8

1.3K 62 7
                                    

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

         ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 8️⃣
Adan birkice direba ya gangara zuwa gefen hanya yayi parking yin yanda Nura yabuga ihu, Nura yana murmushi sosai kaman wanda yaci lottery yakalli su Musa da duk suke kallonshi asankare irin ikon Allah din nan yace "kufita mana" dasauri Musa yace "ohhh Allah kana gwadamin halin Nura yau kaine haka kake rawan jiki kaman wani sabon shiga? Shekaran ka nawa yanzu kana buga odafere"? Kwashewa da dariya Engineer yayi yace "kai wlh dan iska ne Musa, mekuma Odafere" yakalli Nura yace "dan Allah kayakuri mutafi Nura, mukoma Abuja this one week Musa ya loda maka maganin basir kaga system dinka yayi refreshing afitar da toxins din ciki, sabon ruwa yazo yataru a buhu" dasauri Musa yace "itama bakasan da Gwaggon nata tace abarta abinda za'a mata ba kenan duk dadin kane fa, gyaramaka ita za'ayi fa, kuma ma ai da kunya kawani koma saikace wani saurayi, kawa Allah ka rungumi letter nan yarage maka zafi mutafi kai direba tada mota next week fa karenka zakaci ba babbaka" tada motan direba yayi badan yasoba yahakura cus yasan gaskiya suke fadi, koda suka shiga Abuja gidan engineer yaje yaci abinci yayi knack sukasha hira wuraren 11 yabaro gidan yakama hanya suwa gudanshi yakira Ummi amman wayanta akashe maybe ba chaji baiso yakira wayan Meena kuma around 11:30 yashigo gidan, yana bude kofan falon yasan Ummi bata gidan yau kaman ba falon da Ummi ta gyara dazu da safe ba.

Dakin gabaki daya a hargitse, school uniform din su Aman na nan falon da jakunkunan su da safa, dinning hargitse da plates ga ragowan abinci indomie yagani da egg is as if yaran basuci ba gadai cups na tea da ragowan slice bread da alamun abinda sukaci kenan, kitchen yaleka daganan dinning just indomie da Hadiza ta dafa tajuya kitchen din up side down kaman ba kitchen din daya shiga ya zauna aciki bane harya sha shayi rannan da Ummi ba, ijiyan zuciya yasauke yadawo falo da kanshi ya duka ya tattare kayansu na school sannan yabude baga nasu yaciro books nasu sunada homework ba'ayiba and wlh dudda Ummi is uneducated she manage ta koya musu homework duba ayyukan su nada yayi da Ummi ke tayasu duk sunci to menene ma amfanin auren Mai ilimi tunda bazata iya yima yaranta homework ba, kwasan komi yayi yawuce sama yakai kayan kowa dakinsu yana kallon yaran da ba'a musu wanka ba normal kayane ajikinsu bana bacci ba da Ummi tasaba saka musu, shiru yayi yanzu haka yaran nan zasuyi rayuwa, shi karan kanshi bazai iya kwatanta yanda yakeson yaranshi ba bazai dauki rashin kulan nan ba da rashin basu abincin nan ba ko kin musu homework ko uniform ma sabida yasan sunada wani set dazasu saka gobe ne amman what's all this dakinshi yatashi yatafi yaje yayi wanka.

Da asuba as usual yafito harzai wuce yasauka kasa saikuma yajuyo dan yayadata tama yaran nan abincin school ta shiryasu gaban dakinta yaje tareda bude kofan yashiga ya kunna wutan dakin, bauu dakin yayi haske yatsine fuska Hadiza dake lafiyayyen bacci tayi jin  haske, tadan bude idanunta kadan ganin Nura yasa cikin muryan bacci tace "Nuri am off salat ka tafiyan ka masallaci basaika tasheni ba" yana daga wajen yace "get up fix something for the kids and get them ready for school sannan basuyi home task nasuba, and arrange the house yayi datti gidan" wani kalan ware idanunta Hadiza tayi tasss takalli sama saikuma ta tashi zaune da sauri ta kakkalli gefe da gefenta  dan she wanna be sure cewa bada ita Nuri yake ba ganin bakowa adakin yasa tanuna kanta da sauri tana kallonshi cikeda mamaki tace "Nuri ni kake bama order haka kake lissafo ma ayyuka haka?" Duk yanda taso kasa rike dariyan datakeji tayi tadan kyalkyala dariya tana nuna kanta tace "wait are u mistaking me for Ummi ne or wat dakake lissafo mini abubuwan da zanyi, idanunka gizo suke maka ne Nuri? Nayi kama da yar aikin mu ne? Wait ma kai what happen da u can't do all of this abubuwan nan daka fadi are you not mahaifinsu? Can't u cook for them? Can't you bathe them and get them ready for school? Bazaka iya musu homework nasu ba? Who said shirya yara, basu abinci, getting them ready for school da gyaran gida responsibility mata ne kadai?" Babu wasa kan fuskan Nura yace "ki tabbatar kin tashi kin soma aikin dana fadi kafin nadawo gidan nan daga mosque" yana maganan yajuya yafita daga dakin mamaki yasa  Hadiza tama kasa zama tashi tayi dasauri tasauko daga kan gado tafito daga dakin tabiyoshi abaya tace "Nuri ni kake commanding like that are you for real? Kalleni fa" tanuna kanta tana sanye dawasu arnaye kayan bacci tace "do I look like a house help? Listen fa Nuri lemme tell u something ko Allah yasan ni ba housewife bace, I have a business danake managing, I contacted agency masu kawo yan aiki babu wasu akasa za'a nemo mini, idanma zaka zauna and be attending to this children reschedule work naka do it tunda Ummi tatafi garinsu dankai ur company is big kaine CEO kanada manager dazasu iya managing komi niko banda manager, I manage everything about business dina nikadai banda sales girls danake dashi dake attending to customers namu but I do komi dakaina dan haka Nuri attend to ur kids, babu inda aka rubuta a musulunci cewa dolen dole mama ce zata dingama yara komi yaran nan na me and you get them, gaskiya I don't have that tim....." ganin Nuri yabude kofa yafita yasa Hadiza ta tsaya turus da mamaki, Nuri just walk out on her tanamai magana irin baida lokacin ta wow! Tana kallon kofan kirjinta na tafarfasa, da tayi niyan ko falon ne tadan tattare suyi sharing work din amman wlh tafasa tayaya zaiki girmamata ita ta girmamashi, wani disrespect ne hakan? Wannan sabon confidence din da Nuri yake mata kodan sabida yaga yasaketa tadawo gidan da next day ne yasa yake mata Iskanci haka, ta inama zata fara all this ayyuka Allah ma yasan bazata iyaba wlh, rabon datayi aikin gida harta manta to tariga tawuce wannan level din nayin aiki dakanta agidanta Allah ma yasani, idan tayi aiki agidan mijinta menene banbancin gidan ubanta da gidan mijinta? Kana gidan iyaye ne u must work, abaka umarni kabi, but your husband house suppose to be your paradise that's the beauty of aure, kiyi duk yanda kikaga dama agidanki, kici karenki ba babbaka, tanada kudi mijinta nada kudi maisa zata tsaya da kanta tana all this silly household chores? No Nuri u can't subject to into doing abinda zuciyana baiso yayi, itama shegiyan yarinyar nan akan wani dalili zata sakani in this tight spot, that stupid Ummi datawani tafi shegen kauyensu wai wajen kakanta,  juyowa Hadiza tayi tarike waist nata tabi falon da kallo yanda yayi datti ga kwanukan abinci tsaki da ragowan food a dinning tayi tai ihuuu. "Wayyyooooo, Goddddd! A ina zan sami yar aiki yaune ni Hadiza? Ohhhh I can't do this, how can I start doing this chores haba dan Allah, ai abin kunya ne, niba yar aiki bace ba I can't do this wlh, ni nama manta yaya ake girki ma, indomie nan koni nakasa ci dana dafa jiya ewww, yuck" ta yatsine fuska, komawa sama tayi dakinta tawuce bayi abinta.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now