YAN UBANCI
NAMAMAN AFARAH
🅿️3️⃣⏩4️⃣K'arasowa Malam Buba ya yi tsakiyar d'akin bakinsa d'auke da addu, a, yana kallon micijin da yake kaiwa tsakiyar d'akin wani irin mugu mugun Sara na ban mamaki, so yake ya fita ya d'akko wani ruwan addu, a a d'akinsa domin zai yi amfani dashi amma kuma zuciyarsa ba ta so ya tafi ya bar Ishalle da macijin a d'akin Dan gudun kar ya sareta domin girman miciji ya wuce misali tabbas zai cutar da ita dan da ganin macijin kasan cewa ba na lafiya bane. Ganin micijin ya tunkaro inda ya ke yasa yake ja da baya domin hatta idon macijin jajawur ya ke kamar garwashin wuta,Malam Buba nan take ya shiga karanta addu, o, i dan tunda yake bai tab'a ganin maciji mai girma da suffa irin tarbiyar wannan babban, dan har wani irin gashi ne a jikinsa fari tass kamar furfura, Kande tana tsaye a jikin labule tana hango Malam ta windon d'akin Ishalle ya wani rabe a jikin bango bakin nan sai motsi ya ke alamar ana janyo addu, a sosai ta ke dariya marar sauti har da hawaye dan dama boka ya fad'a mata cewa miciji Ishalle zata haifa domin ya dad'e da sanya aljannu sun narkar da jinjirin d'a ke cikin Ishallen sun ajiye k'aton maciji.
Malam Buba so ya ke ya d'akko ruwan addu, a a d'akinsa wanda zai yi amfani dashi shi wajen yiwa macijin addu, a amma kuma ba dama, nan take ya shiga k'walawa Kande kira domin ta d'akko ruwan a d'akinsa amma Kanden ta k'yaleshi ga macijin ya gama zuwa dab dance shi neman saransa ya ke, da ya gaji da kiran Kanden sai ya shiga kiran gozomar, gozoma tana wajen zaure a tsaye kamar ka ce kulle ta ce cass dan ma tana tausayin Ishalle sabo da macece mai hak'uri da dattako ga sanin ya kamata amma da wata ce zata haifi maciji da tuni ta tsufa a gidanta. Haka ta zo ta tsaya daga bakin kofa Malam Buba ya fad'a mata ta d'akko masa wata gora a rataye a jikin bango a d'akinsa haka ta d'akko ta zo tana d'ari - d'ari ta mik'a masa ta window.Malam karb'a ya yi ya fara k'ok'arin bud'ewa ,yana gama bud'ewa ya tsiyayo ruwan a hannunsa ya yi bismilla ya watsawa micijin nan take micijin ya yi wani irin k'ara mai ban tsoro, sake tsiyayo ruwan ya yi ya karanta ayatul kursiyyu ya k'ara watsawa micijin sai kawai Malam Buba ya ga idanun macijin sun koma koraye yana wani mirginawa a tsakar d'akin da Malam ya watsa masa a karo na uku sai kawai ya fara hayak'i ya ke zama kamar toka,a take tokar ta ke bin kofar d'aki har sai da ya zamana babu ko d'igon sauranta. Gozoma da ke wajen zaure a tsaye tana ganin ikon Allah bare Kande da take jin kamar ta je ta shak'e Malam Buba domin so ta yi micijin ya kashe Ishalle da Malam d'in in ya so sai ta ci gadon ita kad'ai dan ita bata MA zancen Nana dan har mantawa take da ita Dan bata fiya zaman gidan ba kullum tana mak'ota
mmn afrah 09030283375
YOU ARE READING
YAN UBANCI
ActionLabari ne mai cike da cin amana butulci, abubuwan al,ajabi kaa-kala