1.

594 50 7
                                    

KWANTACCIYA 1
(2nd Edition)
Pharty BB

Hidimar biki ake cikin ahalin da ya zamto su ne cikin unguwar daga farkon layi har karshenta. Ahali ne da iyaye da kakanni suka tara a gurin wanda yawansu ya zamto sun ƙwace unguwar kusan gaba ɗaya.
Tsakaninsu suke aurarwa basa bawa bare, don yawansu da kuma ƙin bare da ya zamto hakan cikin zukatansu yake tun iyaye da kakanni. Ahali ne babba manya da yara, ƴaƴa da jikoki kowa hidimar bikin yake da gobe za'a ɗaura auren ƴan uwan junan.
...
Tun da ta tabbatar da gaske auren fa za ayi ba fashi ta ji hankalinta ya tashi duk da kullum cikinta take, ya za tayi to? Dabararta ta ƙare? Ta gudu kawai tabar gidan shine mafitarta, to wani hali ahlinta zasu shiga?
Ta musu bayanin sun kasa fahimtarta? Ta roƙesu, tayi kukan tayi jinyar duk sun kasa janye ƙudirunsu a kanta?
Buga ƙofar ɗakin da aka yi take, tana kwance kamar kayan wanki shi ya sata buɗe kumburarrun idanuwanta ta kalli ƙofar, kamar ba za tayi magana ta buɗe dishashshiyar muryarta tace."Waye?"
"Ni ce nan Innarki?" Muryar mahaifiyartan ya ratsa dodon kunnenta wanda ya sakata ta tashi daga kan gadon ta nufi kofar tare da buɗewa.
Da kallo mahaifiyartan ta bita dashi yadda daga jiya zuwa yau duk ta ƙara fita hayyacinta.
Kan ba kitso duk da ba wani datti ne dashi ba amma duk ya hargitse, ƙafarta da hannunta ba lalle, idan ba faɗa maka aka yi ba ba za ka kace amarya ba ce.
"Shigo mana Innah." Zaina ta faɗa tana bawa mahaifiyarta ta hanya ta shiga ta zauna bakin katifa, kafin itama ta rufe kofar ta nemi gurin zama ta kasa cewa komai.
Kallon ta take, ba ita ɗaya Allah ya bata ba amma tana sonta sosai, ko dan ta kasance KWANTACCIYA ce kuma itace ƴa mace kaɗai da Allah ya bata sauran mazane.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana ƙiran sunanta."Zaina!"
"Na'am Inna?" Zaina ta amsa idonta a ƙasa.
"Har yanzu ba ki sawa zuciyarki hakuri da dangana ba? Umarnin iyayenki ne ba za ki iya bi ba? Ko kuma soyayya ce ta rufe miki ido? Shin kinsan waye Hashim a wajenki? Kin fi kowa saninshi, Yayankin ɗan uwanki da duk cikin dangi yafi kaunarki tun kafin ki zo duniya? Hashim ya nuna miki so tun kina ciki har girmanki, ke kanki shaidace kin san hakan amma me yasa kika ka sa hakura da ra'ayin ki?"
Kuka Zaina ta fashe dashi tace."Innah shi fa Ya Hash kallon Yayana nake masa tamkar su Yaya Ado da Tahiru, don Allah kuyi hakuri ku janye maganar aure tsakaninmu."
"Hmmm Zaina kenan kamar har yanzu kin mance waye Hashim a gurinki." Faɗin Innah.
Girgiza kai Zaina tayi hawaye na zuba a idanuwanta ta kasa magana, hakan yasa Inna tace. "Hashim shine masoyinki duk faɗin duniyar nan ki saka haka a ranki ko bayan raina za ki tuna kalamaina."
Daga haka Inna ta tashi ta fita a ɗakin, Zaina ta faɗa kan gadon ta fashe da kuka zuciyarta yana yna zafi duk da son yayanta da take amma haushinsa take ji da ya kasa fahimtar ta ya rabu da sonta ya barta da wanda take so yaƙi ya bi nashi zuciyar.
Kuka take sosai da ya zamto shine abincinta tun da aka saka ranar bikinsu dashi da ta kasa dainawa.
A hankali ta fara tariyo tarihin rayuwarsu ta baya tare dashi kamar yadda taji labari da kuma sauran da ta taso ta gani.
....

1998.

Tsoho Hashimu Modibbo tare da Kannenshi biyu Ishiyaku da Fatime, su uku iyayensu suka haifa wanda bayan sun tara iyali yara da jikoki Allah ya ɗauki ransu suka bar ƙanwarsu da ƴaƴansu da jikokinsu.
Tsoho Hashimu Modibbo yana da Yara maza biyu Isa da Lamiɗo. Waɗanda su ma duk sunyi aure da ƴaƴansu da har sun fara aurar, sai masu tasowa.
Haka ma Ƙaninsa Ishiyaku Modibbo da nashi yaran duk ya aurar dasu kafin ya rasu, sai ƴaƴansu da suma sun fara aurarwa. Kanwarsu Fatime ma haka ta haifi yara sunyi aure da ƴaƴansu.
A ahlin ba'a auran bare da hakan ya samo asali ne daga iyaye da kakanni, tsakinsu suke auren haɗin gida, kuma allahamdulillahi duk wanda aka bashi mace ko aka zaɓa miki miji ba'a samun matsala zaman lafiya suke.
A cikin gidan suke gini su ajiye matansu, wanda har ya zamana sun fara yin gini a waje har suka ƙwace layin unguwar.
Akwai ƴan mata da yawa a familyn, haka samarin matasa ma da su kaɗai su ka fara samun karatun boko da ƙyar, mata kam islamiyya suke tsayawa.
...
Sannu yake jera mata lokacin da take son zama kusa dashi, tana jinshi haka mijinta dake zaune saman tabarma yana gefenshi.
Murmushi tayi bayan ta zauna ta dubi yaron ɗan shekaru tara tace."Ya isa Hashim kamar ka ari baki."
"Tausayinki nake ji Inna, gani nake ya miki nauyi."
Dariya tayi ta shafa kanshi tace."Babu komai Hashim ka daina damun kanka."
"To yaushe za tazo na ganta?" Ya tambayeta.
"Waye kenan?" Mijinta ya tambayi Hisham da mamaki.
"KWANTACCIYA ta cikin Inna." Ya ba ta amsa yana kallonta da kyawawan idanuwansa.
Murmushi Baba ya yi yace. "Za tazo kwanan nan kar ka damu."
"To Baba." Yace ya saka hannunsa cikin kwanon abincin sa su kaci tare dashi, suna gamawa ya miƙe bayan ya wanke hannunsa yace."Bari inje gida."
"To ka gaishe da Mama da Baba, zuwa anjima zan shigo mu gaisa." Inna ta faɗa mishi.
"Inna amma ki tafi a hankali kar Kwantacciya ta ji ciwo."Daga haka ya fita.
Inna ta kalli mijintan tace."Waya faɗa masa wannan maganar?"
"Ina zan sani wayon Hashim, balle magana kam zai ji tana yawo cikin gida."
Shuru tayi cikin jimami, hakan yasa Baba yace."Yaushe za ki koma asibitin."
"Anya zan koma tunda an samu maganin da aka rasa tsawon shekaru uku." Ta faɗa yanayin fuskarta ta canza.
"Ki ƙoƙarta dai gobe ki je a duba lafiyarku, wannan maganin daban waccan daban." Baba ya ce cikin kwantar murya.
"Hakane kam."Ta ce su kaci gaba da hiran har magriba.
Yaransa maza biyu da suka fara zama samari suka shigo alwala, suka yi tare da mahaifinsun suka fita zuwa masallacin dake unguwar ya zamto nasu ne sai ɗaiɗaikune suke zuwa.
A hanyar dawowa iyaye mazan suka haɗu suka nufi gidajen su da ƴayansu, manya maza ukun in ka gansu ba zaka banbance su ba ka ce ƴaƴan maza bane da mace, haka manyan ƴaƴan su da wasu sunyi aure wasu yanzu suke tasowa ba za kace yayan mutum ukun bane da jikokin mutum uku.
A hanya kowanne ya shige gidanshi.
Baba Abubakar da ya shige gidanshi ya samu matarshi Hamsatu tana saka turaren wuta a falo don koran sauro, ya shigo falonta ɗan madaidaici ya zauna saman kujera.
"Sauron bana kamar su ɗauke mutum."
Murmushi tayi tace."Eh ciyawa yasa su yin yawa, balle yanzu damuna sun fi yawa."
"Eh, kunyi magana da Aminatu?" Ya faɗa yana canza hirar.
Abin hannunta ta ajiye na turaren wuta ta ce."A'a yanzu zan shiga mata dama."
"To idan kin gama ki je, babu daɗi goben ki je mata kai tsaye gwara ta san da maganar."
"To an gama." Tace mishi taci gaba da yin aikinta.
Har Ado da Tahiru suka shigo, ta ɗauki hijabinta ta kalli mijinta da yake kallon NTA a madaidaiciyar tvn su ƙarama tace."Baban Ado zanje wajen Aminatu."
"To a dawo lafiya. Tahiru ya raka ki."
Daga nan ta fita tare da Tahiru ɗanta na biyu tana riƙe da hannunshi.
Gidan gefenta ta wuce ta shiga na biyu tare da sallama, sau biyu tayi kafin aka amsa mata ta shiga cikin gidan ta samu Baba Hadizatu tana kwashe tuwo ta gaishe ta.
Da lafiya ta amsa taci gaba da aikinta, hakan yasa Inna Hamsatu wucewa bakin ƙofar falon Aminatu da ta shimfida musu tabarma ta ce ba zata zauna ba wahalan tashi za taji, hakan ya sa Aminatu bata kujera ta zauna.
"Ya ya akayi Adda Hamsatu ya gida?"
"Lafiya ƙalau dama akan maganar zuwa asibitin ne na sanar dake da saffafe zamu wuce, ni kam ba dan baban su Ado ba da ba zanje ba." Inna ta faɗa da jimami.
Da sauri Adda Aminatu ta ce."Ai gaskiyarsa Adda Hamsatu, duk da an samu maganin kinga ya kamata kije ko dan duba lafiyar abin ciki, idan sun ga dama ma su bamu sallama da saka ranar haifa."
"To Allah yasa Allah ya kaimu." Inna Hamsatu tace tana tashi, ta musu sallama tana shirin fita Hashim ya shigo da gudunshi yayi gurinta Baba Hadizatu ta tareshi."Kai ina za kaje, ina aiken nawa?"
"Gashi nan."Yace ya miƙa mata zai nufi gurin Inna Hamsatu ta ƙara rikoshi tana haɗa rai. "Zauna ban gama aikenka ba."
Murmushi kawai Innah tayi ta kalli gurin Hashim da ya haɗa rai kamar yayi kuka, ta musu sallama ta fita.
Ta rasa mai ta tarewa matar? Tun ranar da ta shigo gidan? Ba kishiyar balbali ba amma ta sa ta gaba? Mazan sune suka haɗa dangi shima yaran yaya da ƙanwa suke? Sai ita ɗin da suke ƴan uwan juna. Abin nata musamman yanzu da take ƙoƙarin raba ɗanta da ita da tun ranar da ya buɗe ido ya ganta ya maƙale mata.
Gidan Surukarta Baba Fatime ta shiga, ta gaisheta sai faɗa take mai ya fito da ita da ciki haka ga dare, banda kuma abin da ya faru tana son jawo wa kanta wani abun.
Murmushi kawai tayi ta mata sallama ta shiga gidanta, ta sanar da mijinta yadda suka yi, ya ciro dubu biyu ya bata yace ta ajiye wajenta zuwa safe su wuce, ta karɓa tace ta gode.
Karfe bakwai na safe Aminatu ta biyo mata suka wuce asibitin da bayan sun ga likitan ya duba lafiyarta da abin cikinta yace.
"Lafiyarki da na cikinki, abin cikinki yana motsi zamu ba ki sallama in sha Allah zuwa nan da sati biyu za ki haifa muna saka rai."
Hawaye taji ya cika idonta, ashe da ranta za ta haifi kwantaccen cikin dake jikinta tsawon shekaru uku, za taga abin cikinta da ta daɗe tana mafarkin kallo.
Mace ko namiji ne? Mai zata haifi?
Tambayoyin da take ma kanta har suka isa gida Aminatu ta wuce gidanta, ita ma Inna Hamsatu ta shiga gida a anan ta tarar da Ado da Tahiru da Hashim sun dawo daga makarantan.
Tahiru da Hashim su na primary 6, Ado yana aji ɗaya na sakandare.
Hashim da ko cire uniform bai yi ba ya nufeta da sauri yace.
"Sannu Sannu Sannu Inna kun dawo?"
"Mun dawo Hashim ya ba'a cire kayan makaranta ba?" Ta faɗa tana shafa kansa.
"Dama ke nake jira in ganki, na ga kwantacciya sai in tafi gida." Ya faɗa yana murmushi.
Ya fito shi tayi da hannu, ya zo ya zauna wajenta tace.
"Waya faɗa maka cikin jikina kwantacce ne?"
"Mama naji tana hiran da Adda Adama." Ya ce yaro babu ƙarya.
Shuru ta yi, sai kuma wani zargi ya ɗarsu a zuciyarta tayi saurin kawar da tunanin ta ce.
"Shike nan kaje gida ka canza kaya ka ci abinci, sai ka zo ku tafi karatun islamiyya kar kuyi latti."
To yace mata ya miƙe ya fita, ta samu ta kwanta tana sauƙe gajiyar hanya.
Da daren da mijinta ya shigo ta sanar dashi yadda su kayi da likita, bayan ya gama saurara yace. "To kinga amfanin zuwan ba."
Tana dariya tace."Haka ne kam."
...
Cikin satin aka shiga bikin jikokin Baba Isa Modibbo, ɗa ga ɗanshi na biyu(jikansa kenan) an haɗashi aure da ƴa ga ɗanshi na uku(jikarsa).
Auren da aka saka wata uku yau suka fara shirye shiryen shi da aure suke ɗaurawa akai yarinya gidanta.
Hakan kuwa aka yi dangi duk shiri suke basa gayyatar bare ko wani don su kansu dangine guda.
Ranar asabar aka ɗaura auren, da yamma aka fara shirin kai amarya da mota ɗaya tal suka samu zai kaita dan rashin nisan gidanta da na danginta.
Tun da yara mazan suka watse da sauran ƴan matan da a gidanta amarya tayi taronta da ƴayan ƴan uwanta mata. Ita ɗaya ta rage, ta lallaɓa ta fara gyara gidanta tana yi tana hutawa don bayanta da ya riƙe, har ta kusa gamawa ta taji mararta ya fara murdawa ga cikin jikinta da sai juyi yake.
Daga bakin rijiyar da take ta tashi ta shiga falonta ta fara zagayawa don ciwon damunta yake sosai sai haɗa gumi take, haihuwace ta sani hakan yake mata in zata haifi yaranta.
Hashim tun da yaga ɗakin amarya ya fito da gudu haka kawai ya tuna an bar Inna Hamsatu ita ɗaya a gida, ya nufi gidan don bata labarin gidan amarya kuma ya tayata zama kafin matan su dawo.
Da gudu ya bankada kofar gidan ya shigo ya nufi falonta ya sameta durƙushe, ya ƙarasa da gudu gurinta yana tambayar ta lafiya.
"Ka ƙira min Babarka Aminatu."
Shine kawai abin da yaji ta faɗa ya fita da gudu ya barta.
Cikin mintuna goma ya shiga gidansu ya lalimota cikin matan da ake biki, ya faɗa mata ta zari mayafinta suka yi gidan.
A kofa tace ya tsaya, ta shiga falon ta sameta can cikin ɗaki ta shirya kayan haihuwa ta shimfida leda da zannuwa, ta ƙarasa wajenta da sauri bayan ta cire mayafinta ta fara taimaka mata.
Da fara nakudar da haihuwar cikin awa huɗu, da taimakon Baba Aminatu da sunan Allah da take ambata ta haifo kyakkyawar yarinyarta fara mai ƙiba.
Gyarta Baba Aminatu tayi ta nannaɗe cikin zani ta kwantarta gefe, kafin ta taimako Inna Hamsatu ta gyara jikinta ta zauna sannan ta fita don ɗaura ruwan zafi.
"An haifi kwantacciya?"Hashim dake rakaɓe kofa ya tambayi Adda Aminatu.
Murmushi tayi ta ɗaga mishi kai, zai shiga ta hana shi tace."Ka bari a mata wanka a saka mata kaya sai ka ganta."
Bai so hakan ba ya zauna, ta wuce ta hura wuta ta ɗaura katuwar tukunya da ruwa. Tana shiga tana fita yana gani har ruwan ya tafasa ta kai wani bangida wani ɗaki kafin Innah Hamsatu ta fito a ɗakin ta ganshi zaune yana ganinta ya miƙe ya kalli cikin jikinta da ya ragu yace.
"Zan iya shiga."
Kai ta ɗaga mishi tana murmushi ta wuce bangida. Da bismillah ya saka ƙafarsa falon ɗakin, ya ji kukan yarinya da a hankali take fitar da shi, wani irin bugun zuciya da tsoro ne ya ziyarci shi lokaci ɗaya ya ja baya zai koma Baba ya shigo falon su kayi karo yace."Mai ya faru Hashim kamar kuka nake ji na jariri?"
"Innah ta haihu."Yace yana shirin fita.
Baba ya rikeshi yace."Ka tsaya ka gani mana kai da kullum ka ke jiran ganin ƙanwarka ko Ƙaninka."
Hannunshi Baba ya kama suka zauna. Inna ta shigo Baba ya ce.
"Sannu Hamsatu allahamdulillahi Allah ya nuna mana ranar haihuwar sai mu gode mishi."
"Sosai bari a kawota ku ganta." Tace ta wuce ciki ta samu Adda Aminatu ta gyarata ta naɗeta cikin towel mai kyau sai ƙamshin powder take, ta sanar da ita ta kaiwa Baban su Ado ya ganta kafin mutane su shigo.
To tace ta miƙe ta fita da ita.
Baba ta fara miƙawa ita ya karɓeta yana kallo, yayi murmushi yace.
"Allah na gode maka da ka nunamin ranar haihuwar kwantacciya. Allah kai ne abin godiya msi rayawa."
Dukkansu suka amsa har da Innah da fito ta zauna ta fara shan kunun kanwa da Baba Aminatu ta dama mata.
Jaririyar aka ɗaura Hashim saman cinyarshi, ya riƙeta sosai don karta faɗi tare da zuba mata ido, can ya kalli Inna yace."Ina sonta Innah."
...
KWANTACCIYA.
Labarin kwantacciya da ta ɗauki tsawon shekara uku cikin gidan kwan haihuwarta.
Bayan girmanta ta zo musu da canje-canje cikin ahlin da karya dokar da suka kafa tsawon shekaru tun zamanin iyaye da kakanni.
Ku biyoni kawai kuji labarin kwantacciya.
...

#vote
#comment

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now