11.

174 24 5
                                    

KWANTACCIYA 11
(2nd Edition)
Pharty BB

Zaina tana shiga gida ta shiga ta falo ajiye jakarta a kujeran falo ta ji ƙara a ciki, da sauri ta buɗe jakarta ta ciro wayar tabi da kallo ganin mai ƙira, har ya katse ta kasa ɗauka.
So take shi ma ya ji mai taji da ta ƙira baya ɗauka har ya zo ya daina shiga.

Ƙira yake yana sake ƙira ta ƙi ɗauka, haka kusan sau biyar sai ga text message, ta buɗe ta gani saƙo ne na roƙo da lallashi akan ta ɗauki wayar.

Ba ta gama karantawa ba ya sake ƙira, ta ɗauka tana kafawa a kunne ba ta ce komai ba.
...

Naunanniyar ajiyar zuciya Hashim ya sauƙe jin ta ɗauka, cikin kwantar da murya yace. "My Zayn."
"Bana so." Zaina tace kamar yana gabanta ta ɓata rai.

"I'm sorry ni ne ko?" Ya faɗa cikin lallashi.

"Kai ne mana Ya Hash, ba ka da lafiya ba ka sanar dani ba sai dai inji a bakin Yaya Ado, wai har kwantarka aka yi, me yake damunka haka?" Ta ce kamar za ta fashe da kuka.

Murmushi Hashim yake daga ɓangaren shi, jin ta yi shuru yace. "Ciwon rashinki kusa da ni ne Zayn."

Zain rai ta ɓata tana tura baki ta ce. "Ni dai ka faɗa min me yake damunka?"

"Zazzaɓi ne kawai ya min mugun kamu kuma naji sauƙi, wayana kuma ya faɗi sai ɗazu na samu sabo." Ya faɗa mata.

Numfashi Zaina ta sauƙe sannan ta ce. "Allah kawo sauki, ni kam kana kula da kanka."

"In sha Allah. Ina Inna?" Ya tambayeta.

"Tana waje, nima yanzu dawowata daga makaranta, naje na kasa fahimtarta komai saboda bansan halin da kake ciki ba." Ta faɗa mishi da damuwa.

"Haka nake da muhimmanci ashe." Ya tambayeta yana murmushin jin daɗi.

Kai ta ɗaga kamar zai ganta ta ce  "Eh mana, kai ne fa Ya Hash ɗina."

Murmushin jin daɗi Hashim yayi yace. "Hakane kam, ni kuma ke ce My Zayn ba."

"Bana son sunan nan." Ta ce tana ɓata rai a shagwaɓe.

"To ki bani wani ina ƙiranki da shi." Ya faɗa mata yana murmushi.

Shuru Zaina tayi, can ta ce. "Ka ce min Zaina ko ka zaɓi wani."

Murmushi yayi har lokacin kamar tana ganinshi yace. "Shikenan idan na dawo zan ba ki wani. Zaina sunan ƴan gidane, ni kuma nawa daban ne don ba zan ba ki sunan da wasu zasu ƙiraki dashi ba, ina kishinki sosai."

Dariya Zaina tayi tace. "To Allah kaimu sai ka zo Yayana."

"Ameen."  Ya ce suka kashe wayar, sai lokacin taji hankalinta ya kwanta da ta samu yayantan ta ji muryar shi ta ji lafiyarshi.

Ba ta gama ajiye wayar ba ya ɗauki ƙara, taga numbern Moses da ta kasa saving, dauƙa tayi kafin tayi magana ya jefa mata tambaya. "Ke dawa kike waya haka ina ta ƙiranki line busy."

"Yayana." Zaina ta ba shi amsa kai tsaye.

"Yayanki? Wani irin yayanki za ku jima kuna waya haka? Kin san tsawon lokacin da na ɗauka ina ƙiranki." Ya tambayeta cikin ranshi yana jin wani iri.

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now