma ya zauna ya rabu da ita.
  Haka ta ci gaba da zama har malama tazo shiga ta ga Zaina zaune, ta ƙarasa kusa da ita.
"Me kike yi anan?" Ta tambayeta.
Ɗago kai Zaina tayi ta kalli malamar tace. "Gurin yayana nazo, ni ma ina son koyan abinda ake musu."
"To ki je ajinku mana, ga can ɓangaren yara." Cewar malama ta nunawa Zaina ajin ɗalibai yara sa'anninta. Miƙe ta yi ta nufi gurin su, malama ta miƙe ta shige aji.
Zaina na zuwa ba ta tsaya tambaya ba ta shige cikin ajin, cikin sa'anninta ta samu guri ta zauna.
Malami ne ya shigo ajin ya hango Zaina da kayan gida ya mata alamar ta zo da hannu, ta tashi ta isa wajensa, ya dubeta cikin sakin fuska yace. "Ina kayan makarantar ki?"
Babu shakka ko tsoro ta ce."Yau na fara zuwa bani da shi."
"To kiyi kokari a ɗinka miki kinji." Ya faɗa mata.
Kai ta ɗaga mishi ta koma ta zauna.
  Harufan turanci aka koya musu, suna yi cikin wake don saurin ɗauka suna tafi, inda Zaina ma ta yi ƙoƙarin koyon wasu harufan farko cikin ABCD.
Ana fita break Zaina ta ga ko wani yaro ya tashi ya ɗauki cooker na abincinsa, ta fita da gudu wajen Hashim ta hango shi sai nemanta yake, yana ganinta ya ƙarasa wajenta.
"Ina kika je?"
"Can aji, mu ma an koya mana karatu." Ta faɗa mishi cikin murna.
"Ba nace miki ki koma gida ba."
Cikin damuwa ta ce. "Ni ka ga Ya Hash yunwa nake ji, ka ga kowa abinci yake ci."
Kallonta ya yi yanda ta ɓata rai ya sa shi jan hannunta suka yi gurin sayar da abu, ya siya mata biscuit na goma da ruwa biyu ya ba ta ya riƙe ruwa ɗaya.
Tas ta cinye tasha ruwan, suka koma bakin ajinsu Hashim ya dubeta yace.
"Kar ki ƙara biyo ni? Ko kin san Inna za ta dake ki amma kika zo."
  Za ta yi magana ya ce."Rufe min baki, idan kika ƙara biyo ni sai na dake ki."
Kallon shi ta yi da jin sai yau ya fara faɗa mata kalmar duka, ya ware mata manyan idanuwanshi yace.
"Yes dukanki zanyi ban taɓa ba ko? To zan fara."
Shuru tayi ganin ya haɗa rai, ta ɗauke kanta. Haka har aka koma aji ya shiga ya barta zaune, ita ma ta gudu aji da ta mayar nasu.
Karfe sha biyu aka tashi ƴan yaran, ta fito tana ta karatun lissafi da aka koya musu daga ɗaya zuwa hamsin, wanda da ƙyar ta iya koyar ɗaya zuwa goma sha.
Bakin ajinsu Hashim ta zauna jiransa, yunwa ma take ji sosai haka ta zauna jiran shi har aka tashesu.
  Bai kulata ba yayi gaba ta bi bayan shi. Haka suka isa gida, shi ya fara shiga wanda sai yace ta jirashi kofar gida. Ai kuwa da Inna ya fara haɗuwa, cikin ɓacin rai  tace. "Ina Zaina?"
Cikin kwantar murya ya ce. "Inna don Allah kar ki daketa, na mata magana ba zata ƙara zuwa ba."
"Wato binka tayi yau ɗin ma?" Ta tambaye shi tanansake ɓata rai.
  Shuru ya yi bai ce komai ba, Zaina ta shigo da gudu jin shuru ga yunwa yana cinta. Tuni Inna ta cafkota ta nufi falo da ita. Hashim ganin haka ya bi bayanta tare da su Ado da Tahiru da suka shigo, kulleta tayi ciki ta fito tace.
"Na ga ta inda za ki ƙara fita, ƙaramar yarinya dake za ki jawo min magana ciki dangi ban isa ba."
Kallon su Hashim da Ado ta yi tace.
"Ku wuce ku bani guri ku kuma."
  Sum suka bar gurin banda Hashim,vcike da tausayin Zaina ya ce."Inna ba ta ci komai ba, yunwa take ji."
  Cikin tsawa Inna ta ce. "Za ka bar gurin nan ko sai na ɓata maka rai."
Kafarshi yaja yana barin gurin. Inna ta koma ɗaki ta samu Zaina zaune tana ƙirga yatsun hannunta, tana faɗar kalmomin da take ji bakin su Ado da kuma wanda aka koya musu yau.
Zama tayi tana kallonta tace. "Tashi kije ki ɗauki abinci ki zo ki ci."
Zaina tashi tayi ta fita, ta je bakin murhu ta ɗauko kwanon ta dawo falon ta zauna ta fara ci, da ta gama ta fitar ta dawo gurin Inna ta ƙi kulata.
Har lokacin islamiyya ya yi ta fita a gidan, a hanya ta haɗu Hashim.
Da sauri ya ƙarasa wajenta ya ce. "Inna ta dake ki."
Girgiza kai ta yi ya kama hannunta suka ci gaba da tafiya.
Da dare Baba yana zaune Hashim gefen shi suna cin abinci. Inna da Zaina suma suna cin nasu, bayan sun gama Hashim da Zaina suka ɗauke kwanukan.
Inna ta dubi Baba tace. "Baban su Ado ka ma Zaina magana, na daka na daketa ta ƙi ji ta ƙi bari. Yau kwana biyu tana bin Hashim makarantar boko, da na mata magana wai ita ma koyar abin da ake koya musu take son koya."
  Cikim mamaki Babayana duban Innaya ce. "Ita Zainar? Yaushe ta yi wayon haka? Ko yaushe tasan hanyar makarantar?"
  Kai Inna ta ɗaga mishi dai-dai lokacin su Hashim da Zaina suka dawo wajen su.
Baba yaja Zaina ya riƙo kunnenta, ta fasa ihu ya kai mata duka. Hashim da sauri ya shiga tsakinsu dukan ya sameshi a kafaɗa, ya runtse idonsa don zafin dukan, ya riƙe Zaina da sauri wacce ta runtse ido.
Sakinta Baba ya yi ganin haka, Zaina ta kamkame Hashim tana kuka sosai.
Cikin tsawa Baba yace. "Na ƙara ganin fitar kafarki gidan nan da sunan zuwa makarantar boko sai na karya shi, ba za'a fara a kanki ba."
Kuka kawai Zaina take yi, cikin kukan tace. "Baba akwai fa mata suna zuwa, yau ma har karatu mun yi."
Da sauri ya katseta yana shirin kai mata wani dukan ta sake kankame Hashim, cikin jin haushi ya ce.
"Rufe min baki ko in buge shi. Me mace za tayi da karatun boko bana addini ba, duk yaran da ki ka ga suna zuwa karatun boko ba abin kirki yake kaisu ba."
"Baba amma..." Zaina ta ce za tayi magana Inna ta daka mata tsawa."Ana miki magana kina yi."
  Shuru Zaina ta yi ba don taso ba ta taci gaba da share hawayenta. Hashim ya lallasheta ya ce ta daina kuka, kuma karta ƙara zuwa.
Kai ta ɗaga mishi ba don tana jin za ta fasa zuwa ba, don in dai wannan abun shi ne karatun boko to yanzu ta fara zuwa.
...
#comment
#vote

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now