9.

195 24 5
                                    

KWANTACCIYA 9
(2nd Edition)
Pharty BB

Ku yi following nawa fisabilillah 🙏
https://arewabooks.com/u/phartybb

Zaina juyi take saman shimfiɗarta daren ranar ta kasa runtsawa, maganganun Moses suke mata yawo a kai da ta kasa daina tunanin su, don neman gane kansu take son yi.
Fahimtarsu take son yi ta kasa, neman ƙarin bayani take a ciki ta rasa wa zai mata?
'Shi kaɗai ne.' Amsar da zuciyarta ya bata.
To ta ya ya? Mutumin da ba ta son ganinshi don takura mata da yake? Kuma me haɗinshi da ita da zata damu kanta cikin lamuransa har haka?
'Son sanin shi waye da me yasa ya ƙi musulunci take son yi?' Zuciyarta ta faɗa mata haka.
...
Washegari ranar Lahadi ba ta da lecture, bayan ta farka ta ɗaura abincin safe don hutar da Inna, da ta gama ta saka kowa nashi ta tattare gidan ta share ta haɗa wanke wanke tayi, sannan tayi karin kumullonta ta yi wanka ta koma bacci.
Sha biyu da rabi ƙarar wayarta ya farkar da ita, ta lalibo ƙarƙashin pillow ba ta tsaya duba waye ba ta kafa a kunne tace. "Ya Hash!"
"Is not him." Taji muryar Moses da ya sakata tashi zaune ta kasa magana.
Fahimtar haka ya sa Moses cewa. "Da ma na fito daga church ne na ƙiraki mu gaisa, sai gobe mun haɗu a school."
Kafin tayi magana ta ji ya kashe wayarsa, ta cire a kunnenta ta bi fuskar wayar da kallo. Tana shirin ajiyewa ya ɗauki ƙara ta ɗaga ta ga Hashim, ta ɗauka cikin sanyin jiki da ta rasa na menene.
"My Zayn!" Ta ji muryar Hashim.
Ta amsa tana cewa. "Ya Hash. Ya aiki? Sorry weekend?"
Murmushi ya yi yace. "Bacci kike ko na tashe ki, kin kasa banbance yau yaushe."
Saman idanunta ta sosa da hannunta, ta buɗe ido ta rufe gaba ɗaya Moses ya sakata tunani, da ƙyar tace. "Bacci nake Ya Hash."
Hashim ya sake cewa. "Kina sauƙe gajiyar school, to ya karatun fatan lafiya?"
"Lafiya ƙalau, ya kuma gurin aiki da ba'a hutawa, wai da ma haka aikin Bank yake." Ta faɗa mishi tana ɓata murya.
"Muna nan muna yi. 8am-5pm ne." Ya ce yana murmushi.
"Tab! shikenan matarka ba za ta ƙara ganinka ba idan ka fita tun safe sai yamma." Ta ce cike jin haushi.
"To ya za'a yi, in kece ya za ki yi?" Ya tambayeta jin ta taɓa mishi inda yake mishi kaikayi
Shuru Zaina tayi can tace. "Binka zan dinga yi ko ina zuwa dubaka."
Dariya Hashim yayi da taji sautinshi yace. "Shike nan zamu gani."
Ba ta fahimci zancensa ba yasa ba ta ƙara wani kalma ba.
Basu wani jina ba ya kashe yace ta koma baccinta, kafin ta kashe wayarta ta kwanta wanda a zahiri idonta rufe amma tunani take.
Tana kwance haka har aka ƙira sallar azahar, ta miƙe ta fita ta samu Inna tana gyaran yakuwa, ta kalleta tace. "Inna an yi abincin rana ko na ɗaura."
Kallonta Inna tayi tace. "Kina nan kina baccinki na gama abuna, ga wannan zan gyara sai ki mana da dare da biski, ki yi mai kyau don zan kaiwa Baba Fatime ba ta jin daɗi."
"To Inna Allah bata lafiya." Zaina tace ta miƙe tayi alwala ta koma ɗaki ta gabatar da sallah.
Yamma yanayi ta ɗaura miyarta na yakuwa, ta gama tayi tuwon biski ta kwashe a coolers, ta zuba na Baba Fatime ma daban, kafin ta kimtsa wajen murhun tai wanke wanke sannan tayi wanka ta ɗaura alwala.
Bayan sunyi sallah ta taimaka Inna ta ɗauki coolers din suka nufi gidan Baba Fatime.
Da sallama suka shiga tana zauna saman taburma da samanshi darduma. Gefenta jikokin ƴan uwanta ne maza da mata sun zo gaisheta da wanda suke tare da ita, guri Inna ta samu ta zauna, haka Zaina ma da kallo ɗaya ta musu ta maida hankalinta ga Baba Fatime, ta gaisheta tana mata ya jiki.
"Kwantacciya ina labarin yayanki Hashimu?" Zaina ta ji daga gefenta, ta juya ta kalla mai maganar ta ga Yaya Bukar ne ɗa ga ƙanin Baba Lamiɗo wato Baba Isa.
"Yana lafiya ɗazu ma munyi waya dashi." Ta ba shi amsa tana tashi, matan gurin suka bita da kallo kafin shi ma ya miƙe ya bi bayanta.
"Ya wajen aikinsa." Ta ji an tambayeta daga bayanta, ta juya ta kalleshi tace. "Lafiya lau."
Shuru ya biyo baya tsakaninsu, da ma ba wani sabo suka yi ba sai yanzu da gulma ta kawoshi.
Tahowar mutane ta gani ya sakata komawa ciki wajen Inna, ta samu tana shirin fita ta yima Baba Fatime Allah ƙara lafiya suka fito tare.
A ƙofar gidan suka haɗu da Adda Adama da Mama Hadizatu, Inna tace musu. "Ina wuninku?"
"Lafiya." Suka amsa da shi.
Mama Hadizatu ta kalla Zaina tace. "Ke ga ki ishashshiya Kwantacciya ba ki iya gaishe na gaba dake ba, ko da yake an watsar a makaranta."
"Zato dai ba kyau." Inna tace da ranta ya ɓaci da maganganun Mama Hadizatu.
Harara Mama Hadizatu tayi cikin duhun kamar Inna za ta ganta tace. "To zage ni Hamsatu akan ƴarki, karya nayi ne? Kuma kice ma ƴarki tayi nisa da yarona idan ba haka ba ko ta ƙarfi da yaji sai na rabasu in dai ni Hadiza ina numfashi."
Girgiza kai kawai Inna tayi taja hannun Zaina suka bar gurin, har suka isa gida ba wanda yama wani magana, bayan sun zauna Zaina ta ɗauko musu abinci da ruwa ta ajiye, kafin ta zauna kusa da Inna ta zuba musu abincin suka fara ci.
Suna ci ba wanda ya yi magana, shurun da yayi yawa yasa Zaina cewa. "Inna wai me kika ma Mama Hadizatu?"
Inna kallon Zaina ta yi ta girgiza kanta tace. "Ni ma ban sani ba Zaina tun tasowata haka nake da ita, duk abinda nake da shi tana jin haushi idan ita bata da shi, haka har aurenmu ga shi har zuwa yanzu abin ya koma kanki, ba zan rabaki da Hashim ba amma ina son kiyi baya da shi ko don mahaifiyarshi kar ta cutar dake bayan cutar da aka taɓa yi miki."

KWANTACCIYAWhere stories live. Discover now