YAN UBANCI

38 1 0
                                    

🅿️2️⃣2️⃣⏩2️⃣3️⃣

"Haba yaya Ikilima  ki masa a hankali mana shi fa bawai wurinki ne ba ya son zuwa ba a, a gidan baba Malam ne bai so na tafi na barshi "Hindatu ta fad'a ganin Ikilima tana yiwa yaron tsawa kamar za ta kai masa duka.

"To uwar iyayi na ga dai d'ana ne ko zaki hana na masa fad'a "Ta fad'a tana wani mata kallo mai nuna tsantsar tsana da bak'inciki.

"ki yi hak'uri "Hindatu ta ce cikin sanyin muryarta.

  Banza ta yi da ita ta mik'a hannu ta rik'o hannun IMRAN da ta ke gani kamar wani d'an shugaban k'asa, ga wani kamshi da yake tashi daga jikinsa mai dadin shak'a. Cikin gidan ta shiga rik'e da IMRAN wanda ke waiwayen Hindatu,ita kuma Hindatun ta tsaya ta cewa direban ya jirata a mota bayan ya shigar da kayayyakin har da kayan IMRAN. Itama baya ta  mara musu ta shiga gidan d'auke da sallama ,IMRAN ne ya amsa mata ta samu wuri akan tabarmar da aka dora kayan da suka zo da su ta zauna. Gaishe da Ikilima ta yi ta  amsa mata ba yabo ba fallasa,daga wannan bata k'ara mata magana ba itama  Hindatun bakinta ta kama take danna wayarta, ita kuma Ikilima sai tambayoyi take jerowa IMRAN akan k'asar waje wani ya bata amsa wani kuma ya yi shiru dan dama ba mai hayaniya bane sosai. Ana haka sai ga Aliyu ya shigo d'auke da  pure water leda guda mai sanyi sai kuma d'aya hannun rike da bark'ar leda mai d'auke da lemukan roba guda hudu .

"Assalamu Alaikum " yace yana nuna tsantsar farincikin ganin IMRAN da Hindatu.

"Wa alaikumus salam "Hindatu tace tana murmushi kamar yadda shima ya ke murmushin dan ita Ikilima hankalinta yanzu yana kan kayan da aka kawo.

"Oyoyo abba" IMRAN ya tafi da murna ya rungume mahaifinsa.
    Bayan gaishe -gaishe da aka gabatar tsakanin Aliyu da Hindatu da IMRAN shi kuma aka shiga hirar yaushe gamo sosai Hindatu da  IMRAN suka saki jiki da Aliyun da ya gabatar musu da ruwan sanyi da lemon ma  Hindatun  ce kawai ta sha ruwan amma bata sha  lemon ba. Kuma koda Aliyu ya buk'aci Ikilima ta kawo mata abinci cewa ta yi bata gama ba dan mugun hali dan kar aci nama,ita kwa daman sauri ta ke ta je ta ga iyayenta haka ta musu sallama Aliyu yana ta mata godiyar kaya kamar ya ari baki ita kuma tana ta cewa ba komai, sun fito bakin kofa  ita da Aliyu da IMRAN suna Lallab'ashi akan ya yi hak'uri, aikuwa sai ga wata yarinya a guje kamar an biyota tana zuwa ba sallama ba natsuwa dan har buge Hindatu ta yi garin zuwa kusa da IMRAN, tana wani tattabashi tana washe hak'wara.

"Haba ABIDA  wai yaushe zaki nutsu me yasa kullum bakya tafiya ta natsuwa sai gudu kamar wata barewa? kina gani kika bige auntynki amma ko ki bata hak'uri "Aliyu ya mata magana ganin ko a jikinta data bige babba

"Lah yau dai Allah ya nuna min kai IMRAN daman ban Sanka ba sai a waya lokacin da ka tafi mama ta ce ina k'arama "ABIDA  da ko ta kula da maganar Abbanta sai ma hankalinta da ta maida kan IMRAN. Haushi da takaicin irin tarbiyar da Ikilima ke baiwa yarinyar ya tsayawa Aliyu  a rai ba ta  jin magana ko kad'an ga rawar kan masifa sai abin da  Ikilima ta ce take yi.

"Haba kai kwa ai bata lura ba, kasan yarinta "Hindatu ta ce tana murmushi

Shi dai Aliyu bai k'ara magana ba.

"Wai ba da ke Abba ke magana ba amma ki kai shiru "IMRAN ya fad'a fuskar nan babu annuri, ganin ta bige mummyn shi kuma Abbansu ya mata magana ta yi biris.

Zunburo baki ta yi irin na sangartattun yara maras sa jin magana ta juya ta shige gida Hindatu na kiranta amma ko juyowa bata yi ba ta shige abin ta. Sallama Hindatu ta musu IMRAN na ta d'aga mata hannu itama haka har sai da ya daina hangen motar sannan ya hak'ura.

   satin ta  guda a kukayasku ta tafi maigatari can ma kwana biyu ta yiwa yaya Nana ta dawo kukayasku duk da zaman ba wani dad'i ya ke mata ba sabo da Umma Kande duk da bata fiya zaman gidan ba, ficewa ta ke wataran kuma ta ce ta tafi Gumel haka take zaune dan dama halin Umma Kande abu ne da aka saba  sai dai ganin iyayenta  da ta ke yi kad'ai ya sa bata damu da hakan ba. Su Umma Kande kwa sun kasa zaune da tsaye ne kawai dan ganin sun samo maganin da zai cika musu burinsu na janyowa Hindatu bak'in jini a wurin Dr koma su rabata  da auren baki d'aya  dan yanzu suna gani wannan ce damar da suka samu tunda ga IMRAN duk abin da suka bashi zai musu dan idan ya tafi su basu da yadda za su je k'asar Chaina. To fa inda gizon ke sak'ar shine sun kasa shawo kan IMRAN dan gaba d'aya ya tubure musu sai ma nuna musu yake abin da suke so su yi ba mai kyau bane, gashi yanzu kwana biyu ya rage su koma k'asar chaina amma kuma har yau bai yarda da musu aikin ba.Umma Kande Gumel d'in ta ke zuwa su sakashi gaba suyi ta lallashi amma a banza tun suna lallashi har suka dawo masa fad'a kamar sa cinyeshi d'anye, har barazanar hana shi komawa suka yi amma ko a jikinsa  sosai suke dana sani  akan turashi k'asar waje dan dama sabo da cikar burinsu amma gashi yazo da gardama da ace ABIDA  ce da babu abin da zai gagareta ta musu domin tun yanzun wannan da take da ta takwas gagararriya ce ta bugawa a jarida.Ranar da Hindatu za ta biyo ta d'aukeshi  su tafi Kano ana gobe jirginsu zai tashi a ranar ne ya yanke shawarar karb'ar magungunan da su ke so ayi amfani da su dan bayaso su yi rabuwar rashin dad'i da mahaifiyarsa  duk da abin kirki ta ke so ya yi mata ba amma zai karb'a dan hannunka baya tab'a  rub'ewa ka yanke ka jefar, kuma duk lalacewar mahaifiyarka sunanta mahaifiya duk da  babu biyayya a yin sab'on  Allah ko kuma cutar da  wani bawa  dan wannan sab'on Allah ne dan kwa wurin boka da Malaman tsubbunsu suka karbo magungunan.

   Umma Kande ta yi sammakon zuwa Gumel dan su jaddada bashi maganin dan jiya har wurin wani malami ta je aka yi aiki akan IMRAN  dan ya amince da buk'atarsu, aikwa tana zuwa ya yarda ya amince haka suka mishi bayanin magungunan  dalla --dalla da wanda zai barbad'a mata  a abinci da  wanda zai  zuba mata a ruwan shayi kar har da wanda zai saka mata a ruwan wanka. Haka suka danka masa cike da farinciki suna sanya mishi albarka. Sallama Umma Kande ta musu ta nufi kukayasku  lokacin da ta zo har Hindatu ta gama shiryawa, direban ya zo d'aukanta Umma Kande har  fadan wasa take mata wai za ta tafi bata mata sallama ba, sosai Umma Kanden ta ke fara, a wacce bata tab'a yi ba tunda Hindatun ta zo garin abin har  mamaki ya basu kai ita Ummi Ishalle ma sai ta ke  zaton ko murnar tafiyar Hindatun ta ke yi. Haka dai ta shiga mota ana mata fatan sauka lafiya  rakiya k'ofar gida har da Umma Kande.Sun iso Gumel suka je daukan IMRAN ya  shirya  suna zuwa aka d'an gaggaisa dan sosai Hindatu ta ga canji a wurin Ikilima  tana ta dariya da musu fatan sauka lafiya, bata san sharrin da suka k'ulla mata ba, shi kwa IMRAN  duk jikinsa ya yi mugun sanyi idan ya kalli mummyn tasa sai ya tab'a ledar magungunan  da take cikin aljihunsa, gaba d'aya ya ji tausayinta ya kamashi gashi dai  ita babu komai a ranta sai alkahiri amma su suna binta da sharri duniya kenan.

YAN UBANCIWhere stories live. Discover now