🅿️3️⃣2️⃣⏩3️⃣3️⃣Haka aka sallamesu daga asibitin dan dama lafiya k'alaw sulast haihu. Ran kowa fari kal amma ban da ran Ikilima da ta ke jinshi cike kuma cunkushe da tarin bak'inciki, sabo da cikinta da bai ci akan wacce ta sa aka mata aikin dominta ba, gashi yanzu mafarkinsu ba zama gaskiya ba domin ita ko kad'an bata damu da maganin da Yaya Nana ta taka ba, hankalinta ya karkata ne ga cikar burinsu wato Hindatu domin ita ce yanzu gaba d'aya y'an ubancin ya karkata akanta sabo da ita ce ta had'a komai na rayuwa wanda su ba su samu ba. Duk da k'ok'arinta na ganin ba su yi rashin komai ba a rayuwa amma hakan bai sa sun raga mata ba. Dan ko zancen da sukayi wato Ikilima da ABIDA akan b'atan Yaya Nana, da ABIDA ke bata shawara akan asa bokan ya karya maganin ta dawo tunda ba ita akayi niyyar yiwa ba Ikilima cewa ta yi
"Ke dalla k'yaleta ta karata can an rage mugun iri"
"Kuma hakane fa mama" ABIDA ta ce, suka fashe da dariya.
Bayan sun dawo gidan Hindatu daga asibitin, komai da komai na baby aka siyowa Ikilima Hindatu ta sanya IMRAN ya iyo shopping babu abinda babu wani abun ma Ikilima bata san amfaninsa ba, amma haka Hindatun ta yi list aka soya komai. Hatta da kayan shayi an ajiye mata manyan gwangwanaye isassu ga nama Kala-kala kafin a d'auke wata kulan naman an kawo wani. Dan Hindatu ta hanasu tafiya wai sai ta warware. Ko su Malam Buba da Ummi Ishalle da kuma Umma Kande nan suka zo ganin baby anan har Malam ke yiwa Iko fad'a akan ta zo ta zauna a gidan k'anwarta menene amfanin hakan. Haka dai Hindatun ta Lallab'a Malam Buba wai kai ta dan huta sabo da d'anyen jiki na jego, da haka suka tausheshi ita da Ummi Ishalle har dai ya hak'ura. Amma ita Umma Kande cewa ta yi karta yarda ta tafi ta zauna anan ayi suna tare da na Hindatun dan Dr Ayuba ya yankawa d'an nata abin yanka dan ta san ba lallai Aliyu ya bata yanka ba, sabo a sunan ABIDA ma wasu d'an akuyabin ya siyo sai Hindatu ce ta bayar ask siyo manyan raguna guda biyu dan haka yanzu ma gwara ayi sunan tare yanda Dr zai mata duk abin da ya yiwa Hindatun.Sun yiwa Dr Ayuba godiya akan biya musu makka da ya yi, ya nuna musu babu komai kawai su godewa Allah domin shi ne ya kirasu, shi Dr sanadi kawai ya yi. Sun ji dad'i da karamcin irin na sirikinsu Dr amma umma kande a cikin ranta haushin Dr Ayuba ta ke ji saboda bai biyawa Ikilima ba
Ranar da suka cika kwana biyar da haihuwa, Dr ya bada buhun shinkafa 2 taliya cartoon 3 buhun nikarkiyar masara dana hatsi sai kuma kud'in raguna guda biyu. Duk taurin rai irin na Ikilima da ABIDA sai da suka ji dad'i kuma suka ji a ransu lallai Hindatu mutumce kuma tabbas tana da kyan zuciya, sai dai hakan bai sa sun ji cewa Wataran za su janye mugun nufinsu akanta ba. Suna ya kama guda biyu anayi a Kano ana kuma yi a Gumel, Dr ya kashe kud'i sosai an ci an sha an raba kaya na gani a fad'a yarinya ta ci suna Fadila kowa ya yi farinciki da wannan rana. A can Gumel ma ana ta buduri su kande anci shinkafa an ci nama har sai da aka kwana zuwa bayi ana gudawa, y'an garin kukayasku kwa sun sha gori wai k'walamar shinkafa suka zo.Yaro ya ci suna SAFWAN an rak'ashe sosai su Ikilima manyan makwadaita wai Allah sa ta k'ara haihuwa a Kano, in ji umma kande da ta ke sud'in hannu tana cin naman kai 🥵
Yaya Nana tun da ta tafi daga kan wata bola haka ta kama hanya tana ta tafiya har sai da ta gaji sosai k'arfinta ya k'are ta galabaita sosai ga yunwa ga wahalar tafiya,haka ta fita daga cikin gari ta fara fita wajen gari gajiyar ce ta mata yawa ta samu wata bishiya zauna tun tana zaune har ta fara gyara gyad'i har dai barci ya d'auketa a wurin cikin barci ta zame ta kwanta a wurin. Bayan kamar awa biyu ta farka tana farkawa ta ji yunwa sosai dan dama itace ta tasheta. Wahiawa ta yi ta ga babu wani abun da za ta ci sai kawai ta fara cirar ciyawa tana sawa a baki,tana ta cirar ganyen ciyayi tana ci sai ga wata mota ce hilux ta tsaya daga can baya daga in da ta ke mutane biyu ne suka fito daga motar d'aya daga mazaunin direba d'aya kuma daga gefen me zaman banza,nan kowa ya lura da Yaya Nana da ke cin ciyawa, cikin hanzari suka k'arasa wurinta, suka dakatar da ita daga cin ciyawa amma ta k'i anan d'aya ya koma cikin motar ya d'akko biredi da pure water guda biyu tana hango biredin nan ta dena cin ciyawar da gudu ta nufi mutumin me d'auke da biredin ta warce biredin ledar ta yaga ta fara ci kamar bata tab'a cin abinci ba. Tausayinta ya kamasu, ganin ta zauna ta maida hankalinta kan cin biredin suka ajiye mata ruwan suka juya suka koma mota ruwa dama Malam Habu zai kama shine dalilin Tsayuwar ta su, lokacin da Malam Habu ya taho daga Inda ya kama ruwa, a lokacin har Yaya Nana ta cinye biredin tas tana shan ruwan, dede zai shiga motar dan dama shi Malam Inuwa yana cikin motar wani mutum da motarsa ta tsaya ne ya k'ara so wurinsu ya musu sallama tare da neman alfarmar su daure su tura masa motarsa ta tsaya. Bin bayansa sukayi suka je suka tura masa motarsa dak'er ta tashi,haka suka dawo wurin motar tasu,amma sai ba su ga wannan mahaukaciyar da su ka baiwa biredin nan ba, sai su ka d'auka ta tafi, motar suka tafi dama Kano suka zo suka kawo buhhunan hatsi da na rid'i domin Malam Habu manomine da ke zaune a wurin, yana kai kaya cikin Kano ya siyar, yanzu ma kayan suka kai shi da abokinsa Malam Inuwa ya rakashi .Suna tsayawa suka fara musabiha domin kowa zai shiga gidansa sabo da Malam Habu da Malam Inuwa mak'otane kuma abokan juna, Motar nan ma ta Malam Inuwa ce amma a cikinta aka kai buhhunan.
"Lah Malam Habu ka manta da sakon Talle na barkonanta so ka ke ta koroka idan ka shiga gidan" Cewar Malam Inuwa yana dariyar tsokana.
"Ka ga kwa na manta kwata -kwata amma kuma ai kasan ko zaure ba ta koroni ba" Shima ya ce yana dariya.
Nufar bayan motar ya yi zai d'akko buhun barkonan, yana lekawa me zai gani
"Malam Inuwa ka...ga... wannan...... "
Ai kafin ya k'arasa fad'a har Malam Inuwa ya k'araso, shima mamaki ya lullube shi."Ikon Allah to daman nan ta shiga " Malam Habu ya ce cike da mamaki.
"Nima abin da na ke tunani kenan, ina ga lokacin da muka tafi mu turawa wannan mutumin mota ta shiga bayan motarmu.
"Tabbas shi ya sa da muka dawo muka rasata"
Suna ta Al, ajabin ganinta kwance a bayan motar amma ita Yaya Nana barcinta ta ke hankali kwance. Haka aka tasheta daga barcin dan Talle matar Malam Habu da Rabi matar Malam Inuwa aka kira suka kamata dak'er ta yarda ta shiga gidan Malam Habu dan anan aka yanke shawarar ta zauna, tunda gidan ba yara bare su dameta dan Malam Habu bai tab'a haihuwa ba.
BAYAN SHEKARA BAKWAI
Yaya Nana na gani zaune akan tabarma tana karanta Qur, an ita kuma Talle tana bakace hatsi dan wannan bakacen ma dak'er Yaya Nana ta barta take yi dan komai na aikin gidan ita ta ke yi. Yanzu Talle ta d'auki Yaya Nana da suke kira da Amina dan ba su san sunanta ba itama kuma Yaya Nana ta manta da sunanta kai ba sunanta ba hatta komai nata ma ta manta.Dan tun sanda ta dawo gidan Malam Habu da zama Talle ta ke kula da ita sai Rabi da ke shigowa wani lokacin tana tayata kula da ita duk da hauka tuburan ta ke yi dan wani lokacin ma sai an daureta amma a haka suka ci gaba da kula da ita, suke nema mata magani dan sun fahimci sammu ne abin ba wai mahaukaciya bace tun asali. An sha wahala sosai kafin a samu maganin dan sun kashe kudade masu yawa wajen neman maganin ,har dai aka dace lafiya ta fara samuwa kad'an kad'an har dai ta warke sai dai kuma ta manta da komai ta manta Wacece ita cigiya har gidan TV dana rediio su Malam Habu suke zuwa su yi ko Allah zai sa a samu y'an uwanta amma dai har yau shiru.
Gidan Aliyu mijin Ikilima na hango k'ofar gidan an masa penti rangad'a d''a d'au, cikin gidan na shigo shima na ga an yi gini a inda filine da a wurin mata sai shige da fice su ke, wasu na Jere a kicin wasu kuma suna ta gyara abin da be yi ba a falo da d'aki,dan yau za, a kawo amarya shema,u sai Shirye Shirye ake dan karfe biyar na yamma za a kawota sabo da dokar da Alhaji Ahmad Muhammad sani, wato sarkin Gumel ya sanya ta hana d'aukan amare da daddare. Duk wannan buduri da ake Ikilima bata sani ba suna can sun tafi wani k'auye cikin Niger wurin wani boka da zai musu aiki akan Hindatu, ko SAFWAN ma can kukayasku ta kai shi dan dama ya fi zama a can dan ita kullum tana yawon barbad'a .Yau kwanansu goma a can ita da ABIDA dan auren nan ma bata san Aliyu zai yi ba,.
Dan sahu ne ya tsaya a k'ofar gidan Aliyu, Mama Ikilima ce da ABIDA suka fito suna yiwa gidan na su kallon mamakii ganin ya sha penti ga kuma mata na shiga suna uzurinsu dan tuni an tafi a taho da amarya, gidan suka shiga dan sanin me ke faruwa, Ikilima ido biyu ta yi da ginan nan b'angaren da ya fi shekaru biyar a gine amma a d'an kwana goma da sukayi basa nan har an yi plasta an yi penti har Jere an yi kafin ta gama tantance abin da ta ke gani sai jiyo muryar mata ta yi suna rangad'a gud'a ana cewa amarya ta k'araso. A take Ikilima ta ga gidan na juya mata kafin me wannan sai kiji ka ke gif ta fad'i kamar wata tsohuwar saniya.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala