YAN UBANCI

40 1 0
                                    

        🅿️4️⃣0️⃣⏩4️⃣1️⃣

   Wani matashi na gani cikin dare ya nufi makabarta, ciki ya shiga yana waige waige alamar rashin gaskiya tattare da shi bin bayansa nake ba tare da ya sani ba, har dai ya je dede kan wasu sabbin kabarbura, haska fitilar wayarsa ya yi a jikin allon da ake rubuta sunan mutum da ranar da ya mutu, sai da ya tabbatar wannan ne kabarin da ya ke nema kafin cikin hanzari da zafin nama ya shiga tone kabarin har sai da ya bud'e kabarin tsaf sannan ya fito da gawar da ke nad'e a cikin likkafani, ajiyeta ya yi a gefe ya  maida komai na kabarin ya rufe ba zaka tab'a cewa an tona ba. Kinkimar gawar ya yi cikin sauri ya fito dan bayaso me gadin makabartar ya ganshi, sai da yayu tafiya mai dan nisa kafin ya zi im da ya yi parkin d'in motarsa yana zuwa ya sanya gawar a bayan motarsa ya shiga ya bar wurin  a 360.hanya ya d'auka sosai wacce za ta kaishi bayan gari sai da ya yi nisa sosai sannan ya samu wuri ya faka motar, cikin hanzari ya fito ya bud'e bayan motar gawar nan ya bud'e ya dakko wata doguwar riga sabuwa a ledarta ya sanya mata ya jefar da likafanin ya gyara mata kwanciya ya shiga motar sai da ya je wata gona da ke d'aya daga cikin ginakin da ke mak'otaka da wudil sannan ya faka motar ya fito da gawar ya  ajiyeta a wurin sannan ya tsugunna akan gawar ya fara magana kamar haka.

"Na san kina jina dan haka nakeso in miki bayanin abin da ya faru dalla -dalla, na tab'a haduwa da ke a garin Gumel wata rana, na yi sata an kamani yara da manya na ta kallona hakan ya sa na ji ciwo sosai a raina, y'an sandan sun sanya min ankwa kenan sai gaki a mota  kun zo wucewa haka kika sanya direba ya tsaya ki ka fito kika tambayi meke faruwa, anan aka baki labarin abun da ke faruwa, haka kika shiga mota ki ka bi motar yan sandan nan har police station ki ka yi belin d'ina sannan kika taho dani kika mun nasiha akan in bar yin sata in koma karatu na ce miki karatu baya cikin tsarina haka kika d'auki kud'ad'e masu yawa kika bani in je in yi sana, a, wannan abun da kika min ya dad'ad'a min rai amma kuma banyi sana, ar ba, na kashe kud'ad'en to a lokacin da wanda suka bamu aikin nan suka nuna min hotonki ina ganinki na ganeki sai dai babu yadda zanyi insa su fasa k'udurinsu dan ko ban karb'i aikin ba nasan za su samu wasu su basu aikin dan haka na karb'i aikin akan zan kubutar da ke, bayan an kamoki ni na bada shawarar a miki allurar poison haka suka amince ba tare da sun nemi dalili ba. Dan ko da aka tashi sai na ce ni zan miki allurar dan haka sai na canja allurar daga ta poison zuwa wacce za ta sa ki suma na wasu a wanni to shine yanzu na je na tonoki dan haka yanzu idan kin gama dawowa hayyacinki sai ki tafi inda zaki kar ki tab'a komawa gida matsawar kinaso ki rayu da ranki dan wanda suka bamu aikin nan basu da imani za su iya kasheki ko da yaushe ko su sa a kasheki dan haka yanzu sai ki je wani wuri ki cigaba da rayuwarki nagode"Yana gama fad'in haka ya shiga motarsa ya bar wurin a guje.

   Sai da hasken rana ya fito ya haske fuskarta wannan ne dalilin da ya farfado da ita  a hankali -a hankali take bud'e idonta wani haske ta gani gaw wanda ya sa ta yi saurin maida idon ta rufe, jim kad'an ta sake bud'ewa kad'an haka ta dinga yi da kad'an -kad'an har dai ta bud'e idon gaba d'aya. Wurin ta ke bi da kallo har dai ta fahimci a dokar jeji ta ke haka ta tashi ta zauna a hankali ta ke bin jikinta da kallo nan take abin da ya faru da ita ya shiga dawo mata, tun daga lokacin da aka tafi da ita da direba har zuwa lokacin da wannan matashin ke mata bayani, amma bata san ya akayi ba da aka binneta  a matsayin gawa dan bata san me ya gudana ba ta dai ji an fitar da ita daga wani wuri mai mugun matsi da aka sanyata  ,kenan wannan wurin kabari ne, lallai Allah ka rabamu da duhu da kuma azabar kabari ta ce, sai kuma maganganun da matashin ya mata tabbas ta ji maganganunshi, dan lokacin allurar ta saketa hayyyacinta ne kawai bata dawo ba,nan take kuma ta tuno da cewar ta ji matashin nan ya ce mijinta ya mutu, itama dan ya ceceta ne da yanzu kasheta za ayi, nan ta  fara kuka mai tsuma zuciya na rashin mijinta mai sonta da kaunarta, sai kuma ta shiga tunanin halin da IMRAN da kuma FADILA za su shiga su ma tana tsoron kar a cutar da su to shin wanene wannan me sanya a kashesu a kawo masa takardun kadarori?  ya ma akayi ya san da zancen takardun har haka ta faru? lallai akwai lauje cikin nad'i, shin shi ya kauro zaman duniyar ne da ya ke sakawa a karb'o masa abin duniya, haka dai ta yi ta sak'e -sak'e kafin daga bisani ta tashi daker ta tako a  hankali har ta zo bakin titi tsallakawar da za ta yi sai kawai ji ta yi mota ta yi sama da ita.

"Subhanallah Innalillahi wa inna ilaihir raji, un "Malam inusa da Malam Inuwa suka fad'a a tare ganin sun bige mace wacce ba su ga tahowarta ba sai kawai ganinta sukayi ta hauro tsakiyar titi kafin Malam Inuwa ya taka birki har mai afkuwa ta afku. Haka suka kama ta suka sanya a mota suka nufi gari da ita domin kaita asibiti dan dama ana fitowa daga masallacin asuba suka tafi gonar Malam Habu domin yin gewaya shine haka ta faru a hanyar su ta dawowa. Emergency aka shiga da ita nan take likitoci suka dukufa akanta har dai suka samu nasarar ceto ranta.An sanya mata drip inda kuma aka gane babu jin ciwo a jikin nata, anan ne su  malam suka kira gida suka sanar da iyalansu abin da ya faru, sai wajen azahar matan nasu suka zo da kulolin abinci suka duba jikin Hindatu dan lokacin har drip din ya k'are tana zaune amma bata magana sai dai idan an mata sannu ta gyada kai. Dan gaba d'aya abin duniya ya dameta, wajen karfe biyu na rana aka sallameta suka dawo gida sai dai Hindatu gidan Malam Inuwa aka kaita tare da matar Malam Inuwa a cewar Malam Inuwa  tunda kwanaki ne za ta yi idan warware sai ta kwatanta gidan su a kaita. Haka Malam Habu ma suka shiga gidansu a lokacin Yaya Nana tana tankade garin tuwon dare, sannu da zuwa ta musu da ban gajiya suka amsa fuska sake dan suna jin dad'in zama da ita sosai dan yanzu sun d'auketa a matsayin y'ar su tunda gashi har shekara goma sha biyu amma babu labarin y'an uwanta har sun gaji da cigiya sun hak'ura tfn su  Allah ya bata miji ta yi aure.Nan ta ke tambayar iya Talle mai jikin, ta ce idan ta yi sallar la, asar ta je ta dubota a gidan babanta inuwa, da to ta amsa mata a ladabce, hakan ya sa iya Talle ta ji kamar y'ar da ta haifa.

   A b'angaren su Ikilima ma kwa tun kan a sanar da su mutuwar su Hindatu Okasha ya sanar da su amma ko  a jikinsu to da me ma zai damesu tunda su suka bada aikin suka kuma ce idan ma kisa ya kama ayi dan haka da ya fad'a musu ma mutuwar cewa sukayi Allah jik'an  rai dan su duniyar ce kawai a gabansu, tunda dai takardu sun zo hannu basu da wata damuwa. Dan Okasha ma bai sanar da su abinda ya yiwa Hindatu ba, dan ya fahimci basu da imani bare tsoron Allah, shi yasa ya kyalesu dan haka da suka baro kano ma Gumel suka zo suka damka musu takardun, sai kuma Ikilima ta ce su koma da dare can gidan Dr ABIDA za ta musu jagora su dakko kud'ad'e a ciki za su sallamesu to komawar da sukayi ne bayan sun d'akko kud'in ba tare da an kamasu ba, dan babu kowa a b'angaren Dr hakane ma ya basu damar cin karansu ba babbaka dan lokacin kowa hankalinsa a tashe ya ke. Kud'ad'en da suka d'akko kimamnin miliyan biyar ne dan haka su Okasha ko kwandala basu baiwa su Ikilima ko kwandala ba dan cewa sukayi ma ba za su karb'a ba, dak'er suka karb'a to bayan sun raba kud'in ne Okasha ya zame jikinsa ba tare da kowa ya  sani ba ya je ya tono mummy Hindatu.

   Misalin k'arfe biyar na yamma Yaya Nana ta gama komai dan yau bata da zuwa islamiya malamin dake d'aukan class d'insu baya jin dad'i dan haka yau hutu suke. Bayan ta kimtsa  sosai ta yiwa iya Talle sallama domin zuwa gidan Malam Inuwa ta dubo bakuwar da aka kad'e. Da sallama ta shiga gidan ta tsugunna har k'asa ta gaishe da matar Malam Inuwa sannan ta tambayeta me jiki ta amsa mata, d'akin da aka ajiye bakuwar ta nuna mata akan ta shiga ta mata sannu duk da ta san ba amsawa za ta yi ba, sai dai ta ghad'a kai.

"Assalamu Alaikum "Yaya Nana ta shiga dakin bakinta d'auke da sallama.

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now