YAN UBANCI

35 1 0
                                    

🅿️2️⃣6️⃣⏩2️⃣7️⃣

  ABIDA jin k'aran  Bud's k'ofar d'akin da yaya Nana ke ciki ya sa ta yi saurin juyawa ta kama hanyar zuwa falo kamar dama ba a tsaye ta ke ba, dan kar ta ganta a tsaye ta yi tunanin wani abu da ban,dan za ta yi tunanin me ya sa ta tsaya bata shiga falon ba, gashi Kuma gaba d'aya alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ABIDA sabo da ba ta yi tunanin fitowar yaya Nana ba a lokacin. Da ya ke d'akin da yaya Nana ta ke kusa ya ke da na Hindatun tana fitowa sai kawai ta nufi d'akin Hindatu dan ta fito su tafi, tana zuwa ta bi ta kan maganin da Ikilima ta barbad'a ta shige falon, a inda suka kusan yin karo da Hindatu da ke k'ok'arin fitowa dan dama lokacin da Ikilima ta lek'ota zobe ta manta akan mirror  shine ta koma sai kuma da ta ji kiran da ABIDA ta mata shine ta taho, murmushi su   ka yiwa juna ita da yaya Nana kafin su juyo suka fito tare. A lokacin da ABIDA ta koma babban falon gidan wanda acan ne Ikilima ta ke zaune, ganin ABIDA ya sa ta tashi ta nufo ta wanda sanadin hakan ne ta hango abin da ya mugun razana ta, da yake hanya ce street kana hango har can k'ofar d'akin Hindatu da yake ita ABIDA ta baiwa hanyar d'akin Hindatu baya sai bata ga abin da mahaifiyarta ta gani ba.nufo ABIDA da Ikilima ta yi sai idanunta suka sauka akan yaya Nana da ta shiga d'akin Hindatu, ganin haka ya sa ta k'wala wani uban k'ara wanda ya isa kunnuwan su Hindatu suka nufo gurin hankali tashe.

  "Subhanallah menene "Hindatu ta tambaya tana kama Ikilima ganin ta dafe saitin mararta, da ya wani murd'a mata take ta fara jin d'an cikinta ya hautsina da k'arfin ,sanadin ganin yaya Nana ta taka maganin da ya zama makaminta na b'atar da Hindatu shine ya tayar mata da nak'uda.

"Ikilima ko haihuwar ce ta zo "itama yaya Nana ta tambaya a rud'e ganin Ikilimar ta tsugunna sai cije leb'e ta ke, duk da bata tab'a haihuwa ba ita yaya Nana  ta san tabbas akwai ciwo a nak'uda.

  Haka suka kamata suka shiga da ita wani d'aki, da kulawa nan falon, dan ta kasa magana kwata -kwata, itama kuma ABIDA duk ta tsorata dan itama ba ta san me Ikilima ta gani ba amma dai tunda ga Hindatu ta taka magani burinsu zai cika sai ta ji komai da sauk'i.

"Amma yaya Nana ko direba zai, a kira a tafi asibiti kin ga halin da take ciki kawai a hak'ura da  zuwa wurin taron, mu kaita asibitin gwabnati kar mu je d'aya daga cikin asibitocin Dr dan za,a iya fad'a masa gani a asibiti kuma kin ga yana da baki kar mu katse masa. Idan ma ya kirani zan ce na fasa zuwa wurin taron gwara idan ta haihu kowa ya ji haihuwar" Hindatu tace kamar ta yi kuka ganin yadda Ikilima ke ta had'a zufa sai murkususu ta ke.

"Eh hakan ya fi kira direban kawai mu je asibitin"Yaya Nana ta ce cikin hanzari.
  Kiran direban  ta yi cewar ya fito da mota ga su nan zuwa, tana kashe wayar Ikilima ta k'wala wani wawan ihun da ya sa Hindatu ta tsorata ai ita ma take mararta ta murd'a say kuma bayanta ya rik'e salati ta d'auka suka k'arasa da Yaya Nana itama nak'udar ce gadan -gadan. Haka Yaya Nana ta kira y'an aiki mata guda biyu suka taimaka mata aka kama su Hindatun aka kai su mota, Yaya Nana ta tafi da d'aya daga cikin masu aikin mata ce za ta kai sa,ar Ummi Ishalle dan kar su tafi su kad'ai tun da ABIDA yarinya ce kuma itama Yaya Nanar ba sanin kankara gadon abin ta yi ba.Haka suka yi mota biyu suka nufi asibiti bayan Yaya Nana ta d'akko wasu kaya daga cikin kayan haihuwar Hindatun da zannuwa da duk wasu abu da za, a buk'ata har da fallaye biyu na atamfa masu iri d'aya kuma a rabe suke. Bayan zuwansu asibitin gaba d'ayan su aka shiga da su d'akin haihuwa, sai Nurse d'in suka hana kowa shiga bayan sun haihu sai aka ce mutum d'aya ta zo sai Yaya Nana ta tafi, sun shigo dakin a inda Yaya Nana ta bada fallen atamfa guda biyu iri d'aya, aka dauki jariri aka bata ta taho da murna ta baiwa ABIDA ta koma ta karb'o jaririyar ta baiwa tsohuwa da sukayi zo da ita, ta musu bayanin da nurse d'in ta mata akan sun sha wahala sosai dan haka an musu allurar barci dan su samu hutu. Ruwa ta ce za ta biyo tana jin kishi, a hanyarta  ta dawowa daga siyan ruwan ne ta ji kanta ya mugun sara mata, ya kuma sara mata a karo na biyu, ledar ruwan ta jefar kafin a karo na uku ta ji kamar an buga mata guduma, nan take ta ji ana juyata kafin me wannan sai ta nemi tunani da hankalinta ta rasa dan kuwa d'ankwalinta da mayafi ta cire ta yi jifa da su sai kawai ta fara tik'ar rawa, ta sille takalmanta ta ruga bakin get d'in asibitin  a guje. Mutane sai kaucewa suke suna cewa
  Ga mahaukaciya nan"

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now