🅿️7️⃣⏩8️⃣Kande bata da wani abin da ta sanya a gaba sai Hindatu ,ta kafawa yarinyar karan tsana na babu gaira babu dalili sai ta shiga d'aki ta zauna ta ringa turo Ikilima tana dukan Hindatu idan ta daketa ta ji ta d'auki kuka sai ta koma d'aki da gudu wurin uwarta hallaw daga an d'an jima Kanden za ta sake turo ta dan ta sake dukan Hindatu amma tsabar hak'uri da kauda kai irin na Ishalle bata ko d'aga kai ta kalli Ikilima bare har ta sanya Hindatu ta rama ko kuma ita ta ramawa Hindatu. A haka kullum suke tun abin baya damun Ishalle har dai abin ya zo yana damunta yau da gobe sai Allah kuma tsakanin uwa da d'a sai Allah sannan kuma ita zuciya bata da k'ashi.Wani lokacin haka za ta hana Hindatu fitowa ko k'ofar d'akinta sabo da Ikilima kar ta daketa amma sai Kande ta aikata har cikin d'akin Ishalle ta doki Hindatu kuma bafa a hankali take dukanta ba da k'arfi dan idan Kanden za ta aikata sai ta nannaga mata kan cewa tayi dage k'arfinta idan zata daketa. Kai wata rana har cizon Hindatu Ikilima ke yi dan duk jikin Hindatu tabon cizo ne dan idan ka tsaya ka k'arewa yarinyar kallo idan tana dukan Hindatu za kaga tsantsar tsana a fuskarta domin gaba d'aya Kande ta koyawa yarinyar Y'AN UBANCI yarinyar ta gama gane cewar Hindatu ba y'ar d'akinsu ba ce, ba uwarsu d'aya ba kawai gaba d'aya Kande ta yi amfani da jahilci da Kuma son zuciya wajen koyawa y'arta mummunar d'abi, a. Wanda a b'angaren Ishalle ba haka abin yake ba kullum bata da buri da ya wuce nunawa Hindatu ta so y'ar uwarta Ikilima sabo da dukansu abu d'aya ne basu da wani banbanci, dan ko d'inki Ishalle za ta yiwa Hindatu to tare take musu da Ikilima kai ko da wani abu ne na ci za ta baiwa Hindatu to tare za ta raba musu da Ikilima ,wanda ba haka bane a b'angaren Kande dan ko Hindatu tana tsaye tana kallon abu suna ci ita da Ikilima to Kande na zata tab'a baiwa Hindatu ba ko da kuwa Hindatun za take kuka amma Kande ba za ta tab'a Hindatu abun ba.
Wata ranar asabar ne da yammaci Ishalle tana hura wuta domin ita ce da girki,bayan ta hura wutar ta koma can kan tabarmar da take zaune tana goga d'anyar kub'ewa ,Hindatu name gefenta a zaune tana wasan k'asa Kande kwa tana d'akinta ita da Ikilima kawai sai ganin Ikilima Ishalle ta yi ta fito hannunta a b'oye a bayanta murmushi Ishallen ta yi ta ce
"Ikilima zo ki yi wasa ke da y'ar uwarki mana"
"Ni ba zan yi wasa da ita ba kuma ni ba y'ar uwata bace kuma Ummata ta ce kar in so ta in tsaneta" Ikilima ta ce tana kumbura baki irin na maras kunya.
"To ai shikenan tun da baya zaki yi wasan ba"
"Ni kwa Ummina ta ce in ke son ki kuma ke y'ar uwata ce komai na samu in ke sammiki "Hindatu ta fad'a tana yiwa Ikilima murmushi.
"Ke ni bana sonki "Ikilima ta ce tana harar Hindatun.
Ummi Ishalle ce ta d'ago kai ta kalli Ikilima domin ji ta yi maganar ta tab'ata ta duk da cewa a lokacin Ikilima tana da shekara tara amma hakan bai hana Ummi Ishalle ta ji zafin maganar ba, sannan kuma da ta dubi fuskar Ikilima sai ta ga tarbiyar b'ata rai alamar da gaske take.Kau da kai ta yi gefe ta tashi ta sanya silifas d'inta za ta je ta iza wuta.
"Kema fa ba uwata bace sabo da ba ke ki ka haifeni ba" Ikilima ta fad'a tana murgud'a baki.
Tsayawa Ummi Ishalle ta yi da fifita wutar ta tsaya tana kallon Ikilima yadda take magana kamar wata uwar mata duk wani manyance yarinya k'arama ta iya sabo da koya mata da uwarta ke yi.juyawa ta yi ta k'ara itace ta duba tukunyarta juyowar da za ta yi kawai sai jin k'aran duka ta yi zaro idanu Ummi Ishalle ta yi ganin wata murd'igegiyar bulala a hannun Ikilima da ta zabgawa Hindatu a kan ta,kafin Ummi Ishalle ta k'araso Ikilima ta kuma zabga mata a gadon baya nan take Hindatun ta fad'i k'asa tana kuka da murza wurin dukan."Ke Ikilima wannan wane irin duka ne me ma ta miki da zaki daketa da wannan bulalar? "Ummi Ishalle ta ce tana k'arasowa wurin.
"An duka d'in kuma ai ba sai ta mini wani abu ba tun da ni ce gaba da ita ,kuma ita ba y'ar d'akinmu ba ce"
Ummi Ishalle bata kuma bi ta kan Ikilima ma ba sai ta nufi kan Hindatu ta d'aga ta, sosai yarinyar ke kuka har shid'ewa take jijjigata Ummi Ishalle ta shiga yi tana lallashinta kama rigar Hindatun ta yi ta d'aga abinka da farar fata har wurin ya yi jajawur ga bird'in nan ya fito wata k'wallar tausayin y'ar tata ne ya taru a idanunta haka kawai bata ji ba bata gani na an duketa dukan da ko ita da ta haifeta bata tab'a mata ba.
"Kin min dai -dai ikily haka nake sonki ai duk wanda yace ya ci tuwo da mu to wallahi miya ya shahara, ba dai kin had'a Y'AN UBANCI da y'ata ba to kwa wallahi kin had'a kan ki da jaraba dan ki sa a ranki cewa baki ga komai ba dan yanzu aka fara kuma ba, a gama barbad'a wai an ba gozoma tuwo a hannu ta ce ba, a gama haihuwar ba ai"Umma Kande da ta fito daga d'aki ta fad'a tana kama hannun Ikilima ta rik'e.
Baki sake Ummi ta tsaya tana kallonta mamaki gaba d'aya ya gama lullub'eta duk da ta san halin Kande amma yau abin ya d'aure mata kai kasa cinye abin da ya zo ranta ta yi ta ce.
"Haba ke kwa Ummar Ikilima bai kamata ace kina yin haka ba ai ,kalli bayan yarinyar nan ki ga bird'in da Ikilima ta mata kuma ki ce ta kyauta? " Ummi Ishalle ta k'arasa fad'a tana nuna mata Bayan na Hindatu.
mtssss ta ja wani wawan tsaki sannan ta ce " hmmm lallai Ishalle ki ke ki iya shege to bari ki ji in fad'a miki gaba tsakanin Ikilima da Hindatu yanzu aka soma ko kuma ma in ce ba, a soma ba dan wallahi babu afuwa babu ragawa a tsakanin mu da ku, yadda ki ke kishiyata to Hindatu tafi kishiya a wurin Ikilima, kuma in dai dukane baki ga komai ba dan gaba tafi baya yawa dan abin da za ta mata nan gaba sai yafi wannan dan ki sani ma yanzu ma ni na turo ta ke hatta bulalar ma ni na bata" ta fad'a tana turo d'ankwalinta gaban goshi.
Ummi Ishalle da ta sanya hannu a hab'arta tana bin Umma Kande da kallo ta sauke sansanyar ajiyar zuciya ta ce
"Allah kyauta to Allah kuma ya baki hak'uri""Wuhuhu da hak'urin ta mutu sadakar nawa kike ka samu"
"Ni dai na san Hindatu ba komai take yiwa Ikilima ba,amma dai duk da haka zata k'ara kiyayewa da shiga harkarta "Ummi Ishalle ta ce tana kama Hindatu ta d'agata tsaye.
"Hehehehe ai dole a kira akuyar sirika iya"Umma Kanden tace tana juyawa rik'e da hannun Hindatu suka shige d'aki.
Tun daga wannan ranar Ummi Ishalle ta sanya Hindatu take kiyaye duk wani abu da zai kawo sab'ani tsakaninsu da Ikilima duk da dama ita Ikilimar ce mai laifi da kuma saurin hannu. Ummi Ishalle ta baiwa Malam Buba shawara akan ta ya taimaka ya sanya Ikilima da Hindatu a makarantar boko sabo da su samu ilimin zamani duk da ita Hindatu tana zuwa makarantar allo da Malam amma Ikilima sam bata zuwa makarantar allon Malam ya yi fad'an ya gaji kullum uwarta ke hanata zuwa ta gwammace take d'ora mata tallan gyada da alkaki.Malam Buba ya amince zai sanya su a makarantar boko domin shima baya so su taso a haka ba.
"To munafuka algunguma wato shawara ki ke bashi akan a sanya su a boko ,to wallahi ba dai y'ata ba dan ban ga wanda ya isa ya sanya min y'a a bokoko a wuta ba sai dai ke a kai taki y'ar ban da renin wayo ke kin san ma hanyar makarkatar bokon dan ba makaranta ba ce makarkata ce dan haka babu in da za, a kai ta wallahi "cewar Kande da ke tsaye bakin k'ofar d'akin Malam dama tana tsakar gidan amma kunnenta a kan maganar da su ke yi.
"Haba Ummar Ikilima yanzu abin arzik'i ma sai ya zama na tsiya ,dan na ce a sanya su makarantar boko shi ne ya zama lefi kuma da ki ke maganar ni ban je boko ba ai zamani mu da na su akwai ban banci amma in maganar ta b'ata miki rai ki yi hak'uri "cewar Ummi Ishalle.
"Ke ki ka sani in ma menene dai ba in da Ikilima za ta je, makarantar allo ma bata je ba bare wata boko"
"Ya isa haka Kande wai ke me yasa kullum bakya so a zauna lafiya, yanzu menene lefinta dan ta ce a sanya su makaranta kamar wacce ta ce a sanya su a gidan rawa, tukunna ma ke fa ba da ke ake maganar ba"Malam Buba ya ce cikin b'acin rai.
"An fad'a d'in idan ma ba da ni ake maganar ba ai da y'ata ake sanyawa a maganar ,kuma da ka ke maganar bana son zaman lafiya ai zama lafiya k'auyanci ne, sannan ni wallahi da a sanya Ikilima a makarantar boko gwara a sanyata a gidan rawar ko banza y'ata ta yi suna ana nunata a talabijin "ta k'are maganar tana tafa hannu.
"To shikenan Allah shiryeki ya shiga lamuranki in dai kuma kina ganin hana Ikilima zuwa makarantar cinyewa shikenan dama ni ba isa na yi da ke ba sai abin da ki ka ga dama kike yin, amma ki sani wata rana za ki yi da ma sani"yana gama fad'ar haka ya tashi ya yiwa Ummi Ishalle sallama yaran fita wurin almajiransa.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala