🅿️3️⃣8️⃣⏩3️⃣9️⃣Direban yana sauketa ya shigar mata da jakarta cikin gidan ya fito ya yi tafiyarsa, tana shigowa gidan ga Shema, u na bakin famfo tana ta shek'a amai kallon hadarin kaji ta mata ta shige d'akin Mama Ikilima .Jim kad'an suka fito daga d'akin ko sallama ba su yiwa Shema, u ba suka fice daga gidan, waya ta yiwa Okasha ya fad'a mata inda za su had'u, d'an sahu suka tare suka shiga suna dab da zuwa wurin suka sauka suka sallameshi yayi tafiyarsa, da kafa suka k'arasa wurin da Okasha ke jiransu suna zuwa suka gama tsara abin da za ayi, sun kwatanta masa gidan da kuma asibitin da Dr ayuba ke aiki daga K'arshe ABIDA ta tura masa hotunnansu ,dan sun ce ko kisa ne ya kama ayi matsawar dai za, a zo musu da takardun kadarorin, sun gama tsara komai Okasha ya ce su bar komai a hannunsa haka suka rabu da Okasha ran su fari kal shi kuma ya dawo gida ya yiwa y'ar uwar mahaifinsa sallama ya kama hanyar kano domin su fara aiwatar da aikinsu.
Tun da Okasha ya sauka a garin Kanon dabo ya je suka tsara yadda za su aiwatar da aikin, tun a ranar juma, ar suka fara bibiyar duk wani motsin Dr ayuba ta haka ne suka gane cewar takardun basa tare da shi amma kuma tabbas suna bin diddigin motsinsa ba tare da ya sani ba.
Ranar asabar da misalin karfe sha biyu na rana, Dr Ayuba ne a bayan mota sai direbansa da yake jan motar, hanyar asibinsa da ya ke aiki suka nufa, motar su Okasha na biye da su a boye ba tare da sun fahimta ba har dai direban ya yi parking Dr ya fito, mutane da damane suke ta gaishe da shi yana amsa musu cikin sakin fuska, Office dinsa ya nufa ya bude sannan ya maida k'ofar ya sanya key ya k'ulle, wata loka dake cikin office din ya janye sannan ya d'aga capet wasu takardu ya fiddo na kadarorinsa, da ya boye in bashi ya fad'a maka ba babu yadda za ayi ka fahimci cewa akwai wasu takardu a wajen. Daman ya rarraba takardun ne saboda samun akasi shi yasa ya bar wasu a gida wasu a office, yana dauka ya maida lokar mazauninta ya ajiye, toilet ya shiga ya wanke hannunsa da kura ta taba garin dakko takardun, daukan takardun ya yi ya sanya a wani file ya bude k'ofar ya fito ya k'ulle, Okasha da ke lab'e a windon office d'in daga bayan can ya yi murmushin mugunta, jujjuyawa ya yi ya ga babu wanda ya ganshi dan haka ya fito ya shiga motarsa ya bari sai da su kamar Dr suka fita sannan ya tada motar ya bi bayansu, danja ta tsayar da su Okasha yana saitin motar Dr yana satar kallonsa lokacin da yake saka wasu takardun da ya fito da su daga gida shine yake had'asu a file d'aya .Waya Okasha ya yiwa abokansa ya sanar da su kan cewa su je layin hanyar gidan Dr wanda Dr ke bi su tsaya in da ba mutane motar na zuwa su aiwatar da aikinsu, yana gama fad'a musu ya yi hanyar gidan da suke ajiye mutane in buk'atar hakan ta taso. Dr suna zuwa layin suka ga mota ta sha gabansu kafin me wannan sai ganin mutane sukayi fuskokinsu a rufe, salati Dr da direban suka fara yi kafin mutane su nuna mu su bindiga, shiru sukayi aikwa aka sa direban ya baiwa d'aya daga cikin mutanen tuk'in shi kuma ya shiga d'aya motar suka ja suka tafi,ana fara tafiya suka shak'a musu powder nan take suka fara barci, wata hanya suka d'auka suna gudu kamar masu barin k'asar sai da suka yi tafiya mai d'an nisa can bayan gari kafin suka tsaya a k'ofar wani gida, shiga akayi da Dr da direba aka sanyasu a wani d'aki.
Bayan kamar awa d'aya Dr ya kawo hankali nan suka tisa keyarsa akan ya sanya hannu akan takardun da sunan da suke so, ya musu gardama suka hau dukansa da ya ga suna neman halakashi sai ya ce zai yi abin da suke so nan Okasha ya ce ya sanya hannu da sunan SAFWAN kamar yadda su Ikilima suka buk'ata dan suna so idan SAFWAN ya taso wannan tarin dukiyar ya zama mallakinsa, yanda zasu mora dan basa so a sanya sunansu dan kar a gano su amma SAFWAN ba lallai ne a gane ba kuma sun san dole ba za a saida kadarorin ba sai da takardun to kafin lokacin da SAFWAN zai girma maganar b'atan takardun ta lafa ka ji tunani irin na Ikilima da y'ar ta ABIDA. Bi ya yi ko ina ya sanya sunan SAFWAN ya sa hannu sai wurin da Hindatu za ta sa hannu ne kawai ya rage, anan suka buk'aci ya sa hannu ya nuna musu wurin suka ga ansa sunan Hindatu dan haka suka karb'i takardun suka sakesu dan shima direban ya farfado sai dai shi basu masa komai ba. Mukullin motar Dr suka baiwa direban daga nan suka sallamesu haka suka fito jikinsu sanyi k'alaw ,motar suka shiga direba ya mata key suka bar gidan suka kamo hanya ,sun hau kan kwalta kenan direban na baiwa Dr hak'uri shi dai Dr bai cewa komai dan ba kowa ya ke tunani ba sai Hindatu ya san tunda suka san akwai wurin da za ta sa hannu to tabbas kamar yadda suka kamoshi to tabbas za su nemo ta itama dan haka ma baya son ya kirata a waya so ya ke sai ya je gida ,dan dole ma a sanya tsaro mai tsanani a gidan sannan duk inda suke sai an nemo su, yana cikin ayyana maganar a ransa sai ji ya yi motar tana tangal tangal
"Yallabai motar nan birkinta ba yi kwata-kwata "direban ya ce a kidime dan sai auna arzik'i suke.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji, un kar dai sun kunce birkin ne? "shima Dr ya ce hankali tashe."Walllahi inaga sun since dan bayaji"
"Ya salam ni daman na yi mamakin da suka barmu sikau dan sun san dole za, a sanarwa tsaro ashe su mana abun da suka yi...ai kafin me wannan motar ta tintsira kawai gangarawa suke har dai ta hantsila ta fad'a cikin ruwa.Hindatu kwa ganin Dr bai dawo ba har sha biyu ta wuce gashi ta yi ta kiran wayarsa bata shiga hatta wayar direban ma in ta kira a kashe ake cewa. Ganin haka sai hankalinta ya tashi dan cewa ya yi ta bashi yan mintoci yanzu zaije ya dawo, daga K'arshe dai ta yanke shawarar bin bayansu zuwa asibitin dan hankalinta ya kwanta, bata yi tunanin kiran IMRAN ba dan ta san yanzu yana gida bataso ta d'aga masa hankali, fitowa ta yi ta tura FADILA wurin wasa Inda kayan wasanta suke birjik ita da masu kula da ita, direba ta sa ya d'akko mota suka fito dan direbobi ne birjik a gidan suna fitowa, su Okasha da ke lab'e suna lura da duk wani shige da fice na gidan dan ko hatsarin da su Dr suka yi akan idansu dan kwa suna biye da su. Haka suka ringa bin motar har suka kai layin da suka kama su Dr anan suka musu yadda suka yiwa su Dr haka suka kai su gidan da suka kai su Dr,har dai suka farfado daga K'arshe bayan sun sa Hindatu ta sanya hannu a. jikin takardun, tana ta kuka da rokonsu su fad'a mata inda mijinta yake amma suka k'i, haka suka baiwa direban Mukullin motar ya tafi dan Okasha ya hana a barta su tafi da direban. Domin sun shirya shi da abokan aikin nasa za, a yiwa Hindatu allurar poison in yaso sai su jefer da gawar a wajejen gidan a tsinceta wannan plan d'in Okasha ne ya shirya musu shi, haka aka mata alluran haka suka d'auki gawar suka kai ta bakin titi suka yarda suka k'arawa. rigarsu iska. Yan sandan da suka je d'akko wanda aka ce sunyi hatsari da motar ambulance su ne suka tsinci gawar Hindatu,, sun samu motar Dr da gawar direban amma ba a samu gawar Dr ba, sannan an samu gawar direban da ya d'akko Hindatu wanda ya je ya bugu da bishiyar maina dan itama motar sai da suka since mata burki suka bashi.
Yan sandan sunyi bincike akan gawarwakin amma basu gano komai ba, dan su Okasha sun san aikinsu ba su bar wata alama da za a gano su ba dan tuni ma sun bar garin Kanon dabo amma in kere na yawo zabo na yawo watarana za, a had'u. Itama gawar Hindatu haka aka gama bincike bincike akanta aka je aka binneta acan in da kowa sai ya je Allah sa mu cika da imani ameen. Yanzu dai tsaro sun ce za su tsaurara bincike akan gano wanda suka aikata haka, dan sun gano cewa wasu ne suka aikata haka Ummi Ishalle sai kuka take amma har gwara Hindatu an ga gawarta an sallaceta akan Dr da ko gawarsa ba, a gani ba, ya nitse a cikin ruwan.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala