YAN UBANCI

34 1 0
                                    

🅿️2️⃣8️⃣⏩2️⃣9️⃣

  Yaya Nana fitowa ta yi daga cikin asibitin tana ta soshe -soshen kai, wata bola ta hau daga tsallaken asibitin ta je ta ke tsince -tsince haka dai ta yi ta tafiya daga bola zuwa bola kai Allah ka rabamu da mak'iya hauka ba dad'i.

    A can cikin asibiti tsakanin y'ar aikin Hindatun da ABIDA babu wanda ya bi ta kan dawowar Yaya Hindatu dama bokan ya ce idan Hindatu ta taka maganin babu wanda zai k'ara tambayarta kowa zai manta da ita ba wanda zai k'ara ko da tunata. Y'ar aikin mai suna hanne ita ke tambayar ABIDA

"ABIDA wanne ne d'an Hajiya  a ciki"

"Haba Hanne in dai ba tsufan bane ya kama ki baki ga ni namijin bane a hannu na hakan na nufin shine na  mama macen kuma ita ce ta aunty Hindatu.

"To amma dai bari sai mun tambayi malamar mai karb'ar haihuwar mu tabbatar "Hanne ta ce tana kallon ABIDA .

"Tunda baki yarda ba shikkenan " cewar ABIDA tana mata wani kallon raini. Ana haka sai ga nurse d'in ta fito rataye da jaka dan lokacin tashin aiki ya yi.

"Malama ina da tambaya,"Hanne ta tambayeta tana nufar inda take itama ABIDA tashi ta yi ta bi bayanta.

"Ina jin ki"cewar nurse d'in ta tsaya tana sauraren abin da Hanne za ta ce.

"Dama matan nan da muka kawo su biyu, da suka haihu aka ajiye su a d'akin hutu shine mu ke so a fad'a mana jinsin da kowacce ta haifa.

"OK bak'ar ce ta haifi namiji, farar kuma ta  haifi mace" tana gama fad'in haka ta juya abinta ta tafi ba tare da ta ce komai ba, sannan ba tare da ta saurari wani abu daga garesu ba.

"To yanzu tunda kin ji da kunnenki ai sai ki yarda "ABIDA ta fad'a tana juyawa ta koma in da suke zaune.

"ki yi hak'uri ABIDA ba wai yarda bane ban yi ba kawai dai inaso a tabbatar tunda su duka baas cikin hayyacinsu lokacin da suka haihu" Cewar Hanne lokacin da ta k'araso wurin ABIDA.

"Ke ki ka sani "Ta ce tana tab'e baki.

  Bayan kamar minti talatin, aka kira su ABIDA domin su zo wurin y'an uwansu, haka su ka shigo d'auke da yaran, ABIDA na shigowa ta nufi gadon da Ikilima ke kwance tana murmushi,Hindatu na ganin Hanne ta nufo gadon da ta ke d'auke da jariri ya sa ta fahimci cewa na hannun Hanne shine abin da ta haifa, wasu hawayen murna da jin dad'i ne suka fara gangarowa zuwa kumatunta, dan ta kasa tantance irin farincikin da take ciki. Hannunta har karkarwa yake  da Hanne ta mik'a masa jaririyarta hannayenta ta zaga sama tana mai godewa Allah akan kyautar da ya mata, tana karb'ar y'ar ta mata addu, a sannan ta rungume ta  tana jin wata iriyar k'auna da soyayyar da kowacce uwa ke yiwa y'arta. Itama Hanne sai murmushin take zabgawa ganin uwar d'akinta na cikin farinciki dan tana jin dadin zama da Hindatu domin Mutuniyar kirki ce ta d'auketa kamar uwa sabo da tana girmamata  iya zaman da su ka yi bata tab'a b'ata mata ba kai ba ita kad'ai bama hatta sauran ma,aikatan babu wanda zai koka da Hindatun.

"Baba Hanne kin ga kyautar da Ubangiji  ya min" ta ce tana dariyar murna.

"Na gani Hajiya hak'ik'a Allah shine abin godiya  ,shine mai  ji kuma mai gani ,shi ke bayarwa a lokacin da ya so kuma shine  ke hanawa a lokacin da ya so dan haka godiya ta tabbata Allah madaukaki " Cewar Hanne.

"Wannan haka ya ke Baba Hanne Alhamdulillah "Hindatu ta ce cikin farinciki.

  Tunawa da ta yi da y'ar uwarta Ikilima ya sa ta yi saurin juyawa  inda gadonta ya ke domin lokacin da suka farka ma ta ganta kafin su ABIDA su shigo har ta ke mata sannu amma Ikilimar ta yi banza da ita ta k'aura kai gefe. Yanzu ma tana juyawa ta ga Ikilima da ABIDA sun zubo musu ido suna zance k'asa -k'asa.

"Aunty Ikilima bari Baba Hanne ta miko miki ita ki ganta, ABIDA Milo min shi nima in ganshi " Ta ce fuskarta na nuna ainihin tsantsar farincikin da take ciki.

"A, a kar ma a miko min ita ba sai na ganta ba, kuma shima ba sai kin ganshi ba, yo da Allah na tuba dan kin haifi mace ma har wani abin murna ne, ai da namiji ne sai ki yi wannan d'aga kan tunda mun san namiji shi ke da rabo me talla idan tsoronsa mutuwa ta riskeshi"

Wani daci da rad'ad'i ne suka ziyarci zuciyar Hindatu jin kalaman da suka fito daga bakin Ikilima.

Wai dan Allah Aunty Ikilima me na miki ne a rayuwa da bakya son ko kad'an ki ganni ina farinciki?" Hindatu ta fad'a wasu hawaye masu zafi na zubo mata, tabbas tana jin ciwon abinda iko ke mata amma na yau ya dara na kullum kuma hakan ba ya rasa  nasaba da ciwon haihuwar da ta ji sannan kuma Ikilima ta nuna bama ta k'aunar ganin abin da ta haifa d'in kuma itama ba za ta bata nata d'an ba tare gani. Lallai k'iyayyar ba k'arama ba ce.

"Dalla can malama kar ki dameni, kuma wa ya ce miki sai ka yiwa mutum abu ya ke tsanarka, ko kad'an ba haka bane duk wanda ba ya k'aunarta to kwa baya kaunarka har gaba da abada! dan haka ki rik'e yarki na rike d'ana " Ta ce tana mike kafarta  akan gadon.

  Juyawa Hindatun  ta yi tana kallon Hanne, jin maganar da y'ar uwarta ta fad'a har zuwa lokacin hawaye basu bar kwaranya ba idanunta ba.

"Ki yi hak'uri Hindatu komai mai wucewa ne wataran sai labari, ke labarin mai  ba,a ji ba" Cewar Hanne tana dafa kafadar Hindatu don lallashinta domin ta ga sauran mutane da ke d'akin sun fara ankara duk da kowa sabgar gabanshi ya ke.

"To munafuka da ki daurewa munafurci tsantsa ai dai y'aruwata ce kuma ba, a canjawa tuwo suna " Ikilima ta ce dan zuwa yanzu ta gama k'uluwa domin ta fahimci cewar Yaya Nana ta tafi ma,ana magani ya fara aiki sabo da ta san sun manta da ita kamar yadda boka ya ce, amma daman mantuwar banda ita, dan haka ji take kamar ta je ta shak'e Hindatun har sai ta mutu MI's, dan yanzu ne yan ubanci ya fara tunda ta haihu.

  Daga Hanne har Hindatu  babu wanda  ya k'ara tanka mata, ana haka ta ce Hanne ta miko mata  waya dan so take ta kira Dr ta sanar dashi dan direbobin da suka kawosu ma ta ce su koma gida kuma kar su sanar da kowa halin da ake ciki. Ana miko mata waya ta ga  16 miss call na Dr sai 4Miss call na Ummi Ishalle ,Umminta ta fara kira ta sanarwa sosai ta yi murna da godiya ga  Allah, kafin daga bisani ta kira  Dr.

"Haba ina ki ka shiga tun dazu na sa a duboki cikin taron nan ba, a ganki ba, kuma na kira waya baki  d'auka ba?"

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now