5.

233 27 0
                                    

KWANTACCIYA 5
(2nd Edition)
Pharty BB

Don mallakar sabon littafina
GOBE DA NISA
#300 2028167156
First Bank Fatima Bello Bukar
Evidence of payment
http://wa.me//+2347037487278
...

Bayan shekaru biyu.

A yau aka yaye su Hashim daga makaranta sakandare, sun yi taro makaranta ta tara iyayen ɗalibai dan taya su murnar kammalawa.
Baban Hashim da Baba Abubakar ne suka samu zuwa don ganin taron ƴaƴan sun Ado da Hashim, wanda sune suka gama, sai Zaina kaɗai da za'a bari sauran, sun riga da sun gama tuni.
Kasancewar abin nasu ya zo da hutun ƙarshen shekara, hakan yasa aka haɗa da taron canja aji inda ɗalibai daga ajujuwa da dama sun fito sunyi gabatarwa.
Ciki har da Zaina da take aji huɗu za ta tafi biyar, ita ce a gaba sai masu bi mata, haka ta yi nata suma suka yi.
Abin ya ƙayatar da iyayenta ganin ƴarsun cikin mutane tana yaren da tsakanin yayansu maza suke ji. Hashim yafi kowa jin farin ciki ganinta tayi fes abunta, don tun daren jiya har karfe sha ɗayan dare suna tare, shi ya wanke musu uniform ya musu guga kafin ya tafi gida.
Taro aka yi lafiya aka watse, Hashim ya fita da kyauta biyu na ɗalibi da yafi kowa zuwa makaranta baya fashi, sai kuma mai ƙoƙari. Zaina ta samu kyautar tsafta da ƙoƙari ita ma.
Haka aka gama taron aka watse suka tafi. Gidan su Zaina suka wuce, iyayensu mazan suka wuce wajen aikin su.
Abubuwan da aka bawa Zaina ta buɗe, ɗaya ciki yadin uniform ne da kuɗin ɗinki ɗaya kuma takardu da sweets, ɗiban sweet din dukka tayi ta ba Hashim.
"Ya Hash ga sweet nan, tunda takardu ba amfani za ka yi dasu ba da na ba ka."
Ɗaya ya ɗauka ya bar mata sauran.
"Ki riƙe min a gurinki wannna ya ishe ni, amma fa idan kina so ki sha."
Murmushi tayi ta kwasa ta kaiwa Inna tace. "Inna ke ma ki dauƙa."
Girgiza kai Inna ta yi tace.
"A'a ki ajiye a wajenki kawai, Allah sanya albarkar abin da kike karanta."
"Ameen Inna." Zaina ta ce ta wuce cikin ɗaki.
Inna tabi ta da kallo, ba don dole ba ba ta son karatun ƴartan ko don maganganun da yake yawo a cikin dangi, waɗanda ta toshe kunnuwanta daga ji.
Ƙaramar yarinya da bata san me rayuwa ba ake jifa da maganganu iri iri.
...

Cikin hutun da su Zaina suka samu Ado da Hashim suka dinga zirga-zirga da shiga da fice suka samu gurbin karatu a Polytechnic, don samun sauran ƴan uwansu da wasu sun gama suna degree, wasu suna shirin gamawa.
Ado ya samu Business administration Hashim ya samu accounting.
Sun biya kuɗi da komai cikin sati biyun aka fara karatu suka fita, kwata kwata ya daina samun lokaci a cikin satin sai kwana uku, shi ma kuma gurin Baba yake zuwa taya shi zaman shago, karatu suke sosai ba shi da isasshen lokaci.
Idan har ya tafi makarantar to idan zai dawo sai ya saya Zaina abun ci in dai ya gani. Inna ta mishi faɗan ta ce ko ɗan takardu yana saya zai mishi amfani, sai dai yayi murmushi yace. "Inna abuna na Zaina ne, da ma don ita nake nema."
Kullum ya faɗa mata haka sai dai tayi shuru ta rabu da shi, tasan mai raba Hashim da Zaina sai Ƙaddarar Allah.
Haka su Zaina suka cinye hutun su suka koma makaranta, ta shiga aji biyar na Firamare.
Shekarun su Hashim biyu suka kammala karatunsu, suka nemi gurbi cikin University inda Allah ya taimake su suka samu aji bibbiyu kuma abin da suka karanta.
Hashim ya zama ɗan gayu matashin saurayi ɗan shekaru ashirin da huɗu, duk wani tsarin halitta na cikakken saurayi matashi Hashim ya ajiye ga gayu.
Bangaren Zaina hutu suke zasu shiga aji uku na sakandare, alamun ƴan matanci ya fara bayyana a tare da ita wanda ya saka hakan jin mugun kishinta, daga mafarinta ma a cike take ta ko'ina balle gaba.
Daga lokacin Inna ta fara hanata zama ba hijab ko yawan shigewa maza, ba don dan ba ta yarda da ita ba sai don tarbiyya.
Duk ƙoƙarin Inna ta hana Zaina yawan mu'amala da Hashim abun ya gagara, don haɗuwar jininsu daga Allah ne, idan har ta wuni ba ta ganshi ba to ba zata iya kwana ba, sai ta faki idon Inna ta shiga gidansu nemanshi, duk da in ta shiga Mama zaginta take amma da ta gane hakan da zaran ta shigo take shigewa ɗakinsu dake soro duk da shi ma ya hanata, don watarana ta shiga ta sameshi da abokansa biyu suna cin abinci, ta nemi guri kusa dashi ta zauna.
Kallonta yayi ya haɗa rai yace. "Ki je gida zan same ki."
"To ba tun safe ina jiranka kaƙi zuwa ba." Zaina tace tana ɓata fuska.
Harararta ya yi ya ce. "Yanzu dawowata zan same ki idan na gama."
Ƙin tashi ta yi, Hashim ya zare hannunsa cikin abincin ya fita ya wanke. Zaina tabi bayanshi, yana gamawa ya damƙo hannunta ya rankwashi kanta. "Kar ki ƙara shigomin ɗaki bada izini na ba."
Hawaye za ta fara ya ware mata idanuwansa yace."Kar ki yarda su zubo, mai da su maza."
Kukanta ta haɗiye yaja hannunta suka fita, suna fita ta ƙwace hannunta ta kwasa da gudu tayi gidansu, tana shiga ba ta tsaya ko'ina ba sai cikin ɗaki ta fara kuka.
Gidan ya shigo da sallama ya samu Tahiru da Inna, ya gaisheta yace.
"Inna ina Zaina."
"Yanzu ta shigo da gudu tayi ɗaki fuskar nan duk hawaye." Fadin Inna.
Kanshi ya dafe da ma yasan za'a yi haka, ya miƙe yace. "Bari inje anjima zan dawo lallashi."
"Ka rabu da ita, banda sangarci na san ma abun da ka mata bai kai ya kawo ba." Inna ta faɗa mishi.
Fita yayi ya nufi gidansu, ya samu abokansa sun fito zasu tafi ya musu rakiya a bakin hanya, suka samu abun hawa suka mishi sallama ya juya, a hanyar ya tsaya a shago ya saya mata sweet kala-kala cikin leda ya nufo gidansu da shi. Yasan yanzu ko ya shiga gidansu Zaina tana ɗaki.
Bayan magriba da ya dawo ya shiga ɗakinsa ya ɗauki ledar ya fita ya nufi gidansu Zaina, tana jin sallamar shi ta haɗa rai ta ci gaba da cin abincinta, ya shigo ya samu Baba da Inna ya gaishesu.
Ado da Tahiru suka ce mishi Bismillah ga abinci, ya girgiza kai ya zauna wajen Zaina zai saka hannu cikin nata ta ɗauke kwanonta, ƙasa-ƙasa yace. "Har yanzu fushi kike da ni."
Kai ta ɗaga mishi, ya ɗauki ledar gefenshi ya ajiye saman cinyarta yace. "Amin afuwa gimbiya ba zan sake ba."
Ledar ta buɗe taga irin sweet ɗin da take so ne, ta sake fuska tace. "Nagode na haƙura."
Ta ajiye kwanon abincin gaban shi ta ce."Mu ci ko in karo mana."
"Wannan ma ya isa." Yace ya saka hannu ya ci kaɗan ya bar mata don bai jima da cin abinci ba.
Har karfe tara yana gidan suna hira da Ado da Tahiru da Zaina da take gefen Hashim kwance, tana taya su hiran har bacci ya kwashe gurin, Inna ta tasheta kafin shi kuma ya musu sallama ya tafi gidansu.
Tun ranar idan har Hashim bai zo gurin Zaina ba to za ta je gidansu, amma bakin kofar ɗakinsu take tsayawa har sai ya ba ta izinin shiga kafin ta shiga, don kullum yana ƙoƙarin shiga dubata, idan yana da lokaci har bincikar takardunta yake kuma ba laifi yana yaba ƙoƙarinta, amma tafi ƙoƙari wajen lissafi da harkar Islamic.
...

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now