🅿️3️⃣6️⃣⏩3️⃣7️⃣
Gatan da FADILA ke samu wannan shine abu na farko da ya sa Umma Kande ,Ikilima da ABIDA suka fara shirin maida y'an ubancin da suke yiwa Hindatu ya koma kan FADILA duba da yadda suke ganin IMRAN na kyautata mat mata, sai Ikilima ke ganin duk wani samunsa akan FADILA ya ke k'arewa. Bata duba da yadda mahaifan yarinyar ne suka masa komai sannan itama Hindatu ce ke d'aukan d'awainiyar SAFWAN dama su kansu su Ikilimar, hakan ya sa Ikilima ke tura ABIDA Kano lokaci zuwa lokaci dan ta ke ganin abin da ke wakana, tana samo rahoto dan su san ta in da za su bullowa al, amarin. Kuma sosai ABIDA kan samo musu labarai akan komai ko dai ta yi lab'e ko kuma idan ta leb'e da FADILA ta ke tambayarta a wayance dan kar ta gane kun san yaro sai ta yi ta fad'a mata duk abin da ta tambayeta. Cikin bin k'wakkwa'afin da ta ke ne ta samo labarin su Hindatun za su je umara ita da FADILA Dr ya biya musu, bayan daman bayan Hindatun ta yaye FADILA ta je wacce ya biya mata a matsayin goron albishir d'in haihuwar FADILA bayan wannan ma zuwanta hajj biyu. Wannan zancen umarar shi ya dagawa musu hankali suna ganin Ikilima bata je ba amma har za,a kai wata kanakanuwar yarinya makka banda asarar kud'i, dan su biyawa Umma Kanden ma da akayi ba burgesu aka yi ba. Haka sukayi ta soki burutsun su da biye biyen malamansu amma Allah ya rubuta zuwan haka suka gaji suka bari.Bayan sun je Umara sun dawo mummy Hindatu ta tafi Dubai, soyayyar kayan lefen d'an lelenta IMRAN daga Dubai ta je Cairo ta k'ara wata siyayyar dama ma kuma a makka ta siyo sarkokin daham dan gwal d'in da ta siyo ba kad'an bane. Haka aka had'a lefe na gani na fad'a haka Hindatu da za ta je kukayasku aka lode akwatunan set biyu ta kai kowa ya gani sannan ta ta wuce da su Gumel ta kai wa Mama Ikilima budar bakinta sai cewa ta yi sai ka ce y'ar gwal wannan uban kayan sunyi yawa, kawai dai na sa IMRAN kashe kud'i dan d'an abin da ya ke dashi ya k'are. A nan Hindatun ta ce ita da Dr ne suka had'a lefen amma dai Ikilima ko ta ce an gode, sai ma cewa da ta yi abar kayan anan dangin Aliyu su gani.A nan aka bar kayan suka kwashi na kwasa, da aka kai kayan sai da Hindatu ta k'ara dan dama akwai ragowa da akwatin suka cika aka ajiye.
An yi taron biki an watse, aka kai amarya gidanta da Dr Ayuba ya baiwa IMRAN, amarya ta tare yarinya y'ar mutunci mai hankali da sanin ya kamata, tabbas IMRAN ya yi dace. FADILA ce ma ta yi ta rigima da ta ke ganin baya kwana a gidan shima kuma baya kwana biyu bai lek'o gidan ba, sannann kuma ya kan kai ta ta yiwa ILHAM weekend itama kuma ILHAM d'in sosai ta ke son FADILA dan yarinyar duk da yar gata ce hakan bai sa an k'i bata tarbiya ba.
BAYAN SHEKARA BIYAR
A lokacin FADILA na da shekaru goma sha biyu, lakacin Hindatun y'ar gidan IMRAN na da shekaru hud'u wacce suke kiranta da (AFNAN) lokacin da aka haifi AFNAN da aka sanya da IMRAN ya sanya mata sunan Hindatu Ikilima kamar ta yi cinyeshi d'anye dan fad'a wai akan me zai sanya sunan Hindatu bai sanya nata ba, itama Hindatu gori babu wanda Ikilima bata mata ba wai ta shanye mata d'a bayan ita kanta Hindatun bata san zai sanya sunan ba sai da ya rada sunan ya sanar mata. Aikwa yarinya ta sha kaya kamar ba gobe.
Wata ranar juma, a ne mummy Hindatu na zaune a falon kasa tana kallo sai ga ABIDA ta yi sallama, amsa mata ta yi cike da nuna jin dad'in zuwanta, duk kuwa da su suna nuna mata basu son ta ita kuma bata tab'a jin bata son su ba ko da kuwa a ranta ne balle a fili. Nan ta sa mai aiki ta kai mata kayanta d'aki sannan aka gabatar mata da aminci da da lemo, anan ta ci ta koshi ta bi lafiyar gado dan mummy Hindatu ta ce ta je ta kwanta ta huta.
Washe gari ya kama weekend dan haka Dr yana gida, idan kwa yana gida to ya kan zauna da iyalansa su yi hira cikin farinciki da kwanciyar hankali. Yau ma hakan ce ta kasance dan itama FADILA ranar bata je gidan Auntie ILHAM ba daman idan ta je ta kan tafi da uniform d'in islamiya daga can a kaita makaranta, domin karfe uku ta ke tafiya islamiya, dan haka yau tana gida. Sun zauna part d'in Dr a falon k'asa suna ta hira FADILA yar gata tana ta shagwab'a abin ta, suna cikin haka ABIDA ta shigo da sallama duk da Hindatun ta yi mamakin ganinta dan basa shiga b'angaren Dr ko gaisuwa ce sai dai in ya shigo part d'in Hindatu su gaishe shi,amma haka ta danne mamakin ta, amsa sallamar ta yi da walwala a inda ABIDA ta zauna a k'asan capet akayi -akayi ta hau kujera amma ta k'i ta zauna a k'asa. Gaishe da Dr ta shiga yi dan dama sun gaisa da mummy Hindatu, sannan ta sa FADILA ma ta je har d'akin da ta sauka ta gaisheta. Nan ABIDA ta ce
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala