20

87 11 1
                                    

KWANTACCIYA 20
(2nd Edition)
Pharty BB

(Page 19 ya goge and babu inda zan samu, but za ku gane.)
...

Da asuba da Hashim ya farka ya tafi masallaci bayan ya dawo ya hau haɗa kayan shi da duk abinda zai buƙata, bayan ya gama ya shiga ɗakin Zaina ya samu tana bacci har lokacin.

Akwatin kayanta ɗaya ya haɗa mata, duk yawanci ƙananan kaya ne sai hijab biyu na sallah da turaruka da lotion ɗinta, ya rufe ya ja akwatin ya haɗa da nashi ya fita wajen motarshi ya saka a boot, ya rufe ya koma ɗakinshi.

Wanka yayi ya fito ya saka kaya, ya fito ya nufi ɗakinta tana bacci har lokacin, ya kalli agogo ya ga karfe shida da arba'in, bakin gadon ya ƙarasa ya saka hannu ya ɗauketa cak, ta buɗe idanunta cike da bacci za ta yi magana ya ce. "Yi baccin ki."

Rufe idonta tayi ta kwantar kanta kan kirjinshi, ya fito da ita ya buɗe gidan baya ya kwantarta ya rufe, kafin ya koma ya kulle gidan ya shiga mota ya kunna ya fita.

Bai ko samu damar yin sallama da kowa ba ya kama hanyar Kaduna, tuƙi kawai yake ganin lokaci yaja yana son leƙa office kafin azahar idan sun isa.

Sai da rana tayi haske sosai Zaina ta farka ta ganta a hanya, a tsorace ta tashi zaune tana bin hanyar da kallo. Hashim da ya ji ta yace. "Kin farka?"

"Ina za muje?" Ta tambayeshi da sauri.

"Gidanmu na Kaduna." Ya faɗa mata.

Shuru ta mishi ta koma ta kwanta, ya ci gaba da tafiya. Sai ƙarfe tara suka shiga cikin garin Kaduna, Zaina ta tashi zaune tana bin garin da kallo har ya iso estate da yake zaune, ya shiga da mota zuwa inda flat nashi.

Bayan ya parker motarshi ya buɗe ya fito yana cewa Zaina. "Fito My Zayn."

Fitowa tayi ta tsaya, ya buɗe boot ya ciro akwatunan su, ta taimaka mishi taja nata yaja nashi yayi gaba ya buɗe kofar falon ya shiga, itama ta shiga tabi falon da kallo, irin mai ƙasan nan ne, da kallo tabi komai ash color da baki, falon da girmanshi ya fi wancan na garinsu, har da gurin dinning da table a gurin mai kyau, daga gurin ƙofar kitchen ne.

Gefe kuma ɗakuna biyu ne a jere, daga gefe idan ka hau step uku gurin kujeru ne marasa hayaniya a gurin, da babban window mai cike da glasses, gurin kamar gurin shan iska, sai ɗaki ɗaya a gefe.

Ɗayan ɗakin Hashim ya nunawa Zaina yace. "Ga ɗakin ki."

Ta ja akwatinta ta ɗaga ta hau da shi ta shiga ɗakin da ya nuna mata, da kallo ta bi shi don yayi mugun haɗuwa cikin shi, komai fari ne tun daga kan gado har paint, godo ne lafiyayye an shimfiɗa mishi bedsheets da bedside drawer nashi a gefe, ga wardrobe da mirror ga extra drawer babba, labulen ciki ma white. Tana cewa falon ya mata kyau da ta ga ɗakin sai taji ta kasa tantancewa wanne yafi kyau.

Akwatinta taja ta ajiye, ta buɗe wardrobe ɗin ba komai ciki ta buɗe akwatin ta ɗiba kayanta na ciki ta jera, nan ta ga kayan cikin duk babu na kirki ta ji haushi, da ƙyar ta samu riga dogo mai gajeren hannu iya gwiwa, ta nemi wando dogo ta ajiye tare da hijab ɗaya da ta gani cikin biyun.
Undies ɗinta da sauran kayan buƙata ba wanda bai saka ba hatta always da yasan za ta buƙata, kunya ne ya kamata shikenan yanzu ba wani kunya tsakanin su da shi, cikin zuciyarta cewa take. "Da ma ya tasheta ta haɗa kayanta."

KWANTACCIYAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن