🅿️4️⃣4️⃣⏩4️⃣5️⃣
"Bismillanku"Malam Buba ya ce yana juyawa suka mara masa baya, a zauren gidan ya musu masauki dan dama manyan tabarmine a zaure a shimfide, da yake zauren na da girma sosai hanyar wucewa ce kawai babu tabarma, bayan kowa ya zazzauna Malam liman ya ce a sanarwa kowa na gidan ya zo domin ayi magana a gaban kowa, haka Malam ya shiga gidan ya sanar da su cewa suna da baki kowa yazo zaure, haka Malam buba ya yiwa kakan Dr waya cewa yazo shi da iyalansa akwai muhimmin abu a gidansa, daman iyayen na Dr sun zo biki garin haka suka taho dan ganin abin da ke faruwa. Ummi Ishalle ce a gaba ta shigo bakinta d'auke da sallama, ta samu wuri ta zauna ta gaishe da su bata gane Nana da Hindatu ba da yake suna daga can k'arshen zauren kuma da d'an duhu, sai ga ABIDA da umma kande sai Ikilima da itace shigowar K'arshe ta tsaya can tana yiwa FADILA masifa wai karta k'ara taba musu komai na gidan sbd gaba d'aya kurajen babu masakar tsinke, sai durar ruwa suke abin tausayi. Sun zazzauna cikinsu babu wanda ya gaishe da bak'in bare ya musu sannu da zuwa suma ba su gane si Nana ba dan duhun zauren shikwa dr dama kai ya Sunkuyar ba wanda ma ya kawo aka,, Ikilima da ABIDA aka nunawa can gefen inda su Nana suke zaune sbd iyalan gidan su Dr da suka shigo aka basu waje kowa ya zauna aka gaggaisa kowa ya kasa kunne yana sauraron banda malam buba dake jiran jin bayani dan shi ya ga kowa. Ikilima ce da shegen tsegumi ta kurawa matan nan biyu da suka zauna kusa da su aikwa idanunta ya sauka akan mummy Hindatu cikin azama ta matsa sai kuma ta fara karkarwa da sumbatu
"wayyo dan Allah fatalwa karki kasheni, ki min rai wlh bazan sake abinda nayi ba, dan Allah karki ke tsoratani wlh dama Umma Kanden ke sakani komai na biye-biyen bokaye akan neman duniya itace kuma ke nuna min in tsaneki tun tasowarmu itake cewa inke nuna miki y'an ubancin ke ba me k'aunata bace wlh bayin kaina bane duk zugarta ce, kuma wlh ko takardun kadarorin mijinki dana sa aka karbo suna nan a gida a ajje babu abin da na musu in ma so kike in maida sai in mayar da kaina nidai kiyi hak'uri kar in ke ganin fatalwarki, wlh ko yau ma ruwan sammun dana watsawa yarki umma kande ta sakani akan tunda baki raye kowane y'an ubancin ya koma kan yarki ita tasa akayi asiri aka d'auke hankalin Malam dana IMRAN dana Ummi Ishalle dan kawai yarinyarta taso babu gata" haka nan Ikilima ke ta faman zayyano abubuwan da sukayi ta yi a rayuwa har wanda suka saka IMRAN yaki ke duk wani tsubbu da makirci da sukayi sai da ikilima ta fad'a, tanayi tana rarrabewa a jikin bango kamar kadangaruwa, hakan da ta yi shi ya ankarar da kowa cewa Hindatu na wurin, kai hatta yaya Nana da kowa mutuwar tsaye sukayi jin sune silar b'atan yaya Nana, kowa ya ga Dr amma umma kande sai zare ido take har da sakin fitsari ganin mummy Hindatu wai ita dole ta ga fatalwa, anan itama ta ringa zayyano nata har asirin micijin da aka sanyawa ummi Ishalle sai data fad'a. Dak'er suka yarda sukayi shiru dan ABIDA ma sai fad'in wasu take gashi sun kasa tashi dan duk a tsure suke suna ganin idan sun gudu ma zasu ganta a duk in da suka je. Nan dai akayi shiru Malam liman ya zayyana komai da komai, banda kabbara babu abinda kake ji, sai kuma jikin su umma kande da ABIDA da Ikilima ya yi sanyi jin ba fatalwa bace gashi kuma sun tonawa kansu asiri, haka dai akayi shiru, sai Yaya Nana ta ce tana da magana bayan an bata dama sai ta ce.
"Dama batun y'ar gidan Hindatu nakeso in yi na ji ana cewa y'ar ta aka watsawa, ruwa, sannan kuma Hindatun ta fad'a min cewa haihuwarta d'aya, ko zaman da mukayi a wudil idan na tambayeta ina d'ana sai ta ce yana lpia to shine nakeso in sani wace y'a ce ake magana "
haka aka bayyanawa yaya Nana komai anan ta ce tana da magana.
*DARA TACI GIDA*
*SHARRI DAN AIKENE*
*IN ZA KA GINA. RAMIN* *MUGUNT*" A sani na Hindatu d'a namiji ta haifa, ita kuma Ikilima y'a mace ta haifa kuma ni da na kawo yaran ban bamcewa su ABIDA cewa ga jinsin da kowacce ta haifa ba, amma ai ita me karbar haihuwar ta san cewa ga abinda kowacce ta haifa mesa bata banbance ba"yaya nana ta fad'a tana kallon Hindatu, kowa ya saki baki da mamaki kalaman da suke fitowa daga bakin yaya Nana, wani uban ihu Ikilima ta kurma nan ta hau zage zage akan cewa karya yaya nana take, aka dinga tafka musu anan Dr ya tambayeta ko ta san sunan matar data karb'i haihuwar fad'a masa ta yi dan bata manta ba, wayar Malam buba ya karb'a ya kira IMRAN ya sanar dashi ya je ya sanar da shugaban asibitin shi ya aikoshi a tafi da metron d'in ,sosai IMRAN ya shiga farinciki jin muryar dr yana ji dama a jikinsa dr bai mutu ba ,haka ya d'akok matar nan ya biya gida ya dakko iyalinsa suka tasamma kukayasku matar tana ta fargaba, amma ta wani sashen tana murna dan tunaninta ko haihuwa za ta karb'a shisa shugaban asibiti ya bada sunanta na ce hmmmm.
a can ma kukayasku Malam buba kiran Aliyu ya yi mijin Ikilima akan ya dakko duk iyalinsa su taho kukayasku, haka kwa akayi sai gashi ya zo shi da shema, u, SAFWAN sai kuma SAFNA wacce ke da shekaru uku kyakkyawar yarinya son kowa k'in wanda ya rasa. Suna zuwa mummy Hindatu da Dr na kallon SAFWAN suka gano tsananin kamar da yake yi da Dr komai nashi har tafiyar irin na Dr ne, wanda a da basu ga hakan ba, bayan zuwan su Aliyun da kamar awa d'aya sai ga su IMRAN sun k'araso, Aliyu ya ji miyagun aiyukan da matarsa Ikilima da y'ar sa ABIDA, ta aikata ya kuma yi ce Allah shiryesu dan ba zai musu baki ba,dan laifin duo na umma kande ne ita d'ora Ikilima akan mummunar akidarta, itama ta yiwa ABIDA tarbiyar da aka bata kenan,shima da lefinsa da ya zab'i Ikilima a matsayin matarsa yana da kyau mu zab'i abokan zama nagari dan su dora mana yara akan tarbiya da turba tagari.
An tambayi matar ta tabbatar da cewa haka zancen yake kawai ta banbantawa su Ikilima y'ay'an ne jin an ce mijin Hindatu yana da arzik'i kuma wannan ce haihuwarta ta farko hakan ya sa ta ji kyashi da Hassada shi yasa ta ce mace Hindatun ta haifa dan kar su samu gado idan Dr ya mutu, su samu kaso mai yawa kinga idan macece ba za su samu wani gado mai yawa ba kamar na d'a namiji, anan matar ta nemi yafiyar Dr da Hindatu suka yafe mata, nan take Aliyu ya dankara Ikilima saki har uku, sannan ya mik'awa su Hindatu SAFWAN ya kumskuma sa aka kira masa FADILA tana fitowa kowa sai da ya zubar da hawaye dan tausayinta, Ikilima kwa sai rusa kuka take ganin yadda ta maida y'arta ta cikinta da hannunta, ga muguwar azabar da suka sha dandana mata duk a rashin sani.haka Malam liman yasa hannu a aljihu ya fito da wani kullin magani aka bashi ruwa ya zuba ya yi addu, a ya watsa wa FADILA ruwan sai gashi kurajen sun bata bat, yace yayi ne dan fa FADILA da Aliyu ba dan Ikilima ba dan da a jikinta kurajen suke sai dai ta dandana kudarta tunda babu imanj a zuciyarta. Haka Aliyu ya tafi da FADILA da shema, u, SAFNA kwa dak'er ta yarda sai SAFWAN take yiwa kuka haka suka tafi shima ranshi babu dad'i dan da su ya saba.Malam buba ya kira mijin yaya Nana a waya ya sanar dashi komai shima beyi kasa a gwaiwa ba ya zo ya tafi da matarsa, Malam buba ma ya saki umma kande saki uku kuka da magiya amma yaki ya saurareta haka yace su fice masa daga gida ita da Ikilima, haka Aliyu na zuwa gida ya dakko takardun kadarorin Dr gaba d'aya a d'akin Ikilima ya kawowa Dr sosai sukayi mamaki da yadda abun ya kasance gashj dai Ikilima ta sa an sanya sunan SAFWAN a jikin takardun ba tare da ta san dama ba danta bane, gashi shi kuma Dr burinsa ya cika na son mallakawa dansa takardun kadarori gashi ba sai an sha wahalar canjawa ba Allah kenan.
*BAYAN SHEKARA 18***
Rayuwa taci gaba da kasancewa cikin farinciki da kwanciyar hankali, Yaya Nana y'ay'anta uku, biyu maza d'aya mace, Mummy Hindatu ta sake haihuwar yan biyu duk mata hassana da husaina, IMRAN ma yanzu yayansa hudu, sai shema, u data kara biyu, ABIDA ta samu wani mutum mai mata biyu ta je a ta uku yanzu duniya ta ta koya mata hankali. Umma Kanden mutuwar barin jiki ta sanya daga karshe tayi ta jinya har tace ga garinku nan,, ilkilma ce mota ta kadeta har aka yanke mata kafa d'aya yanzu tana nan tana tafiya da sanda Duniya kenan.
Anyi bikin SAFWAN da SAFNA auren soyayya auren gata,auren da kowa ke alfahri da shi, sun zauna cikin farinciki da kulawa da junansu, haka sukayiSukayi tahayayyafa suna rike zumunci.
Alhamdulillah anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa y'an ubancin abin danayi kuskure Allah gafartamin na fadakarwa Allah hadamu a ladan,godiya da dimbin yabo ga masoya da suka yi ta bibiyar wannan labari tun daga farko har K'arshe, sannan ina jinjina ga masoyana da suka jure yimin sharshi, har karshen buk din ina godiya bazan taba manta soyayyar ku ba.
maman afrah no 09030283375
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala