22

98 10 2
                                    

KWANTACCIYA 22
(2nd Edition)
Pharty BB

Karfe huɗu da rabi Hashim ya dawo gidan, kamar jiya Zaina ta tashi ta buɗe mishi kofa, ya rumgumeta cikin jikinshi wanda har ta saba da hakan, suka nufi ɗakinshi ya shiga wanka ta cire mishi kayan sawa ta fita a ɗakin, ta zauna a falo zaman jiran shi.

Da Hashim ya gama wanka ya shirya ya fito falo ya samu Zaina saman table, ya zauna shima ta miƙe ta zuba musu abinci suka hau ci, suka gama suka koma falon yana kallo tana danna wayarta har aka ƙira magriba ya wuce masallaci, itama ta miƙe ta shiga ɗakinta tayi sallah.

Bai dawo ba sai isha'a kamar jiya ɗauke da takeaway, duk yadda yayi Zaina taci wani abun kasawa tayi tasha fresh milk kaɗan ta shige ɗakinta, tayi sallar isha'a ta kwanta.
Sai da ya gama tsaf ya sameta kwance shi ma ya kwanta.

Da asuba ya tafi masallaci bai tashi Zaina ba, sai da ta tabbatar ya fita ta miƙe tayi alwala tana cikin yin tahiya ya shigo ɗakin, kamar ta nutse ƙasa taji, haka ta ɗaure ta idar da sallar taci gaba da zama saman darduman ta kasa hawa gadon ganin ya kwanta.

Duk Hashim yana lura da ita, murmushi kawai yayi ya rufe idanuwanshi kusan mintuna goma ya buɗe ya kalleta ta jingina da gini, ya miƙe ya nufi gurinta, da sauri ta tashi tsaye ta hau linke darduman. Ya yi murmushi yace. "In kin gama ki kwanta."

Kai ta ɗaga mishi ya koma ya kwanta, tana gamawa tayi hanyar waje ya tashi ya tarota. "Ina kuma za ki je?"

"Zan ɗaura maka breakfast ne."
Zaina tace muryarta kamar za tayi kuka, ya hanata ya jata zuwa gadon yana kwantarta tare da cewa. "Gari bai gama wayewa ba ai."

Shuru ta mishi, ganin haka ya sashi zare hijab ɗin jikinta ya gyara mata kwanciya cike da farin ciki, a ranshi yana cewa soon dai wannan tsoron zai rabata da shi.

Karfe tara Hashim ya wuce aiki bai tashi Zaina ta haɗa mishi breakfast ba, don bacci da ya ɗauketa, da ta farka bata ganshi ba ta lalubi wayarta ta ƙira shi.

"Hi Zayn." Ya ce yana ɗauka.

"Shine ka wuce baka tashe ni na maka breakfast ba." Ta ce mishi.

"Sorry My Zayn na ga kina bacci ne, ki shirya ina dawowa zamu koma gida." Ya faɗa mata a hankali.

"Da gaske?" Ta ce cikin murna.

"Yes ki zama cikin shiri."

To tace mishi ta kashe wayar, ta miƙe ta gyara ɗakin da gidan gaba ɗaya, tayi breakfast kafin ta hau shirya kayanta ta gama, ta shiga nashi ɗakin ta shirya mishi nashi dayawa ta fito ta ɗaura abinci.

Karfe ɗaya ya dawo daga office, tayi mamaki. Ganin hakan yace. "Masallaci zan wuce in na dawo sai mu tafi."

"To a dawo lafiya kafin nan na gama abinci." Ta faɗa mishi.

Ciki ɗakinshi ya shiga yayi wanka ya shirya cikin silver ash color na shadda da hula, ya fito Zaina ta bishi da kallo yayi mutuƙar kyau.

Ganin irin kallon da take mishi ya ƙarasa kusa da ita, yana kallonta ya ce. "Na miki kyau ne?"

Rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana ɗaga mishi kai, ya yi murmushi yace. "Kin fini kyau ai."

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now