12.

151 26 3
                                    

KWANTACCIYA 12
(2nd Edition)
Pharty BB

Zaina tana shiga gidansu ta samu Inna ta ɗaura abincin rana, ta ajiye jakarta ta kama mata duk da tace ta bari ta ƙi, ta ƙarasa ta kwashe ta gyara bakin murhun ta ɗauraye kwanukan da aka yi amfani dasu.
Inna tana zaune tana murmushi da godiya ga Allah da ya bata ita, don Zaina ba dai tsafta ba, tasan mijinta ba zai yi kuka da ita don ƙazanta ba.
Bayan Zaina ta gama ta watsa ruwa ta yi sallar azahar, suna zaune tana cin tuwo Tahiru ya shigo gidan, ya gaishe da Inna kafin Zaina ta gaishesa, ya karɓi abincin Baba zai kai mishi ta ce za taje.
"Je ki ɗauko mayafinki." Yace yana miƙewa.
Hijabinta na kusa da ita ta saka ta cire ƙaramin na wuyanta, tana wanke hannuwanta sannan suka fita.
A saman mashin ɗinshi suka tafi har gurin aikin Baba da yanzu ya daina kafintanci, ya zama oga sai dai ya saka yaranshi.
Yana ganin Zaina yace. "Yau ke ce a gurin aikina Kwantacciya."
"Eh Baba ya aiki. Na gajine nace bari in rakoshi." Ta faɗa tana murmushi.
"Yayi kyau, ya makaranta?" Ya tambayeta.
Kai ta ɗaga mishi kawai ta ce. "Lafiya lau."
  Ba ta daɗe ba tace zata tafi, ya ciro ɗari biyar yace ta biya ta sayi kayan miyar dare yau ta hutur da ɗan aikensa.
Karɓa tayi ta wuce gida, a hanya ta tsaya ta saya kafin ta ƙarasa gida ta sanar da Inna, ba ta wani huta ba ta ɗaura abincin dare.
Daren ranar har taran dare ba ƙiran Hashim ba na Moses, abin duk ya dameta ga shi ta duba wayarta ba kati balle ta ƙirasu taji lafiyarsu.
Haka Washegarin ranar Lahadi har karfe goman safe ba ta ga ƙiran ko ɗaya ba, hakan yasa ta samu Inna tace ta bata kuɗi ta saka kati.
Inna tace. "Naira na ɗari uku, ki bari in Tahiru ya farka ki tambaye shi."
"To Inna ki ban mana idan ya bani in ba ki." Zaina ta ce cikin roko.
"Na ƙi, wa za ki ƙira? Hashim?" Inna ta tambayeta.
"Eh mana tun jiya ba muyi waya ba." Zaina tace da sauri.
"To ki jira shi idan ya farka ya ba ki, in ma ba shi dashi ya ƙira miki shi ku gaisa." Inna ta faɗa mata.
Baki Zaina ta tura tana shigewa ɗaki, ta ɗauki wayar nata tana niyar cin bashi ƙiran Moses ya shigo.
Da sauri ta ɗauka tana sawa a kunnenta tace. "Hello good morning."
Daga ɓangaren shi ya ce. "Morning Girlfriend yasu Mama."
"Lafiyansu lau." Tace tana kawar da maganarshi ta farko tana ƙara cewa. "Yanzu nake shirin ƙiranka sai nayi tunanin ko ka wuce."
"Ina kenan?" Ya tambayeta da mamaki.
"Church mana." Tace kamar bata so.
"Yau banje ba rabona dashi tun last week da ya wuce." Ya faɗa a hankali.
Daɗi taji cikin ranta don ta lura da sauye sauye cikin lamuransa, amma a fili tace. "Why ba ka zuwa?"
"Zan sanar dake idan mun haɗu, yaushe zamu haɗu ina son muyi magana mai muhimmanci?" Ya ce ƙasa-ƙasa.
"A school!" Ta ba shi amsa kai tsaye.
Da sauri ya ce. "No ina son zuwa gida, i told you maganar na da muhimmanci."
"Ba za'a barni ba, mu haɗu a school kawai." Ta ce a hankali.
"Bana jin yin haka saboda ina son maganar karya tsaya tsakaninmu." Ya faɗa in serious tune.
Da mamaki cike da tsoro Zaina tace. "Ban gane ba."
Bai damu ba ya ce. "Idan har mun haɗu za ki fahimce komai, ki bani dama kawai na zo gidanku."
Girgiza kai ta yi kamar yana gabanta tace. "Kayi hakuri amma hakan ba mai yiwa bane, zan jawowa kaina magana cikin dangi, idan har maganar na da muhimmanci ka sanar dani kawai idan mun haɗu a school."
"Shikenan Girlfriend sai mun haɗu gobe ki kularmin da kan ki." Daga haka ya kashe wayarsa kit.
Kashe wayar ta yi ta kasa ba shi amsa, tana juya maganganunsa ta ji wayar ya sake ƙara, duk tsammaninta shine ya sake ƙira ta ga Hashim ne.
Cikin sanyin jiki ta ɗauka, ta ji ya watsa mata tambaya murya a haɗe ya ce. "Ke dawa kike waya?"
Shuru ta yi ta kasa ba shi amsa, a ɗan tsawace ya sake cewa.
"Ina tambayarki kin mini shuru, ke dawa kike waya nace?"
"Classmate nawa." Ta kirkiro ƙaryar da ba ta san daga ina ya fito ba.
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe duk da ƙasan ranshi ya ji ya kasa yarda, da ƙyar yace. "Classmate shi ne za ku daɗe haka kuna waya."
"Eh munyi discussing na assignment ne." Ta faɗa a hankali jin muryar yayantan ya canza.
Shuru yayi jim, sannan can yace. "Ok Allah taimaka, amma Please next time idan dai na ƙira ko da waye kike waya ki yanke ki sanar dani, idan ba haka ba zuciyata tana zafi ina da kishi sosai akanki kin sani."
"To Ya Hash." Zaina tace duk muryarta wani iri don yanayinta, jin hakan yasa Hashim cewa. "Are You okay My Zayn?"
"Eh ina son na ɗan kwanta ne." Ta faɗa mishi a hankali.
"Fushi ki ka yi don na miki faɗa." Ya tambaye ta cikin kwantar da murya.
Da sauri ta girgiza kai kamar yana gabanta tana cewa. "A'a wallahi."
"Shikenan zuwa anjima zan ƙira ki." Ya faɗa ya kashe wayarsa. Ta zare wayar ta kashe.
...
Hashim cire wayarsa yayi a kunnenshi ya bi da kallo, kwata kwata yau ya kasa fahimtarta, kamar tana da damuwa. Yasan Zayn nashi sosai yasan damuwarta, yanayinta, komai za ta yi kaɗan zai fahimceta.
...
Zaina tunanin ta duk ya ƙare akan kalaman Moses, so take kawai ta gano kan maganar Moses amma ta kasa.
'Ko me zai faɗa mata da har sai yazo gidansu?' Ire-iren tambayoyin da tayi a kanta har washegari ranar Litinin ta shirya ta wuce makaranta.
Yau ma ba ta ganshi ya zo da safiya ba, har sai yamma da ta fito ta ganshi zaune saman motarshi, ta ƙarasa wajensa.
Moses ya zuba mata ido kawai, Bai taɓa tsammanin lokaci ɗaya za ta canza mishi ra'ayi da tsarin rayuwar shi da ya jima da ginuwa a kai ba, dole ya jinjina mata, bai zai taɓa yarda ya rasata ba har sai ya mallaketa.
Kasancewar ba sallama ta saba mishi ba da ta ƙarasa gurin shi tace mishi. "Good afternoon."
"Afternoon My Girlfriend." Ya faɗa mata yana murmushi.
"Bana son sunan nan." Tace tana hararanshi don ta lura tun jiya da shi yake ƙiranta.
Dariya yayi yace. "Ni kuma ina so don yanzu na soma faɗa miki."
Shuru ta mishi ta turo baki, ta zagaya ta shiga motar shi ma ya shiga yaja suna barin harabar makarantar.
Sun hau titi Zaina ta ce. "Har yanzu shuru ba ka sanar dani ba."
"Me kenan?" Ya tambaye ta.
Zaina ta ce. "Maganar da ka ce zamu yi mana."
Ya girgiza kansa ya ce. "Ai nace miki gida zan zo, sai kin bani damar haka."
Shuru ta yi kafin can tace. "Na faɗa maka hakan ba zai taɓa samuwa ba, zan jawowa kaina magana cikin dangina banda wanda yanzu ma ake yi a kaina, dangina wasu irin mutane ne da nasu ra'ayin daban da na kowa ka fahimce ni."
Jin abin da ta faɗaya jinjinakai ya ce. "Shikenan na fahimceki, to ki nema mana gurin da zamu zauna muyi maganar."
"Mu yi ta yanzu mana." Zaina tace, ta ga ya dubeta ya ɗaga mata kai bai ce komai ba yaci gaba da tuƙi.
A bakin titi ya yi parking, ya juya yana dubanta bai san ta ya zata ɗauki kalaman sa ba duk da yasha faɗar su cikin wasa, daurewa yayi ya ce."Za ki aure ni?"
Murmushi ta yi da jin maganar shi duk da ba cikin wasar da ya saba mata ba yayi tace. "Nasha faɗa maka addinina ya mini hani da hakan ka yi hakuri, kuma dangina ba zasu bar ni ba."
Da sauri ya katseta ya ce. "No Zaina kin sanar dani idan har na bar addinina za ki aure ni, kar kice min a'a ba za ki iya ba, na bar addinina na koma naki ba don ke ba sai saboda Allah da manzon sa, kar don danginki ki ƙi bin zuciyarki, na san ke ma kina sona."
Idanuwanta ta buɗe tana kallon shi da mamaki har ya gama maganarshi, sannan tace. "Ka bar addininka ka dawo addinin musulunci?"
Kai ya ɗaga mata ya mayar idonshi kan titi yace. "Sati biyu kenan da yin haka, tun da na tabbatar da gaske ki ke na rasa mafita, ina sonki sosai Zaina, ban taɓa tsammani zan bar addinina cikin sauƙi ba sai da kika zo rayuwata, Zaina nasan musulunci tun ina yaro ƙarami, abin da Momy ta min shi ya hanani karɓar musulunci bayan dawowata, amma yanzu allahamdulillahi soyayyarki tayi sanadin nuna min kuskurena na karbi Musulunci, fatan za ki karɓi soyayyata muyi aure duk da kin nuna ba za ki aure miji marar sana'a ba, amma don't worry everything will be fine."
Hawaye Zaina take sharewa da zuba zubo mata jin yau wai ta dalilinta wani ya bar addinin shi ya karɓi musulmunci, ita ko da me za ta saka mishi banda ta karɓi soyayyarshi ta nuna mishi so da kauna.
Moses kallon Zaina ya yi yadda take share hawayenta ya cire tissue miƙa mata, ta karɓa yace. "Stop crying mana Girlfriend kar hawayen ya ƙare."
Murmushi tayi haɗe da kuka wanda ya saka shi dariya, kafin ya mayar da hakalinsa kanta gaba ɗaya ya tsagaita dariyarsa yace. "Za ki aure ni."
Fuskarta ta rufe da tafin hannunta tana murmushi cike da kunya, duk da ƙasan zuciyarta tasan za ta fuskanci kalubale dayawa amma dole ta jure komai don samun cigaban soyayyarsu.
Farin ciki ne ya lulluɓe zuciyarshi yace. "Thank you so much Zaina."
Murmushi take yi har lokacin, ta juyar da kanta. Hakan yasa ya cire lock ɗin motar ta fita cikin sauri, ya bita da kallo yana murmushi tare da godewa Allah da ya sakashi cikin masu rabo da shiriya.
Daga nan gida ya nufa, bayan yayi parking ya ƙarasa falon, tun daga ma shiga yake jin faɗar Uncle ɗinshi ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
Tare da sallamar da ya fara zama a bakinshi ya shiga falon, babu wanda yaji don duk faɗar uncle ya cika falon.
Momynsa ya hango zaune gefenta da Jawad, tana sharan hawayen da yau ya ji zafin zubarsu, ya ƙarasa wajenta da sauri yace. "Me ya faru Momy?"
Kallon ɗantan ta yi ta girgiza masa kai tace. "Babu komai."
"Ni ne nan Moses." Muryar Uncle ɗinsu ya ratsa shi, ya juya ya mishi wani kallo ya ƙarasa wajen shi ranshi haɗe ya ce. "Me ta yi maka ka sakata kuka?"
"Kai za ka fara amsa min, ina kake zuwa tsawon 2weeks ba ka zo church ba, na san duk laifinta ne za ta hanaka." Ya ce cikin faɗa.
Da sauri Momy tace. "Wallahi bani na hana shi ba."
"Ni na hana kaina, na bar muku addininku na koma addinin gaskiya, fatan kai ma Allah shirya ka." Musa ya faɗa kansa tseye.
Tas Uncle ya kwashe Musa da mari ranshi ya mutuƙar ɓace, ya nuna shi da yatsa yace. "Ba ka isa ba, ba ka isa ka koma waccan addinin ka bar naka ba. Blessing kinji abin da yace, yanzu sai da ki ka yi yadda kika ja ra'ayinsa ya bar addinin shi, to shari'a ce za ta rabamu."
Momy kasa cewa komai tayi sai kallon Musa da take yi wanda ranshi a haɗe, yana duban Uncle ɗinsu.
Unlce ɗin ya nuna su da yatsa dukkansu yace. "Babu mu babu ku, bani ba yaranki blessing."
Daga haka ya saka kai ya fita. Musa ya buga tsaki yana wucewa ɗakinshi. Momy ta fashe da kukan farin ciki da Allah ya nuna mata wannan ranar.
Ɗakinta ta wuce ta share hawayenta ta wanko fuskarta, kafin ta fito ta nufi ɗakin Musa tare da Jawad da ya biyo bayanta.
Tura ƙofar ɗakinsa tayi bayan ta ƙwanƙwasa ta shiga, ta sameshi zauna yana duba wani littafin addini na turanci da shi yafi fahimta.
Guri ta samu ta zauna, ya rufe littafin ya kalleta alamar tambaya amma ta rasa ta ina zata soma tambayarshi, fahimtar hakan yasa yace. "Last two weeks ne da suka wuce na samu cousin ɗin Dady da maganar, shine ya haɗani da wani malami shi ya nuna min komai ya bani kalmar shahada, ya nemi in canza suna naƙi na bar Musa, shi ya bani wannan littafan zasu taimake ni."
Murmushi Momy tayi tace. "Yayi kyau, haƙiƙa naji farin ciki marar misaltuwa a raina, nagode Allah na godewa Girlfriend."
Kallonta yayi da mamaki yace. "Ta ya aka yi kika santa."
Murmushi tayi tace. "Na san duk ita ce sila."
Kai ya ɗaga mata yana juyar da kanshi. Murmushi ta yi tace. "Kana sonta sosai ko?"
Nan ma kai ya ɗaga mata, ta sake cewa. "To Allah sanya albarka, ka kawota mu gaisa."
To yace mata ta tashi ta fita, don har lokacin ya kasa sakewa da ita.
Tana fita ya jawo wayarshi ya ƙira Zaina.
...
Tana tsaka da aiki ba ta ji wayar yana ƙara ba, haka ya ƙirata sau uku ba ta ɗauka ba ya hakura.
Sai da Zaina ta gama aikinta ta samu lokacin ɗaukar wayarta, ta ga ƙiranshi ta duba taga ba ta da kuɗi, ta jawo jakarta ta samu canjinta naira ɗari biyu da Baba ya bata da safe ta saka hijabinta ta fita.
A baƙin titi ta siyo kati ta kamo hanyar gidan, tun a hanya ta saka ta ƙirashi ya ɗauka yana cewa. "Ina kika shiga Girlfriend ina ƙiran ki ba kya ɗauka."
"Ina aiki ne ban gani ba sai yanzu." Ta ce cikin murmushi.
"Ok ya gida ina su Mama yaushe zan zo gaisheta?" Ya tambayeta da tsokana.
Ido ta zaro tace. "Ba yanzu ba don Allah."
"Ni dai yanzu kinga har Momy tasan da zamanki." Ya ce cikin farin ciki.
Kunya ne ya kama Zaina ta kasa cewa komai.
Haka yayi ta janta da hira har ta ƙarasa gida tana jin wani farin ciki da soyayyar shi na shiga ranta.
....

Team Hash❤️
Team Musa🧡
Thank you masu comments #onelove Zaina tana godiya🤪

Keep liking and commenting ❤️
Pharty BB

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now