YAN UBANCI

47 1 0
                                    

   🅿️1️⃣3️⃣⏩1️⃣4️⃣

"Eh acan nake wlh" ta fad'a kamar za ta fashe da kuka ganin yadda ya ke wani yatsina fuska, alamar ba lallai bane ya amince da ita ba. K'ara damk'e maganin nan ta yi  a karo na biyu da mugun k'arfi .

Aliyu da ke shirin juyawa ya koma cikin mota amma sai ya ji wani iri a ransa ji yake idan ya rabu da ita zai iya shiga damuwa.

"Lah meye na b'ata rai kukayasku ma ai gari ne kuma mu ma  duk asalinmu k'auye, ni
ke nake so dan haka kar ki damu idan Allah ya sa ke mata ta ce za mu yi aure, idan kuma ke ba mata ta bace, haka Allah ya kaddara"

"Allah ma zai sa mu yi aure "ta ce a zuciyarta  a zahiri kuma ta ce. "Allah zab'a mafi alheri"

"Amin" yace  ,anan dai suka d'an tab'a hira kafin daga bisani Aliyu ya karb'i phone number d'inta  suka yi sallama ya d'auki 3k ya bata wai ta sanya kati.Murna wurin Ikilima ba, a cewa komai burinta da na Ummarta zai cika za ta yi aure a binni.Tana zuwa gida ta d'auki jakar da ta zo da ita ta ce ta tafi gida za ta koma, su Nana fatan sauka lpia suka mata dan yaya Nana har 500 ta hau mota, haka ta tafi domin tana so ta je ta kai wa Ummarta  wannan labarin mai mugun dad'i domin asan yanda za,ayi kada Aliyun ya kufce musu.

  Umma Kande ta yi murna sosai da labarin da Ikilima ta kai mata, dan gud'a ta ringa rangad'awa wai y'arta ta yi goshi ta samu miji d'an birni mai mota .Haka ta je wurin Malami ya musu abin da suka  kama Aliyu a hannu.

  *BAYAN WATA UKU*

An yi bikin Aliyu da Ikilima, an kai amarya garin Gumel, a unguwar k'ofar saja, gida madaidaici ciki da falo sai kicin da bayi sai kuma d'akin mai gidan mai bayi  a ciki. Amarya ta yi sa,ar gida amma abin da bata sani ba shine bata yi sa,ar miji ba, domin kuwa Aliyun irin mazan nan ne da su ka yi hannun riga  da mutunci ga shi da mak'on tsiya.Ansha amarci lafiya a in da daga baya hali ya bayyana dan kuwa sai a sannan Aliyun  ya san Ikilima  ko aji bata tab'a shiga ba  aikwa daga nan salon ya sauya, itama kuma ta gama gane waye shi amma son zaman birni da son ace ta auri mai mota ya sa ta  watsar da duk wasu abubuwan  da yake mata.Bayan auren da wata  biyu Umma Kande ta kawo mata ziyara anan ta tarar da y'ar tata babu lafiya amma ko d'igon kulawa babu daga miji dan idan ya fita ma da safe sai dare ya ke dawowa sabo da  jinyar da take yi cikine da ita.Tunda ya san tana da ciki sai rashin mutuncin  ya k'aru. Dan haka ita Umma Kande da ta zo  ta samu kud'ad'e  a wurin Ikilima sai ta tarar da ita a halin buk'atar kud'in itama, dan sai da ta zo ta kai ta asibiti aka rattabo mata magunguna ta biya dan gaba d'aya babu  magungunan a wurin da ake ba da magunguna kyauta. Haka duk kud'in hannunta ya k'are, b'acin rai  da  bak'inciki  duk sun isheta  sai kwashewa Aliyu albarka ta ke wai ya cucesu dama ya san shi ba namijin da zai d'auki  d'awainiyar  iyali bane ya  auri y'arta. Haka dai  ta koma da damuwar halin da y'arta take ciki, ga babu kud'in hannunta dak'er kud'in hannunta  ya maidata gida. Wannan  kenan.

   Rayuwar ta ci gaba da gudana babu dad'i a wurin Ikilima, dan kullum Aliyu abin nashi gaba ya ke dan yanzu idan ya  ajiye kayan abinci ko kud'in cefane bai bayarwa, haka zai bar gidan dama shi ba a gidan yake cin abinci ba, dan haka yanzu komai ya cab'e  mata sai wayoyinta ta had'a ta siyar ta kama sana, ar siyar da itace da haka ta ke samun d'an abin rik'ewa a hannu.

 
  A haka har dai Allah ya sauketa lafiya ta haifo d'an tab'a namiji, haka y'an k'auyan kukayasku  su ke ta murna  zasu je su sha suna acii  dad'i amma tsabagen mugunta irin ta Aliyu ko k'wayar shinkafa bai kawotq ba, sai garin masara  da kub'ewa d'anya  wai ayi tuwo tunda su y'an k'auye ne ai tuwo ya kamata  su yi. Haka Umma Kande ta k'uk'uta  ta auno shinkafa  y'ar tsinta dan  a futa kunya kuma dan ta lullube  k'aryar da ta ke na suna sai Gumel  gidan Ikilima.Ana gobe suna Aliyu ya cewa Ikilima  bashi da halin yiwa yaro  yanka sai dai daga baya idan ya samu ya yanka, haka ta sha kukanta ta sanar da Ummarta haka Umma Kanden  ta harhad'a wasu kud'ad'enta da wasu a wurin Ikilima  aka siyo tunkiya dan gudun abin kunya. Ran Umma Kande in ya yi  dubu ya b'aci sai cewa  tayi ke.

"Wannan an yi kudurarran yaro uban shegen mak'on tsiyar jarraba, ni da nake so ka zama bawanmu mu yi ta wankarka amma sai gashi mu ka ke wanka banda tsagwaron wulak'anci  ace yanka ma ya gagareka  sai ni  zan yiwa d'an na ka yanka dan jaraba shinkafa ma ka kasa aunowa wai ta yi tsada ga buhariyya sai dai mu yi tuwon masara san ka sa y'an k'auyenmu su sani  a waka, kai Allah wadai  da wannan abu wallahi "take ta Fad'anta  kamar ta  kaiwa Ikilima  duka duk  haushi ya isheta. Ita kwa Ikilima sai  kukanta ta ke dan itama abin ya fara shallake tunaninta, su ma dangin mijin ba son ta suke ba, dan haka matar wan baban Aliyun  ma cewa tayi  ai komai  d'an  akwai ne in babu  sai hak'uri.

  Ranar suna  yaro ya  ci suna  IMRAN  gidan suna ya cika mak'il da mutanen kukayasku, Hindatu  ma sun zo ita da yaya Nana, amma Ummi Ishalle  ba ta samu zuwa suna ba sabo da  Malam baya jin dad'i. Ta dai zo barka ta kawo atamfa turmi da rigar yaro guda biyu, amma dan bak'in hali ko d'an ba,a bata ba.An gama jalof d'in shinkafa duk an zubawa Jama, a sai ci suke suna santi suna yaba kyan gidan Ikilima  da dace da  miji da ta yi wata ta ce.

"Gaskiya mijin Ikilima  ya yi  k'ok'ari a wannan marrar da ake ciki amma aka dafa shinkafa  ga wata dank'areriyar tunkiya hak'ik'a Ikilima  ta samu miki na nunawa sa, a"ta ce tana aika lomar shinkafa bakinta. sai wata ma ta karbeta.

"Eh wallahi kalli gida dai  ya kai  gida, ko a birnin ma ai ta kerewa sa, a, ga atamfofin da take ta  sawa kyatsa -kyatsa ai abin sai sam barka"

Umma Kande da ke gefe tana jinsu ta doka musu wata uwar harara, ba tare da sun ankara ba, hango Ikilima  da ta yi da d'aya  daga  cikin atamfofin  da ta ciyo bashi dan  a samu  a fita kunya. Tunda dama bai mata lefe ba kud'i kawai suka karb'a.

"Kande gaskiya  kin yi dacen  siriki Allah sa a dad'e anayi "cewar wata tana sud'ar  hannu dan ko gudun muwa bata bada ba, kai hasali ma y'ar aranni muje biki ce dan ba gayyatarta akayi ba. Dariyar yak'e Umma Kanden  ta yi ranta na k'una kafin ta daddage ta ce

"Walllahi kwa, sannan ta k'ara da amin amin"

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now