17

67 6 0
                                    

KWANTACCIYA 17
(2nd Edition)
Pharty BB

Washegari ranar asabar ƙarfe goma ƴan uwa da dangi iyaye maza suka shaida ɗaurin auren HASHIM ISA da ZAINA ABUBAKAR, cikin sadaki mafi sauƙi dubu hamsin.

Nutsuwace ta sauƙarwa Hashim jin an shafa Fatihan aurenshi da Zaina, rana da lokacin da yayi ta jira a rayuwarshi.
...

Zaina tun da taji an ɗaura aurenta ƙara duƙunƙunewa waje ɗaya tana kuka, shikenan ta rasa Musa, rashi na har abada, soyayyarshi ba zai taɓa gushewa a cikin zuciyarta, shi ya kawo kanshi cikin rayuwarta ya koya mata sonshi, ga shi yanzu an musu fin ƙarfi an raba su.

Cikin gida biki ake sosai, manya da yara kowa farin ciki yake da wannan auren musamman wanda suka san girman Zaina da yayanta Hashim mai sonta.
Haka gidansu Hashim kowa ka gani murna yake, banda Mama Hadizatu da ƙin yin taro tayi Adda Adama na gefenta tana tayata baƙin cikin wannan auren.

Har yamma ana hidima inda ƙarfe bakwai na dare bayan sallar magriba aka fara shirin kai amarya. Zaina da zazzaɓi ya rufeta ko kaya bata canza ba tun na safe jikinta.

Lokacin da za'a kaita Surayya ce ta kai mata ruwan wanka, ta shiga ta tayarta ta taimaka mata ta kaita bangida, tayi wanka ta gyara jikinta ta fito ta shiga dakin, lace ta saka riga da skirt da ya zauna a jikinta, duk da ramar da tayi amma ya mata kyau, lulluɓeta tayi da lufaya sai ƙamshin turaren wuta yake ta zaunarta bakin gado, kafin ta fita ta ƙira Inna ta shigo.

Guri ta samu ta zauna tana kallon Zaina da kanta ƙasa, tana hawayen da take ganin zubar su tafin hannunta.
Jikinta ne yayi sanyi ganin hawayen ƴartan, tunawa kaɗai da take Mama Hadizatu bata son Zaina yana tayar mata da hankali, amma ba yanda ta iya dole ta taimaka mata tabi ra'ayin iyayenta ko don samun rahmar Allah.

Shuru tayi kafin a hankali ta ƙira sunanta ta ƙara da cewa. "Zaina! Allah ya nuna min aurenki da na Hashim, Allah ne ya haɗa Ƙaddarar aurenku ba iyayenki ba, da Allah bai rubuta ba aure tsakaninku ba da ba yadda za ayi ayi ko yayane, ki bi mijinki ki mishi ladabi da biyayya, ki cire kowa cikin ranki In sha Allahu za ki ji daɗin zama da Hashim. A gabana ya taso na san tarbiyyar shi da irin son da yake miki, sai Mama Hadizatu kin santa kin san halinta, duk maganganun da yake yawo a kanki cikin dangi rabi da kwata ita take yaɗawa, ki ci gaba da toshe kunnuwanki kamar yadda kike yi, ki mata biyayya ki bita sau da ƙafa saboda uwar mijinki ne dan duk yadda Hashim yake sonki ba zai bari ki raina mishi uwa ba, fatan za ki yi aiki da abinda na faɗa miki, Allah ya ba ku zaman lafiya."

Jikin Zaina ne yayi sanyi jin maganganun Inna, hawayenta ta share ta ɗagawa Inna kai alamun taji komai, kafin Inna ta miƙe ta cewa Surayya. "Ki fito da ita falo Baba zai shigo."

Da to ta amsa, bayan fitar Inna ta tashi ta miƙar da Zaina suka fita falon ta zaunarta a ƙasa. Baba ya shigo ya zauna ya kai dubanshi kan ƴarshin. "Na san abinda zan faɗa duk Innarki ta faɗa, addu'ata gareku Allah ba ku zaman lafiya, ki ma mijinki biyayya Zaina, ki cire wancan yaron cikin zuciyarki da ma Allah ya yi ba mijinki ba ne. Ƙaddarar Allah ne ya haɗaku don nuna mishi hanyar shiriya, kuma hakan da ki kayi yayi dai-dai kin yi jahadi Allah ba ki lada."

Nasiha sosai Baba ya yiwa Zaina waccd take fitar da ruwan hawaye, jikinta yayi mugun sanyi ta riga ta sakawa ranta haƙuri da dangana ta karɓi Ƙaddarar rabuwa da Musa hannu bibbiyu.

Bayan Baba ya gama mata nasiha ya fita, mata suka fara fita don zuwa kai amarya. Surayya ce ta ɗagata suka fita sai kuka take wanda yanzu kukan rabuwa da gidan take, don bata ma san ina ne gidanta ba.

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now