14.

172 28 4
                                    

KWANTACCIYA 14
(2nd Edition)
Pharty BB

Cikin falo Zaina ta ƙarasa shiga kanta ƙasa, ta nemi guri ta zauna ta kalla Hashim wanda idanu kawai ya zuba mata tace. "Ina wuni Ya Hash ya hanya?"
"Lafiya lau Zayn ya karatun?" Ya amsa yana tambayarta har lokacin idanuwansa yawo suke saman fuskarta.
Kai Zaina ta girgiza alamar lafiya, ta miƙe ta shiga ciki ta ajiye jakarta ta dawo ta samu har lokacin shi ɗaya zaune cikin falon, ta zauna kusa dashi ta ce.
"Kasha ruwa mana Ya Hash, ka ci abinci ma kuwa? Yaushe ka zo?"
Kusa da ita ya matsa ya ce. "Duk ta ina zan fara amsa miki Zayn, to naci amma da kin dafa da hannunki kin bani zan ƙara ci."
"Bari in girka maka." Zaina tace tana ƙoƙarin tashi.
Da sauri ya dakatarta. "Bana cin abinci sau uku a rana."
Sai lokacin ta kalleshi idonshi cikin nata tace. "Ba ka son zama kato ko, ai kuwa ga shi nan ka yi."
Rage tazarar dake tsakanin su yayi ya matsa kusa da ita sosai yace.
"Ke kuma ba kya son na zama kato ko?"
Girgiza kai tayi bugun zuciyarta na ƙaruwa don kusancin da suke, ƙamshin turaren shi duk ya cika mata hanci, ta sunkuyar da kanta ƙasa tace. "A'a hakan ma yayi."
Murmushi yayi yace. "Da yau zan fara Gym don na ragu."
Miƙewa tayi tsaye tace. "Bari in kawo maka ruwa to."
Murmushi yayi ya ɗaga mata kai ta fita da sauri ya bita da kallo. Shuru da ya ji ba ta dawo falon ba ya sa shi fita ya samu tana aiki, tana jin fitar shi ta kalle shi suka haɗa ido. Ya mats murmushi yace. "Kin mini wayo ko?"
Murmushi ta yi ta girgiza kai, ya ƙarasa wajenta yace. "Bari inje gida."
To tace mishi ya fita taci gaba da aikinta.
Har dare bai dawo ba tun tana jiran shi har ta yi shirin kwanciya Musa ya ƙirata, suka yi wayar su cikin kwanciyar hankali.
...
Ƙarfe taran dare Hashim ya amsa ƙiran iyayenshi da ya samu safiyar yau, wanda Baba Lamiɗo ne ya ƙirasl shi ya ce duk abin da yake yi ya bari ya zo Baba Fatime tana neman shi.
Kansa sunkuye ƙasa bayan gaishe su da yayi, suka gaisuwa tsakanin su har aka yi shuru ana sauraron bayanin Baba Fatime.
"To Hashimu taron nan dai dan kai aka yi da ƙanwarka Kwantacciya, ni nan ni na yarda Kwantacciya ta fara yin karatun boko to allahamdulillahi tayi karatu ta ƙare sai wanda take yi yanzu, duk sa'anninta sunyi aure wasu harda rabo, kai Abubakar ido na saka maka in ga ko za ka mata maganar aure amma ka yi shuru, to ga Hashimu in har shi ma bai shirya auren ba zan nema mata miji cikin ƴan uwanta in ba shi aurenta, ga samari nan dayawa sun gama karatu wasu har sun samu aikin yi, tunda har ta fara kula wasu samarin gwara mu aurarta da ta zo mana da wani ra'ayinta daban bayan wanda ta zo dashi na son karatun boko."
Hashim kawai gumi yake haɗawa jin kalaman Baba Fatime na ƙarshe, Zaina ta fara kula samari? Ta yaya? Yaushe hakan ya faru? Yaushe yayi saken hakan?
Jin Baba Jamilu ƙani ga Baba Abubakar ɗan auta ga Baba Fatime ya sake tambayarshi shin ya amince ya shirya auren yanzu, ya ɗaga kai da sauri ƙasa ƙasa yace. "Na amince."
Daga haka ya tashi ya fita ya bar iyaye suyi magana tsakaninsu.
Tafiya kawai yake da ya fito bai san ina zai saka kanshi ba, so yake ya samu cikakken bayani game da Zaina bayan tafiyarshi.
Wata kula? Samari nawa tayi bayan tafiyar shi? Har su nawa ne?.
Ire-iren waɗannan tambayoyin yake ma kansa ya ganshi kofar gidan Ado.

'To shi me zai mishi da baya gida bai san me za ta aikata ba.' Ya faɗawa kansa.
Har zai juya ya fasa ya ciro wayarshi ya ƙira wayarshi. Bayan ya ɗauka ya sanar dashi yana kofar gidanshi, ya fito suka yi musabaha yana tambayarsa sauƙar yaushe yace da yamma.
"Mu shiga ciki." Ado yace.
Hashim ya girgiza kai yace. "Da ma zan wuce ne nace bari in zo mu gaisa."
"Ai kuwa sai ka shiga dama akwai maganar da za mu yi da kai ina shirin ƙiranka a waya, tunda ga shi ka zo mu shiga ciki kawai." Ado ya faɗa.
Hashim bai so ba amma jin zai samu wani ƙarin bayani game da Zaina ya sashi shiga ciki, suka zauna cikin falon shi Surayya ta kawo musu ruwa ta shiga ciki ta basu guri.
Bayan shigar Surayya ciki Ado ya kalla Hashim yace.
"Hashim magana ce za mu yi mai muhimmanci, da ma akan Zaina ce, shin da ma ba soyayyar aure ka ke mata ba?"
Hashim da sauri ya ce. "Soyayyar aure nake mata me ka gani?"
"To kuwa ya kamata ka sanar da ita iyaye suyi magana, don da idona na ganta wani ya sauƙeta a motarshi, kuma duk yadda aka yi soyayya suke don da na bita cikin gida don jin wani bayani ta gudu ɗaki, na sanar da Inna ko ta mata magana ban sani ba, amma ka samu Inna za ta sanar da kai komai may be sunyi maganar. Zaina ba ta gudun abin magana cikin dangi tana son jawowa kanta wani magana bayan wanda da ma cikinta ake kullum."
Shuru Hashim yayi kafin yace. "Nagode Ado yanzu ma daga gidan Baba Fatime nake na bar su Baba suna maganarmu, inshaAllah komai zai zo ƙarshe."
"Yawwa da yafi kam." Ado ya faɗa.
Hashim bai jima ba ganin ya samu wani bayani ya sa shi masa sallama ya tafi.
Bai iya biyawa gidan Inna ba ya wuce gidansu dan ganin dare yayi sosai, zuciyarsa cike fal damuwa, amma in ya tuna cewa iyaye sun gama magana sai yaji hankalinshi ya kwanta.
...

Washegari gari Friday Zaina ta shirya za ta tafi makaranta wajen karfe tara don lecture da test da za tayi. Cikin shirinta kullum na hijab da yake dai-dai gwiwarta wanda saka shi ya zamto mata jiki har ta saba da hakan ta shirya, fuskarta ba wani kwalliya sai kyallin hoda da man baki da ta saka.
Sauri take ta tafi taji hayaniya a filin gidan su, ta ɗauki jakarta ta fito da sauri ta tsaya bakin ƙofar falo.
Adda Adama da Mama Hadizatu ta gani, Mama Hadizatu sai zuba ruwan bala'i take tana cewa.
"Akan mai za'a cuci ɗana a ba shi ragowar wasu bayan ba wanda bai san ta gama yawo a titi ba, an fake da zuwa tsinanniyar makarantar boko, to wallahi ba zai yiwu ba, ko mai kika shirya Hamsatu kije ki karya ki raba ɗana da ƴarki, wannan wani irin jaraba ne yaro tun yana ƙarami kika saka min shi a gaba yanzu ya taso a haɗa shi aure da wannan karuwar yarinyar."
Inna wacce ranta ya ɓaci da maganganun Mama Hadizatu ta dubeta ta ce. "Hadiza ki daina jifan ƴata da munanan kalaman ki, ina miki hakuri ne don kawaici ba don komai ba, duk abubuwan da kike faɗa cikin dangi akan ƴata suna dawo mini, kar kisa hakurina ya ƙare."
"Ya ƙare ɗin Hamsatu, ki dake ko ki faɗa min abin da yake zuciyarki." Mama Hadizatu tace tana ƙara jijjiga jikinta cike da masifa.
Inna za tayi magana Tahiru ya shigo gidan ya samesu haka, ya dubi Inna ya dube Mama Hadizatu yace.
"Wani abun ya faru ne na ganku a tsaye haka."
"Ubanka ne ya faru Tahiru, duk da haɗin bakin ku za'a cuci ɗana a aura mishi Kwantacciya sauran wasu." Mama Hadizatu ta ce cikin fusata.
Idonshi ya runtse ya buɗe jin kalaman bakinta da suke zubar mata da ƙima a idonshi, ya ƙarasa wajen Inna suka shiga ɗaki suka bar su tsaye Mama Hadizatu sai zuba zagi take har ta gaji ta fita in da tasha alwashin sai ta raba auren nan in har tana raye.
Inna na zaune saman kujera zuciyarta zafi take mata, da tasan hukuncin da Baba Fatime za ta yanke na haɗa auren Zaina da Hashim da bata sanar da ita cewa a zaɓa Zaina mijin aure ba, Zaina ta fara kula samari.
Mama Hadizatu ta tsaneta, ba kishiyoyin balbali suke ba amma kishinta da tsanar da take mata tamkar wasu kishiyoyi, dole ta samu Baba Fatime ta sanar da ita ta janye aure tsakanin Hashim da Zaina ko don kwanciyar hankalin ta da na Zaina.
"Inna!" Tahiru yace da ɗan ƙarfi ganin ta shiga tunani, a firgita ce ta kalleshi yace. "Wai me yake faruwa ne na kasa gane maganganun Mama."
Girgiza kai tayi ta kalla Zaina dake bakin kofa ta zuba mata ido, ta kawar nata idon ta ce. "Duk wannan yarinyar ce ta jawo min, ba ta gudun ɓacin rai na da abin magana, ga shi dalilinta an zo har gida an ci mun mutunci."
"Ita Zainar me tayi?" Tahiru yace da mamaki.
"Saurayi Ado ya ganta da shi ya sauƙeta, da ya faɗa min na sameta da maganar ta nuna min shi take son aura, na nuna mata illar hakan duk da ita ma ta sani ba barinta za ayi ta aureshi ba ta ƙi ji, shine na samu Baba Fatime da maganar, yanzu Hadiza ta  zo tana faɗa min maganganu da suka bani tabbacin haɗa auren Zaina da Hashim tayi, ban san haka zai biyo baya ba da bazan yi magana ba, ina gudun maganar Hadiza ba ta da daɗi sam a rayuwarta." Inna ta ce cikin jimami.
Durƙushewa gurin Zaina tayi ta fashe da kukan da ya jawo hankalin Inna da Tahiru suka kalleta. Cikin kuka take cewa.
"Na shiga uku don Allah Inna kar ku min haka, wannan wani irin rayuwa ce cikin ahlinmu da danginmu da mutum ba shi da ƴan cin kanshi sai abin da aka zaɓa mishi, ni dai bana son Ya Hash wallahi bazan aureshi ba, Musa nake so."
Cikin tsawa Tahiru yace. "Dalla rufewa mutane baki."
Zaina shuru tayi sai kuka da take kamar ranta zai fita, ji take kamar ta haɗiye zuciya ta huta don zafin da yake mata.
Tahiru ne ya mayar da hankalinshi kan Inna yace. "Inna soyayyar Hashim da Zaina sai Allah ba wanda ya isa ya raba su, iyayenmu maza sun aminta da auren sai ke Inna zaki ce a'a, yin haka zai ƙara jawo wani maganar a cikin dangi, ki sawa zuciyarki hakuri da duk abinda Mama Hadizatu za ta faɗa dama ba yau ta saba ba, maganar Zaina kuma ki rabu da ita kawai, in kika amince da wanda take son kina gani dangi zasu yarda, ki barta kawai in anyi auren in yaso ta kashe kanta."
Inna ta gamsu da bayanin ɗanta don haka tace. "Shikenan Tahiru Allah yasa haka shi yafi alheri."
Ameen yace ya miƙe ya fita a falon ya wuce Zaina dake kuka ko kallonta bai yi ba, tana jin dukkan maganganunsu.
Ci gaba tayi da kukanta, ganin Inna ba magana za ta mata ba ya sakata tashi ta fita.
Makaranta ta nufa bayan ta shiga adaidaita ta ƙira wayar Musa. Yana ɗauka tace. "Boyfriend Ina son ganinka yanzu kana ina."
"Lafiya Girlfriend ya naji ki hankalinki kamar a tashe." Ya ce ta cikin wayar.
"Ni kam kana ina ka shigo cikin makaranta ina jiranka." Ta ce mishi.
To yace ta kashe wayar ta jefa jaka suka ci gaba da tafiya har cikin makarantar, ta sauƙa ta ba shi kuɗin ta shiga cikin department ɗinsu ta wuce class don yin test din da yanzu za'a fara.
Ba don tasan wasu abubuwa ba, da ba za ta iya rubuta test ɗin ba ta yi submetting ta fito waje.
A bakin motarshi ta sameshi, ta ƙarasa wajensa ya bita da kallo ta buɗe gefen d'ayan ta shiga, shi ma ya shiga yana kunna motar suka bar haraban makarantar.
Sunyi nisa a tafiya sun kusa shiga unguwar su Zaina ba wanda yayi wa wani magana. Can Zaina ta numfasa ta ce. "Boyfriend ka turo gidanmu neman aurena."

Keep liking and commenting ❤️.
Pharty BB

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now