7

211 26 3
                                    

KWANTACCIYA 7
(2nd Edition)
Pharty BB

Da safe Hashim ya wuce Kaduna bai samu damar sanar da Zaina ba, da ma kuma sun yi sallama tun daren jiya.

Ƙarfe goma Zaina tana karin kumullo Tahiru ya shigo gida, kasancewar ƴan biki sun watse ya samu Zaina saman taburma a baranda, ya zauna kusa da ita.

"Ina kwana Yaya Tahiru." Ta ce ta ci gaba da cin abincinta.
"Lafiya lau ya hidimar biki?" Ya amsa mata da tambaya.

"Lafiya lau." Ta amsa mishi da shi.
Ya miƙe don tuna aiken Hashim na safe, ɗakinsa ya shiga ya fito ɗauke da ƙaramar leda da kwali a ciki ya isa gurinta, ya miƙa mata ya ce. "Ga shi Hashim ya bada a ba ki, ya wuce Kaduna."
Kallon ledan tayi ta amsa ta ajiye a gefe, ganin haka yace. "Ki buɗe mana ki gani."

Hannunta ta cire ta wanke ta ɗauki ledar ta buɗe, ta ga kwalin waya tecno touch screen mai kyau. Ihu ta fasa da ya saka Tahiru yin baya tana kallonshi ta ce. "Allah sarki Ya Hash ɗina, nagode mishi sosai wallahi."

"Ki ƙira shi ki mishi godiya idan kin ma wayar caji, ga wannan ki sa kati." Tahiru ya ce yana miƙa mata ɗari biyar, ta amsa tayi godiya ta wuce ɗaki don nunawa Inna, abincin da ba ta ƙarasa ci ba kenan.

Da ta nunawa Inna ita ma ta ce ta mishi godiya tace to. Haka ta saka wayar caji ta fita don sayo kati.
Ka sa barin wayar tayi ya yi caji bayan ta dawo, ta cire ta saka katin ta fita ta samu Tahiru baya nan ya wuce aiki da ya samu, haushi taji ta koma cikin ɗaki ta saka wayar a caji ta fita ɗan ɗaura abincin rana.

Kusan karfe ɗaya ta gama ta kwashe a cooler ta cirewa Baba nashi da Tahiru, sai nata da Inna kafin tayi wanka ta shiga ɗaki.

Tana cikin shafa mai taji ƙara, ta kai dubanta gurin wayarta ta ga shi ne, barin abin da take yi tai ta isa gurin ta cire a cajin ta ɗauka, ta ga sunan Ya Hash a rubuce ya bayyana, da sauri ta ɗauka ta kafa a kunne tace.
"Ya Hash!"

"Yes My Zayn." Yace daga bangaren shi ya lumshe lumshashshun idanuwansa ya buɗe yana kwance saman kujera.
Ɓata rai tayi kamar tana ganin shi tace. "Ba na son sunan nan."

"Ni ma ki daina ce min Hash, kuma ba ki san naki ma'anar sunanki ba shi yasa kike son hanani." Ya faɗa mata ƙasa ƙasa cike da shauƙi.

"Ni dai bana so." Tace tana turo baki, sannan ta tayi saurin cewa. "Ya Hash na gode sosai naga sabuwar waya, Allah ya saka ya ƙara budi."
Murmushi ya yi ya ce. "Ameen Zayn, amma ki riƙe godiyarki idan na dawo zan nema."

Dariya sanyayya ta sanya mishi kawai, daga nan hira suka yi sosai da shi, har aka ƙira sallah suka kashe wayar, ta mayar caji ta saka kaya ta zauna jiran Inna don ba sallah take ba.
...

Sati biyu da faruwar haka aka fara bada admission, Tahiru ya sanar da ita ta shirya ya kaita ta karɓa ta ƙira Hashim ta sanar da shi ya ce. "Registration fa zuwa yaushe?"

"Gobe mana Ya Hash, duk na gaji ka san wahalar gurin karɓa kuwa." Ta faɗa a gajiye.

"Sorry Zayn, da ina nan ni zan karɓa miki kin san bana so ki wahala?" Ya ce mata cikin kwantar hankali.
Cike da ƙaunar yayan nata ta ce. "Ai na sani."

"To Allah bada sa'a." Ya faɗa mata.

Ta amsa da amin ta kashe wayar suka ci gaba da tafiya. Tana koma gida ta nunawa Inna, kallo ɗaya ta mishi tace Allah sanya albarka.
Da dare ta nunawa Baba, shi ma ya mata addu'ar samun nasara.
...

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now