6.

212 24 4
                                    

KWANTACCIYA 6
(2nd Edition)
Pharty BB

Sabon littafina GOBE DA NISA
#300 2028167156
First bank Fatima Bello Bukar
Evidence of payment
http://wa.me//+2347037487278
...

Hashim bai shigo gidan su Zaina ba sai gurin karfe takwas na dare, a bakin bishiyar ɗazu ya hango Zaina zaune da fitila a gabanta tana sallah kasancewar wutan waje ya daina.
Gurinta ya ƙarasa ya zauna har ta idar ta yi addu'o'i ta shafa, ya shafa yace. "Allah ya amsa me ki ka roƙa mana."
Tana murmushi ta ce. "Abubuwa da yawa."
Hasken wayarsa ya kunna ya haska fuskarta da shi yace. "Gobe zan koma bakin aikina."
"Sai yaushe? Ka san dai zan yi kewarka? Kuma idan ka tafi ba ka dawowa da wuri." Ta tambayeshi idanunta ƙasa ganin nashi idanun yana wayo a fuskarta.
Murmushi yake yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskar Zayn ɗinsa ya ce. "Sai kuma na samu lokaci na zo ganin ƙanwata, ni ma ya zame min dole ne, da babu abin da zai sani yin nesa dake kin sani."
Murmushi ta yi cikin farin ciki tace. "Da ma Ya Hash ina son maka magana akan karatuna, ka yiwa Baba Fatime magana ina son cigaba, ka ga dai na samu score da results mai kyau."
"Kina ganin zasu yarda da hakan Kwantacciya." Ya tambayeta.
Cikin ɗan shagwaɓa ta ce. "Ni dai don Allah ka taimaka ka mata magana, nasan in Baba ne ba zai yarda ba balle Inna da bata so."
"Shikenan tashi muje mu sameta yanzu." Ya faɗa yana ƙoƙarin tashi.
Zaina idanuwanta ta zaro tana kallonshi da suke mutuƙar masa kyau tun ba yau ba, ta ce. "Ni dai ka je kai ɗaya."
Komawa ya yi ya zauna yana cewa. "Shike nan ba ki damu ba kenan."
"Allah na damu, muje to." Tace ta miƙe shi ma ya miƙe suka fita a gidan.
Tafe suke shuru tsakanin su wajen mintuna sannan tace. "Ya Hash na tambaye ka?"
"Ina jinki Zayn." Ya faɗa mata cike da kulawa.
Da damuwa ta ce. "Me yasa wasu ke ƙirana da Kwantacciya."
Shuru ya yi, hakan ya sa ta dubanshi wanda farin wata ya ba ta damar kallon fuskarshi, ganin haka ya ce yace. "Ba zance miki ga dalili ba, amma tun nima bani da wayo naji sunan wajen Mama da Adda Adama kafin a haifeki, amma ki tambayi Inna za ta sani."
Kai ta gaɗa mishi su kaci gaba da tafiya har gidan Baba Fatime, suka shiga da sallama.
Jikokinta da suke tare da ita suka amsa musu, suka samu guri suka zauna, ƴan matan sai bin Zaina da kallo suke don maganganun da iyayensu ke faɗa a kanta.
Ganin irin kallon da suke mata yasa Hashim tashi yace. "Let's go inside Zayn."
Tashi ta yi tabi bayan shi suka shiga cikin ɗaki suka samu Baba Fatime, guri suka samu suna gaisheta ta amsa. Ta tsufa sosai girma ya zo mata, murya ƙasa tace. "Kamar Kwantacciya da Yayana."
Hashim yana murmushi ya ce mata."Eh mu ne Baba ya kike?"
"Lafiya lau Yayana, ya wajen aikin fatan komai lafiya?" Ta faɗa mishi tana tambayar shi.
"Lafiya lau Allahamdulillahi." Ya amsa mata.
Girgiz kanta ta yi ta ce. "Ga shi har na gama tsufana ina jiran mutuwata kai da ƴan uwanka duk ba wanda ya kai ni naga ɗakin Allah, sai karatu karatu da baya ƙarewa."
Murmushi ya yi yace. "Kar ki damu za ki je, amma Kwantacciya ce za ta kai ki bani ba."
Da mamaki ta ce. "Kwantacciya dai?"
Ganin ya fara samun nasara ya ce. "Eh in har za ki barta ko ki yiwa su Baba Lamiɗo magana akan ta ci gaba da karatunta."
Da sauri Baba Fatime ta ce. "Wani kuma karatu bayan wanda ta yi? Kai Yaya kana ganin dai duk ahlin nan ba wanda yayi boko sai ita, sa'anninta duk sunyi aure wasu da ƴaƴansu, wanda aka haifa ma daga bayanta ana shirin aurensu sai ita za ta tsaya karatun boko, idan har kai ba za ka mata maganar aure ba to zan aurarta ga wanda nake so, ga ƴaƴan yan uwa maza da yawa zan haɗata dasu."
Zaina za ta yi magana Hashim ya riƙe hannunta ya matse alamar ta yi shuru. Da sauri ya tari maganarta yace. "Allah ba ki hakuri Baba, amma ki saka a ranki ba za ki je makka ba."
"Akan me? Idan kai ba ka kaini ba ai sauran jikokina zasu kai ni." Ta faɗa tana ɓata rai.
Shi ma ya ɓata rai ya ce. "Da ma Kwantacciya nace miki za ta kai ki, albarkacinta zan kai ki. Amma tunda kin ƙi tayi karatu ta kai ki shikenan."
"Yaya bana son wannan wasan, wani irin karatu kuma bayan wanda ta gama. Kana ji dai har yanzu dangi maganarta suke." Baba Fatime ta faɗa cikin kwantar murya.
Ganin ya fara samun yardarta yana muryarsa ya ce. "Irin wanda nayi na gama shi za ta yi, abin da ya kaita kawai za ta yi wato karatu, ni na miki alƙawarin ba abin da zai faru domin na yarda da ita, maganar dangi da kuma ake yi in sha Allah wataran za ayi alfahari da abin da ta karanta. Ɗayan maganar kuwa kwana kusa za ki ji daga gare ni."
Baba Fatime kallon Zaina tayi da kanta yake ƙasa tace.
"Kwantacciya kin yarda da abinda Yayanki ya faɗa, kin zaɓi karatu akan aure."
Kai ta ɗaga alamar eh. Baba Fatime tace. "To shikenan na yarda amma da sharaɗin ba zan ji wani abun da bai dace ya fito daga gurinki ba, ko min sonki da karatu zan rabaki da shi in aurarki ga mijin da na jima da miki tanadin shi."
Kai Zaina ta ɗaga tace. "Na miki alƙawari Baba, babu abin da zai faru nagode sosai."
Juyawa tayi ta kalla Hashim, ta riƙo hannayensa tana murmushi tace. "Thank you so much Ya Hash, ban san da me zan saka maka ba."
"Bana buƙatar godiyarki, abin da za ki bani kuma idan na dawo zan sanar dake." Ya faɗa mata yana mata murmushi, tare da matse hannunta da yake cikin nasa yake jin laushinsu.
Murmushi ta yi ita ma, kafin su yiwa Baba Fatime sallama suka tafi gida, gidansu Zaina suka shiga suka samu Inna, ta bisu da kallo ta ce. "Daga ina haka?"
Zaina cikin murmushi ta ce. "Mun je gidan Baba Fatime ne, ta amince na ci gaba da karatu."
Wani kallo Inna ta watsa mata.
"Wato ke ba kya jin magana ba kya gudun abin magana ko Kwantacciya, kar ki jawowa kan ki bakin mutane, ko ina ka shiga maganarki ake akan karatunki."
Baki Zaina ta tura gaba ta ce.
"Ni dai Inna ki rabu dasu suce kome ma, amma ni da zanyi karatuna."
Tsaki Inna tayi ta bar gurin.
Hashim ya ƙarasa wajenta ya ce. "Fitar safe zan yi ba za ki samu ganina ba, zan bada sako a gurin Tahiru zai miki komai na makaranta, idan na samu zuwa nan da ƙarshen wata za ki ganni."
Kallonshi ta yi ta ɓata fuska kamar za ta yi kuka tace. "Ni dai kamar nabi ka."
Dariya yayi mata ganin yadda ta yi da fuska yace. "Kar ki damu soon za ki je."
Daga tsayen suka yi sallama ya tafi, ita kuma ta wuce cikin ɗaki, gefen zuciyarta ɗaya farin ciki za ta fara karatu gefe ɗaya kuma damuwa za ta yi rashin yayanta na kwanaki.
...
Hashim kam yana fita gida ya shiga ya fara haɗa kayansa, zuciyarshi shi ma damuwarce zai yi nisa da kanwar shi da ta zamto jinin jikinsa da numfashinsa, wanda yake ganin ita ce rayuwarshi.
Dole ya nema mata ƙaramar waya suna waya, kafin ya dawo mata da buƙatarshi wanda yake ganin ba zai sha wahala ba wajen samun amsarshi.
Sai da ya gama shirya kayansa tsaf ya kwanta, bai jima ba bacci ya ɗaukeshi. Bai farka ba sai asuba yayi alwala ya wuce masallaci, a hanya ya tari Tahiru ya ciro kuɗi cikin aljihunsa ya ba shi yace.
"Tahiru ga dubu talatin nan ka riƙe wajenka, idan admission ya fito Zayn ta samu abinda take so sai ka yi kuɗin zirga-zirga da shi kafin a fara registration zan aiko sauran."
Karɓa yayi ya saka a aljihunsa suka wuce gida.
Karfe shida ya sami Hashim a tashar mota, ya nemi motar Kaduna ya shiga suka kama hanya.
...
Da safe sukuku Zaina ta tashi, tunawa da Ya Hash ɗinta ya tafi ya barta sai kuma bayan watanni, ba za ta ƙara ganin shi ba sai dai suyi magana ta wayar Yaya Ado.
Kwata kwata ba walwala a fuskarta ta wuni, wanda Inna da ta ga hakan ta ƙi mata magana, haka tayi ayyukanta ta koma ɗaki ko abincin kirki ta kasa ci.
Cikin kwana biyun haka take wuni har ta sawa zuciyarta haƙurin rashinsa, amma lokaci zuwa lokaci tana tuna shi wanda tasan cire tunanin shi abu ne mai wuya a tare da ita.
Sati ɗaya da tafiyarshi aka kai sadakin auren Ado gidansu amarya, aka yanke ranar biki wata biyu masu zuwa.
Daga nan dangi suka shiga hada hadar biki, Ado ya fara gyara gidan da aka ba shi cikin unguwar ɗaki ciki da falo da kuma extra ɗaya, kuma kowanne da bathroom a ciki sai kitchen da store, gidan mai kyau da shi, yayi fenti ya gama komai aka kai kayan amarya aka jera.
Biki saura sati uku aka fara bada admission, Tahiru da ya ji labari ya samu Zaina ya faɗa mata ta shirya ya ɗauketa a mashin ɗinshi suka tafi Cafe ta duba taga an bata Islamic studies.
Kuka ta saka mishi tace ita bata so ya ƙira mata Ya Hash ta sanar mishi.
Wayarshi ya ciro ya ƙira Hashim ya miƙa mata ta karɓa ta kafa a kunnenta.
Daga ɓangaren Hashim yaga ƙiran Tahiru ya bar wajen aikinsa kenan ya samu ƙiran ya ɗauka yana sallama yaji Zaina ta fashe mishi da kuka.
A rikice yake tambayarta.
"Me ya faru? Me ya same ki? Wani abun aka miki? Please tell me kina tada min hankali."
Sai da tayi kukanta ta tsagaita tace.
"Ya Hash Islamic studies fa suka bani."
"Su wa kenan?" Ya tambayeta a rikice.
"Masu bada admission mana don Allah taya zan fara ni bana so na hakura da karatun." Ta faɗa mishi.
Cikin lallashiya fara faɗa mata .
"Inji waye ba zaki iya ba? Islamic studies ɗin ne ba za ki iya ba, ke da kike da sanin arabic sosai taya za kice ba za ki iya ba, ki saka a ranki za ki iya Insha Allahu za kiga kinyi ƙoƙari."
Zaina a hankalita ce."Amma Ya Hash."
"Please Zayn kar ki karaya mana." Ya ce da sauri cikin kwantar hankali.
Shuru tayi ta kasa magana sai da ya maimaita tace."Shikenan zan ƙoƙarta, to yaushe za ka zo."
Murmushiya yi tamkar tana kallon shi ya ce."Kinyi missing ɗina."
"Eh sosai."Tace cike da kunya.
"Soon za ki ganni kafin bikin Ado." Ya faɗa shi ma cike da kewarta.
"To Allah ya kaimu ya dawo da kai lafiya." Ta faɗa cikin farin ciki.
Ameen yace ya kashe wayar, ta dubi Tahiru ya harareta yace.
"Duk kin cika min kunne da kukan ki."
Ba ta mishi magana ba tayi gaba suka wuce gida ta samu Inna ta faɗa mata, jin fannin da Zaina ta samu gurbin karatu yasa Inna jin ɗan daɗi haka Baba ma da yaji fannin Islamic ne sai ɗan boko ya sa yaji damuwarsa ya kau akan karatunta.
Satin biyun da ya wuce satin da aka shiga aka fara hidimar bikin Ado.
Inna ta ɗinkawa Zaina kaya kala biyu da hijabinta irin kayanta dan cewa tayi bata da kuɗi ga auren Ado.
Shuru tun ranar laraba Zaina take zuba ido tana jiran ganin zuwan Hashim amma shuru har ranar asabar aka ɗaura auren Ado da Saruyya da yamma aka fara shirin kai amarya.
Kukan da Zaina tayi dan rashin ganin Hashim bai zo ba shi ya haddasa mata ciwon kai ta kasa bin masu kai amarya ta shiga can cikin ɗakin Inna ta kwanta kan gadonta taci gaba da kukan har bacci ya ɗauketa.
...
Ɓangaren Hashim kam tun da ya shigo yake raba idanu dan ganin ta inda zai hangota bai ganta ba, yan matan ba shiga cikinsu take ba dan duk yawwanci sunyi aure basa kulata yasa bai tambayesu ita ba.
Ga cikin gidansu da mata Tahiru da zai ce ya mata magana shima bai shiga cikin gidan ba dan saboda mata haka ya hakura har yamma za'a kai amarya ya fito ko zai ganta bai hangota ba har aka watse ya koma gida cike da damuwan ko mai ya sameta.
Zaina bata farka ba sai bayan sallar isha'i kasancewar tana hutu bata damu da yin sallah ba tayi wanka ta gyara jikinta ta nemi abinci taci ta koma ta sake kwanciyarta ta riga ta saka a ranta bai zo ba ta hakura.
...
Washegari lahadi aka fara wucewa zuwa gidan amarya wuni abunka da dangi ba'a bambance dangin ango da amarya kowa zuwa yake.
Inna data shiga ɗakin ta samu Zaina kwance idonta biyu tace.
"An fara tafiya gidan amarya ke ba za kije bane."
"Zanje sai anjima da yamma."
"To Allah ya kaimu." Inna tace ta fita.
Har la'asar kafin Zaina ta fita tayi wanka ta shiga ɗaki ta shirya cikin riga da skirt ɗinta tayi kwalliyar ta sama sama ta saka gogeggen hijabinta ta fita waje tama Inna sallama ta fita.
Yana zaune bakin dakalin kofar gidansu da sauran samarin yaga fitowarta da tun safe yake jira.
Da sauri ya tashi mazan gurin suka bishi da kallo wasu suna dariya ganin inda ya dosa sun san ya hango sanyin idaniyar shine.
Gurinta ya ƙarasa tare da sallama ta juya da mamaki tana kallonshi tace.
"Ya Hash dama kazo? Yaushe? Kasan kukan da ka sani yi?"
Kunnenshi ya riƙe alamar ban hakuri yace. "I'm really sorry, nayi ta zaman jiranki tun jiya baki fito ba."
"To ba kai ne baka nemi ni ba kasan yadda nayi ta kuka kwana nayi ina yi har zuwa safe." Ta faɗa tana tura baki.
Dariya yayi ita ma tayi dariyar suka ci gaba da tafiya yace. "Zan rama miki nima yau kwana zanyi ina yi ko in fara tun yanzu."
Girgiza kai tayi tana dariya tace.
"Na hakura amma ka sake sani kuka kai ma sai kayi."
"Na amince." Yace dai-dai suka tsaya kofar gidan amarya yace.
"Shiga ki fito mu koma gida."
To tace mishi ta wuce cikin gidan har ɗakin amarya suka gaisa bata wani jima ba ta fito suka koma gida.
A kofar gidansu Zaina suka tsaya ta ɓata rai tace."Yaushe kuma za ka koma."
"Gobe da safe."Yace ya ciro wayarsa ya saita camera dai-dai fuskarta yace."Kalla nan."
Ɗago kanta tayi ya ɗauketa kusan kala biyar, da ta gane hakan ta saka hijabi ta rufe fuskarta.
"Dan Allah ka goge banyi kyau ba."
"Idan na gogen zaki tsaya na ɗauke ki." Ya faɗa yana binta da kallo.
Shuru ta mishi ya rage tazarar dake tsakanin su ya matsa daf da ita, ƙasa ƙasa yace.
"Nafi son ganinsu haka zasu ɗebemin kewar rashinki kusa dani."
Zuciyarta ce ta dinga bugawa lokacin da ta ganshi daf da ita, tare da maganar da ya faɗa mata ya haddasa mata tsoro.
Ganin ta shiga ruɗu ya sashi barin gurin yana cewa. "Za ki ga sako a gurin Tahiru."
Ba ta ita iya ba shi amsa ba ta shiga cikin gida da saurinta.

#vote

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now