YAN UBANCI

270 5 0
                                    

Ƴ'AN UBANCI

  BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. 

  Godiya da ya yabo sun tabbata ga Allah  madaukaki, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahma (S. A. W).
      page 1

      Malam Buba mai almajirai malami ne da yake koyar da almajirai a k'auyen kukayasku dake Maigatari L.G a Jihar Jigawa, Malami ne da ya yi suna ya shahara sosai a cikin ƙauyen na Kukayasku da ma wasu k'auyukan da ke mak'otaka da kukayasku, kai har ma da rugage da ke kusa da nesa kai har ma daga kauyukan Niger irinsu garin isa,Dogo dogo, Shakunu da dai sauransu. Duk da cewa su ma k'auyukan na da mayan malamai amma shahara da kuma tsayuwa tsayin daka na malam Buba ya sa su ke kai masa yara almajirci. Malam Buba yana da matan aure guda biyu uwar gidansa itace Ishalle sai kuma amarya mai suna Alawiyya, y'arsa d'aya a duniya mai suna Nana y'ar gidan Ishalle ce dan ita amaryar Allah  bai ba ta haihuwa ba. Suna zaune lafiya da iyalansa kuma yana kula da su kamar yadda ya kamata. A kwana a tashi sai matarsa amaryar ta nemi ya sawwak'e mata sabo da tana so ta je wani wurin ta yi aure ko Allah  zai bata rabon haihuwar, haka Malam Buba ya saki Alawiyya ba dan ransa ya so ba sai dan kar ya shiga hak'k'inta domin idan bai amince ba kamar ya tauyeta ne tun da tana ganin kamar rashin haihuwar daga gareshi ne , dan tun da ya haifi y'a d'aya , shiru ka ke ji. Yanzu yarinyar zata kai shekara takwas. Duk da ya nu na mata duk a in da ta ke  sai Allah ya nufe  ta da  samun  haihuwar  tukunna  zata haihu amma haka ta matsa ya sawwak'e mata ta je ta yi wani auren. Bayan shekara d'aya Malam ya sake auro  wata matar mai suna  Kande, bazaware ce aurenta uku amma bata tab'a haihuwa  ba.Kande wata masifaffiyar mata ce wacce tsabar fad'anta ya sa mazan ke sakinta, Malam Buba bai yi wani bincike ba akan ta sabo  da ta nuna masa ita mace ce mai ladabi da sanin ya kamata, wanda a zahiri kuma ba haka bane kawai buge ne.

    Bayan Kanden ta tare da farko zama kamar abin arzik'i, sai daga baya ta fito da halinta na asali daman an ce mai hali baya canjawa.Rashin mutunci  kala-kala Kande ta tsiro da shi wanda hakan ya matuk'ar sanya Ishalle a damuwa domin kullum ba su da zama lafiya kai hatta da Malam da almajiransa basu tsira ba daga rashin mutuncin Kande. Haka zaman ya cigaba  da kasancewa babu dad'i  babu dad'ad'awa, sam Malam Buba ya gaji da fitinun Kande gashi ba yadda son ya sake ta gudun kada mutane su d'aukeshi mutum mai auri saki. A kwana a tashi haka rayuwa ta kasance gaba d'aya gidan ta zamewa Ishalle kamar wani kurkuku gashi ko Nana bata son zama a gidan sai dai ta je mak'otansi, har abin ya kai Ishalle ta daina zama a tsakar gida sai dai a d'aki in ba wani Abu za ta yi ta bata ko k'aunar fitowa tsakar gidan da sunan ta zauna tasha iska. Malam ma sabo da masifar Kande sai da zaman gidan ya zame masa kamar kufai.

  Bayan shekara d'aya matan na Malam dukansu Allah ya azurta su da samun ciki, Malam ya yi murna sosai dama samun wannan k'aruwa duk da hali irin masu Kande amma hakan bai sa ya ji ba dad'i a ransa ba damuwa samun cikin Kanden sai  addu, a da yake Allah sauke su lafiya. Kande kam ta yi matuk'ar bak'inciki ciki da Ishalle ta samu ciki domin so take ta samu ita kad'ai dan ta yi ta haihuwa sabo da gadon dan Malam Buba akwai gonaki da shanaye d'a sauran Dabobi wannan dalilin ne ya sa mazan Kande ta amince da aurensa ba wai dan kasancewarsa Malam ba ita wannan ba damuwarta bace. Tun da cikin na su ya tsufa Kande ta dinga bin malamai da bokaye tana so ta salwantar da abin da ke cikin Ishalle, dama tun yana k'arami take ta son a zubawa  Ishalle  amma hakan ya gagara.cikin yawon Malaman nata ne ta had'u  d'a wani boka wanda ya yi mata wani asiri ta biyashi mak'udan kudad'e dan ya gaya mata mai zai faru, haka ta dawo gida da farinciki.A haka har ita Kanden ta haifi d'iyarta mace duk da ta so haihuwa namijin domin gadonsa ya fi yawa, ranar suna aka sanyawa yarinya Ikilima. Bayan sati uku da haihuwarta itama Ishalle ta fara nak'uda, tun tana yi d'auke k'arfinta har dai ta galabaita, ita kuma kande tana d'akinta tana dariyar k'eta.Malam Buba kuma yana d'akinsa  ya hau buzu yana ta addu, a Allah sauketa lafiya. Gozomar  da zata karb'i haihuwar ce take ta mata sannu a haka har dai haihuwar ta zo gadan -gadan, amma me dai -dai fitowar kan  d'a  me gozoma zata  gani  wani k'atoton kan  miciji  ne ya kawo kai, Dan sauri Gozomar ta ja da baya tana salati ita kuma Ishalle  wahala ta isheta bata ma san meke faruwa ba. Kafin me miciji  yana fitowa zilululu tsayinsa ya kasa  k'arewa  ai  da gudu  Gozomar ta fito daga d'akin ta nufi turakar Malam Buba hankali a mugun tashe, haka ta kira Malam Buba ya fito da sauri ya nufi d'akin Ishalle  hankali a tashe dan  ya d'auka ma Ishallen ta mutu ne dan gozomar  d'akin kawai ta ke  nunawa ta kasa masa bayani tsabagen rud'ewar  da ta yi. Malam Buba na shiga d'akin idanunsa ya sauka akan wani  dank'areran bak'in  maciji a gaban  Ishalle  da take  a mugun tsorace ta takure a wuri d'aya sai ruwan hawaye ke zuba kamar  famfo.


  mmn afrah 09030283375

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now