🅿️1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣Haka dai taron suna ya watse ba tare da sun samu wani abin arzik'i ba, bare ayi zancen biyan bashi..Dan wasu ma barkar naira hamsin ce suke bayarwa. Takaici duk ya ishi Umma Kande dan wasu ma da su na mata sallama kai kawai take gyad'awa ,su yaya Nana ma a ranar suka koma domin ba,a basu fuskar kwana ba, dan daga mai jego har uwar babu wani sakin fuskar da suka nuna musu, sai dai sun karb'e kayan da suka kawo masu uban yawa dan itama Hindatun da nata kayan dan tun da ta kammala secondary school ta ke sana, ar ruwan sanyi zobo,kunun aya da kuma jinger. Mijin yaya Nana ya siya musu wata tsohuwar freezer y'ar hannu sai kankara kwa sana, a suke kuma alhamdulillah suna samu musamman ranar kasuwa. Da dare bayan kowa ya watse sai Umma Kanden kawai da wata y'ar uwarta, lissafi suke su uku ne a d'akin gaba d'aya abin da aka samu bai taka kara ya karya ba. Ran Umma Kande duk ba dad'i ga wata muguwar yunwa da ke addabarta, dan ko abincin da za ta ci babu dan ko tuwon da akayi da garin masarar da Aliyu ya kawo a matsayin abincin dare, gaba d'aya y'an garrinsu sun kwashe dan wasu dashi suka tafi a ledoji. Tsayuwar motar Aliyu suka ji, can sai gashi ya yi sallama ya shigo takaici ya ishi Umma Kande dak'er ta amsa gaisuwarsa dan takaici har tambayarta ya yi ya taro ta ce
"Mun gode Allah"
Leda ya miko yace "Ga wannan ba yawa,"
wani kamshin kuli ne ya ziyarci hancin Umma Kande nan take ta washe baki ganin ledar kusan cike take yasa yawunta tsinkewa da k'ara taso mata da yunwarta, Allah kad'ai ya san illar da cin muguntar da za ta yiwa tsiran nan ."Ikilima d'an zubo min soyen kayan cikin a d'an kwano in tab'a, ki kawo min d'akina"ya ce yana mik'ewa ya musu sallama ya fita daga d'akin.
"Maza kula ki kai masa ki dawo mu ci tsiran nan, dan wallahi ba dan tsiran da ya siyo ba da ba mai bashi naman nan "Umma Kanden ta fad'a tana had'iyar yawu. Jiki a sanyaye Ikilima ta d'auka masa naman ta fita zuwa d'akin nasa dan ta san me zai biyo baya. Umma Kande da sauri ta bud'e ledar da duk kamshin ya cika musu ciki, tana gama bud'ewa aikwa ta kawo wani ashar ta dankara wani rogo ne irin na kasuwa da aka yankawa albasa aka barbad'a kuli -kuli akai. Wani takaici sai da Umma Kande ta ji kamar ta yi kuka, gashi an bashi naman da babu ko kwandalarsa a ciki.Aikwa Ikilima na dawowa sai da Umma Kanden ta yi kamar ta cinyeta d'anya wai dan munafurci ta san rogo ne a ledar amma bata fad'a mata ba.Washe gari kwa haka aka soye uban jikin ragon haka Umma Kande ta raba har dangin mijin ta ba su shima Aliyu ta d'auka masa a cewarta su ba matsiyata bane, amma ni nasan ba haka bane kawai dai dan ba yadda za ta yi na.
*BAYAN SHEKARA BIYAR*
A lokacin IMRAN yana da shekara biyar, a lokacin ne kuma Mama Ikilima ta kuma samun ciki duk da har yau ba ta canja zani ba tsakaninta da Aliyu duk da abin da ya ke mata bai yiwa IMRAN domin yana k'aunar d'an nasa sosai .A lokacin ne kuma Allah ya had'a Hindatu da Dector Ayuba, a lokacin har sun gaji da gorin rashin miji da kuma dariyar k'eta daga wurin Umma Kande, ita dai Ummi Ishalle ko a jikinta dan ta san lokacine bai yi ba ,kullum tana addu, a akan Allah ya sa jinjirin ya zama alkairi.Dector Ayuba iyayen sa y'an asalin k'auyen kukayasku ne. kasuwancine ya mai da iyayensa garin Kano, kuma gidan kakaninsa na mak'otaka da gidan Malam Buba dan gida hud'u ne a tsakaninsu. Tunda iyayen Dector Ayuba suka koma Kano da zama acan ya k'arasa karatunsa na secondary school, dan da a makarantar kwana yake ta maza da ke garin maigatari. Zamansu a Kano ya k'ara hab'aka arzik'in mahaifinsa dan dama gonakai ya siyar ya kama kasuwancinsa, hakan ne ma yasa ya k'aura Kano d''a zama ta sanadin abokinsa da suke harkar kasuwanci tare ya siyi gida ya koma can da iyalansa ya sanya yaronsa d'aya tilo wato Ayuba a makaranta mai kyau da tsada dan ya samu ilimi mai inganci. Bayan ya kammala karatunsa Babansa ya sama mishi admission a kasar chaina. Nan take ya koma can domin yin karatunsa a b'angaren likitanci ,tun da ya tafi sau d'aya ya zo hutu sai dai su iyayen nashi su je su ganshi. A yanzu haka ya kammala karatunsa a Inda manyan asibitoci d''a dama da ake ji da su a kasar chaina suna maraba da shi suna so su d'aukeshi aiki sabo da k'warewarsa.Dan sai da ya yi musu aiki na tsawon shekara biyu, Yanzu kud'in da suka biyashi kad'ai ya isheshi ya k'are rayuwarsa da su. Likita ne na abin da ya shafi k'wak'walwa. Amma dai har yanzu bai yanke shawarar yin aiki da su ba yana so sai ya zo k'asar haihuwarsa wato Nigeria ya yi shawara. Yau kwanansa biyar da dirowa Nigeria shi ne ya je kaiwa kakaninsa ziyara garin kukayasku. A sannan itama Hindatun ta zo gida domin ganin iyayenta, zuwan da sai da ta yi da ta sani sabo da irin gori takura da Umma Kande ta kad'e mata hankali ,ita ba dan komai abin ke damunta ba sai dan Umminta da Baba Malam duk da ta san sun yarda da k'addara amma kuma su ma za su so su aurar da ita dan ba Umma Kanden kad'ai ke mata gori ba hatta y'an k'auyen na su suna yada mata magana akan rashin aure dan yanzu sa,anninta daga mai y'ay'a uku sai masu biyu da wani cikin amma ita har yau duk wanda ta had'u dashi sai ta nemeshi ta rasa kamar wanda aka yiwa wani abun.
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala