1

4.1K 97 2
                                    

    💫MATAN??? Ko MAZAN???💫

            ✍🏻M SHAKUR

        Chapter 1- FEMINISM

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINKAI.

Note: Wannan littafin kagaggen labari ne ba rayuwan wata ko wani narubuta ba, is just fiction danai highlighting major issues dake kawo misunderstanding a aure, I hope we all read and learn.
🙏


EPISODE 1️⃣
Zaune suke akan kujerun dake cikin garden din yahuza suya na bayan central mosque. Maza hudu ne, dukansu suna sanye da suit but duk sun ciccire jacket din sun makala jikin kujerun dasuke kai da alamun  daga wajen aiki suke, gasassun kaji ne agabansu da shayi sunasha suna kallon katon TV dake wajen inda ake buga kwallo tsakanin Manchaster da chealsea.
Kana ganinsu kasan suna bala'in enjoying match din dan sai gardama suke suna dariya kyakyakya.
Wayan daga daga cikinsu ne yay kara hakan yasa yakai hannunshi yataba aljihun gaban riganshi batare daya janye idanunshi dagakan TV ba yaciro wayan yajanye kanshi daga TV yakalli screen din ganin Madam yasa yadanyi tsaki ya ijiye wayan yacigaba da ringing sauran mazan dayake zaune dasu suka kalleshi dan yake yayi yakai hannunshi yana shafa kirjinshi yace "Madam ce wlh ke kirana tahanani sukuni" dauke kansu duka sukai daga kallonshi kaman hada baki suka cigaba da kallon match din abinsu.

Karfe  11:30 daidai aka gama match din inda Manchester sukaci da 4:2, wanda aka kira dazune yatashi yana daukan wayanshi dake ringing har lokacin da jacket nashi duka ya rike a hannu yace "lemme be on my way, inba hakaba Madam zata kashemini batteryn waya wlh, saida safen ku" daya daga cikin ukun dasuka rage zaune shima yamike dasauri yace "nima gani biye dakai Engineer bazan iya da masifan matan nan this night ba tahanani bacci nima" yana maganan yadauki jacket nashi da car key yabi Engineer dasauri zuwa wajen dasukai parking cars dinsu, sake sallama sukayi kowanne ya shige motarshi suka bar wajen.

Daya daga cikin biyun dasuka rage zaune ne yakalli dayan yace "karfe nawa zaka bar nan Nura?" juyawa wanda aka kira da Nura yayi kaman bashi akama magana ba yadaga hannunshi sama yakira daya daga cikin yaran dake aiki a Yahuzan da gudu gayen dayakira yazo cike da girmamawa yace "yallabai gani" juyawa Nuran yayi yakalli mutumin dake kusadashi yace "ya akaro dakai ko zaka wucene kaima?" girgizamai kai yayi alamun a'a hakan yasa Nuran yajuyo yakalli yaron yace "karo mana shayin goruba da kaza asaka masa aciki da gizzard, kasa yaji separately bancin yaji sosai" wucewa yaron yayi yatafi Nura yadauki wayanshi zai fara tabama Musa yace "wai har yanzu kaida Hadiza baku shiryaba? Kai to kasauke girman kanka ka nemeta kuyi sulhu mana" tabe baki Nura yayi yace "wlh ko zan mutu bazan lallashi yarinyar nan ba cus nagaji, any little misunderstanding wanda daga wajetane fa yake farawa amman kullum nike neman sulhu akan wani dalili? She keep taking advantage of rashin son hayaniya na, yo bansan ciwon kaina bane aka gayamata?" Dasauri Musa yace "haba abokina kaima kasan mata da fish brain biyemata zakayi" dasauri Nura yace "bazaka gane bane, duk yanda zan suffanta maka Hadiza bazaka ganeba, she's so bossy, tanada mentality dinnan na feminism, gani take dani da ita daidai muke shoulder to shoulder, she feels irin india kinada kudinki babu shit din da namiji zai kawomiki kidauka, you don't need him for anything, she don't care about me one bit billahillazi kaman ba aurenta nake ba" dafashi Musa yayi yace "chill please kodan yaranku ku shirya haba, Aman is just 4,5yrs ina, little Amal kuma 2 please banson yara tun suna kanana su taso suna ganin iyayensu basa shiri kaji Nura" kabar da hannunshi daga kafadanshi Nura yayi yace "enough Man, talking to Hadiza is impossible, barni nima nabita nazama fish din but saidai ni bazan zama sardine irinta ba mara hankali dake karewa a gwangwani ba, dan trust me mentality feminism nata nan is taking her nowhere, wlh saina gwadamata bonu duk randa takaini bango yar durun uwa" ya kifo uban ashar da hausan shi haba Musa ya kwashe da dariya, dan dariya Nura yayi shima yace "kaikuma meya faru kaima kabiye mini dayin dare awaje yau dan is obvious kaima da naka guntun matsalan kaima" dan tsaki Musa yayi yana tsaida dariyan dayake yace "matata, kaga Maman Shatu I don't even know idan mace ce ita dan at this point cewa nake anya ba namiji bace itaba kuwa" dan dariya Nura yayi daidai lokacin ana kawo musu ordersu yaron ya ijiye yawuce yatafi, tsiyaya musu shayin Musa yayi yadauki kopin yakai baki yadan kurba ya tsaya kaman mai tunani yace "Bro imagine fa duka duka yanzu fa na shiga 45yrs amman this woman na neman maidani tsohon dole, she hates anything tarayya dani, dazaran nazo saita fara ni bansan yakamata yanzu na soma rage kwanciyan aure da itaba nasomas tsufa, menene menene, wai is high time mufara hakura dayi yara sun girma, Shatu is 16 zata shiga university next month let's just focus on yaranmu, I was like what da hell! An gayamata ni katako ne ko sotake da tsufana nafara sopy"? Bushewa da dariya Nura yayi harsaida ya yarda naman bakinshi kasa yana nema ya kware, Musa yace "kadaina dariya is a serious matter ni da kai munada banbanci, kai daman bakin zuciyanka da girman kanka bazai barka kanemi Hadiza ba I don't even know yanda kake surviving wlh, niko bazan iyaba kullum da rokon Allah nake hada matan nan kafin tabari indan taba, da girmana da darajata Maman Shatu ta maidani maibara shine fa jiya tamini karatun Alam Nashara matan nan atafaufau tahanani wai munada budurwa mudaina yi" dariyan da Nura keyi saida yan wasu table suka juyo suna kallonsu dasauri yarage sautin dariyan, kwana nawa kenan kullum cikin kunci yake but yau Musa nabashi dariya sosai wlh he's so funny and hausan shi is just everything, dole ma kai understanding pains nashi sabida kalamomin dayake using to express it, tsagaita dariyan yayi yadauki nama yakai baki yace "to be honest with you Musa bawai banson nasami natsuwa bane ina so sosai but halinta is making me loose interest and love for her, banmason in tuntubeta da neman kwanciyan aure, itakuma ko oho bata damu dani ba, she no send me fa" cike da takaici Musa yace "I don't know yaya brain din mata ke aiki imagine fa sun mana laifi but idan sun taru cikinsu they will belike mijina yamin kaza kaza kaza kaga ana kaimu online ana please hide my ID akai karanka amman baza su taba fadin suga kaza kaza da sukema mazajensu ba bunch of hypocrites, masu fuska biyu kawai, banda gayu da nunama kawayensu suna more mazajensu da aurensu babu abinda suka iya, ita kuma dama nafada mata idan bata chanza ba wlh she is on her own, daleliyar kishiya zanyo mata, da kudina da sana'ata wlh bama saina nemi mata ba Gwaggo zan kira a kano asamomin yarinya yar achan achan atoh ni wlh ban tsufaba garau nake, anma kawomin wasu magungunan basir daga Cotonou bazaka sha ba"? Girgixa kai Nura yayi yace "kaidai da shaye shayen magungunan basir din nan" dariya Musa yayi yace "kaima yakamata kasha wlh ya wanke maka mara tastas, fire for fire wlh ka lallasa Hadiza" "inaaa ni bazan biyemaka ba narasa ina zansa kaina, baridai maybe idan komi ya daidaita nazo na amsa".
Wuraren 1.30AM sukatashi Nura yabiya kudin komi, kowanensu yashiga mota dan tafiya gida, Musa yace "zakazo office kaduba motocin ne gobe sun iso fa" Gyadamai kai Nura yayi yace "inada wani important meeting gobe but zan shigo dazaran nagama" Musa yace "to shikenan nimafa sonake nazo naga site dinnan, terrace dinnan yamin kyau dakukayi" "ba kaki sayaba bakano da son kudi" ckin dariya sosai da barkwanci Musa yace "shikuma bazamfare annubazaranci da kudi, nabiye maka saika karan mini da dan jarin motoci na" dariya dukansu sukai sukai sallama kowa yaja motanshi sukabar wajen.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now