🅿️3️⃣0️⃣⏩3️⃣1️⃣
"Albishirinka" Ta ce cike da farincikin, daga can Dr yana jin irin zak'uwa da son sanar da shi albishir d'in a muryarta.
"Amma dai duk albishir d'in da za ki min ba kamar ganinki ba, na fi so in ganki ko hankalina zai kwanta "
"To nima ina son ganinka,bari in kwatanta maka in da na ke sai ka zo "
"OK ba damuwa, kina nufin bakya wurin taron nan "
"Eh ban je wurin bama yanzu haka ina government Hospital Allah ya saukeni lafiya na samu...
"Babu irin wannan wasan tsakaninmu, dan Allah kar ki sa zuciyata ta tsinke wallahi har kin sa na d'ora rai akan zan ga jinina a yau! "Dr ya katseta cikin hanzari.
"Wallahi da gaske nake,ka kwantar da hankalinka ka....
Ai kafin ta kai k'arshen maganar tata ba ya kashe wayar, daman lokacin an kammala komai sai abubuwan rabo da ake rabawa, a hanzarce Dr ya kira direban da ya kawo su key d'in motar ya karb'a ,ya nufi in da aka ajiye motar ya bud'e yana k'ok'arin shiga IMRAN ya hangoshi da sauri ya nufi inda ya ke dan ya san ba karamin abu bane da zai sa Daddyn ya bar wurin taron ba kuma ba tare da kowa a tare da shi ba, direba bai yi driving d'inshi ba sannan kuma bai nemi IMRAN d'in ba. Ya kusa k'arasawa wurin Dr ya figi motar ya fita daga harabar asibitin. Wurin direban abokan Daddyn ya nufa ya karb'i aron key d'in mota ya marawa Dr Ayuba baya dan ko kad'an bai yi tunanin kiransa a waya ba.A asibiti kuwa Hindatu jin da ta yi Dr ya kashe wayar ta kasa daina murmushi dan ta san yanzu zai bayyana a asibitin, itama Hanne murmushin take, jin an doka wani tsaki ya sa Hanne da Hindatun kallon Ikilima da ta yi tsakin, kallon ido cikin ido sukayi itand da Ikilima kafin ta mik'awa Hanne jaririyar ta sakko da kafafunta k'asa a hankali dan har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba tana d'an jin jikinta na ciwo hakan ma ba zai rasa nasaba da rashin wanka ba, dan da ta yi wanka da ruwan zafi da ciwon jikin ya barta .A haka ta lallab'a ta k'arasa gadon y'ar uwarta duk da harara da Ikilima ke aiko mata, tana zuwa ta ce
"Haba y'ar uwata bai kamata wannan kalaman da ki ka yi yanzu ya fito daga bakin ki ba,ni fa y'ar uwarki ce wallahi har cikin raina nake kaunarki ban tab'a miki Y'AN UBANCI ba...
"Dan Allah Hindatu ki kyaleni kaina ciwo yake banason hayaniya "Ikilima ta katseta cikin hanntara.
" Shikenan Allah baki lafiya "
"To na ji ai sai ki koma gadonki"
"Toh bari na ga jinjirin,, kawo shi ABIDA " Ta ce tana mik'a hannu ya za ta karbeshi.
Da kamar ABIDA ba za ta bata shi ba, kuma koda me ta tuna ta mik'a mata shine.
"Tabarakalla Masha Allah"cewar Hindatu ganin yaron kyakkyawa da shi ta jima tana kallonshi shima tana jin kaunarsa kamar dai yadda ta ji kaunar jaririyarta, dan ita duk d'aya ta daukesu duk da ba kamar wanda ka haifa ba amma shima zai sai ta ji shima tana kaunarsa. Addu, a ta tottofa masa har sai da Ikilima ta ce ta daina tofeshi da matan, sannan ta yi murmushi ta mik'awa ABIDA yaron ta koma gadonta. Zamanta ke da wuya sai ga Dr ya shigo da shi da Likita da kuma nurse guda d'aya, suna shigowa sai ga IMRAN ya shigo hankali tashe kana ganinsa ka san akwai matsala dan duk ya rud'e da ganin Dr Ayuba ya nufo asibitin a tunaninshi ko Mamansa da ABIDA ne suka mata wani abu dan barin su da akayi a gidama hankalinsa bai kwanta ba dan ya gama sanin halin Mama Ikilima. Dan haka ma dak'er ya kawo kansa asibitin,Yana shigowa idanunsa suka sauka akan babyn 👶 da ke rungume a hannun Mummynsa, zaro idanu ya yi baki sake yake kallon Hindatu wani irin farinciki da annushuwa ya ke ji,bai gama mamakin ba ya ga Daddy (Dr Ayuba) ya je ya rungumeta ita da 👶 babyn sai godiya da kirari ya ke yiwa Ubangiji, akan kyautar da ya masa."Sannu my Hindy kin min komai a rayuwa Allah ne ya bamu amma tabbas kece sila Nagode miki kwarai da gaske sannan kuma albishir d'in nan da ki ka min na mallaka miki day'a daga cikin asibitocina, kuma hajjin bana ku shirya ke da Ummi ,Umma da kuma Malam" Ya ce yana kallonta.
"Masha Allah muna godiya Allah k'ara bud'i mai albarka da nisan kwana mai amfani, ya barmu tare, amma kuma su dai sa je ni kuma idan na yaye babyn mu sai in je" Ta ce tana kashe masa ido d'aya.
"Hindatu ni mantawa da tawa haihuwar ki ka yi baki fad'a masa ba"Ikilima tace tana dariyar da ta fi kuka ciwo ,sabo da hajjin da aka biya musu a kokon ranta duk da har mahaifiyarta aka biyawa hakan bai sa ta ji dad'i a ranta ba.
Wannan maganar da Ikilima ta yi ita tasa IMRAN ya lura da su dan daga shi har Dr babu wanda ya gansu, ita kuma Hindatu ganin mai gidanta cikin wani irin yalwataccen farinciki ya sa ta manta da su a wurin.
" Ayya walllahi aunty Ikilima na sha,afa ne, sweet heart tare fa aka kawomu da aunty Ikilima ita kuma baby boy muka samu "ta ce tana sakar masa baby da suka rik'eta tare.
"Kai Masha Allah haihuwar har biyu to bari in gama ganin wannan sai in ganshi ko" yace lokacin da ya sanya bakinsa jikin kunnen baby zai mata kiran salla.
Shi kuma IMRAN gadon da Mamansa ta ke ya nufa yana cewa
"Wallahi Mama bamu lura da ku ba,ashe har ABIDA ma kuna tare amma bata min magana ba " Yace sanda ya ja wata kujera ya zauna a gaban gadon Ikilima.
"Eh ni na hana ABIDA ta maka magana sabo da na ga hankalinku ya tattara akan Hindatu shi yasa, ka ga idan kun gama murnar sai ka dawo wurina nima ka mini sannu "Cewar Ikilima tana wani yatsina fuska, dan daga Dr har Hindatu babu wanda ya san me take yi hankalinsu na kan babyn. Bare Hanne da tun shigowar su Dr ta fita waje.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala