31

1.3K 67 3
                                    

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣1️⃣
Waiwaye baya kadan!
5:00 daidai jirgin su Hadiza ya sauka a kano, fitowa tayi ahankali gabanta sai faduwa yake da maganan Baba, hakanan ta tare taxi 5k yakaita harchan Dakata dan anan gidan su yake, wani madaidaicin gidane yanada gate haka baki, gidan daidai na rufin asiri, sauka tayi tabiya kudi tajuyo gabanta still na bugawa tabude gate tashiga gidansu, kayan dakinta data fara gani a tsakar gidan yasa kawai taji wani irin chills na sanyi na shiga jikinta kawai ta tsaya chak tana kallon kayan, wani abu taji ya tsaya mata awuya amman ta daure ta danne tadauke idanunta dagakan kayan tafara tafiya compund nasu nada fadi gawata hadaddiyar Camry golden dake pake a compound din, babban flat ne guda daya agidan sai bq tabaya daga labule akayi aka fito Rabi ce rikeda kwano a hannunta ganin Hadiza yasa tace "Anty Hadiza, Mama Anty Hadiza ta iso" ijiye kwanon tayi da gudu tai wajen Hadiza sai kawai ta rungumeta tace "Anty Hadizaaaa" fitowa Hafsa tayi da gudu da babynta ma a hannunta amman ta ijiyeta tazo da gudu sai kawai suka rungumeta, Hadiza jitayi jikinta yamata wani kalan sanyi kafafunta kawai sukahau tankwashewa da kansu daidai Anty Jams da Mama nafitowa daga dakin, kallo daya Mama tamata tace "ku shigo da ita daki" kakkamata sukayi Hadiza takalli Maman nata dake mata kallo irin kallon haushinta takeji sosai din nan tace "kin sami abinda kikeso ai shikenan, ga gidan ubanki nan saiki zauna, ku wuce ku kaita ciki nace" Mama tai maganan with so much annoyance Anty Jams tayi shiru tana kallon Hadizan wacce idanunta kadai zaka kalla ta baka tausayi dan sunyi zuru zuru ta wajigu, wlh dudda tana fushi da Hadizan amman tabata tausayi matuka kaman tamata kuka, wucewa da ita ciki sukayi zama tayi a falon Rabi ta kawo mata ruwa da gudu kadan tasha kawai ta ijiye Mama da ranta ke masifar abace dan ba dadi auren yarka ya mutu wlh babu, balle kuma auren da kasan diyar naka ne at fault sai bakın cikin yazaman maka guda biyu, gana mutuwar aure, gana yar cikin nakane taja, no mother wish for mutuwan auren diyarta.
Sallama akayi wani magidancin mutum Ustaz sosai fa yana sanye da babban kaya da hula akanshi mai rawani yashigo gidan da wani mai kama dashi wanda zaka gane kaninshi ne, shiga falon sukayi Hadiza tasauke kanta kasa dasauri ahankali tace "ina wuni Baba" wucewa Baba yayi ya zauna kaninshi a gefenshi ya zubama Hadiza idanu kana ganinshi kasan yanada dan zafi irin ba mutum mai sanyi bane, babu wani bata lokaci ya nuna tundaga kan Jamila, Mama har zuwa kan Hafsatu yace "dago kanki ki kalli yan uwan ki kinsan mesa dukansu ke gidan nan yau"? Kasa dago kanta Hadiza tayi gabanta na faduwa sosai dan tana shakkan mahaifinta matuka tace "a'a Baba" cikin tsananin fada yace "sabida dukansu harda mahaifiyanki sukasa hannu suka tayaki kashe auren ki! Akanme kina gidan mijinki shekara da shekaru dabi'un banza kike zubawa banda labari?" Yayi maganan da fushi yana daga murya kowa ya sauke kanshi kasa cikinsu yace "akan me? Uhn uhn uhmmm Amadu kwanakin baya da diyar nan tai rashin lafiya cemin akayi rashin lafiya ne kawai, mijinta yace duk suje abujan yaturawa Jamila kudin jirgi sabida ciwon zuciya likitoci sunce tana bukatan yan uwan ta abinda aka gayamini ke nan, anyi haka ko ba'ayi haka ba"? Baba ya tambayi Mama data gyadamai jiki asanyaye, Baba da ranshi ke tafarfasa yace "saida sakon bawan Allahn nan Nura ya shigo wayana yace Baba namaka laifi na mari Hadiza abisa kuskuren fushi dakuma zafin zuciya wanda nai nadaman hakan, ta shigar dani kotu anbi mata hakkinta, Baba kayakuri na saki Hadiza saki nabiyu yau, yoo banmasan sanda akai na dayan ba, amman Mahaifiyarta da Yayarta da kannenta sunsan komi sukai shiru suna kallona saida na sami Maman na titsiyeta take gayamini gashi, gashi, gashi, ai yanzu gatanan tadawo gida kun huta"? Yayi maganan yana kallon Maman Hadiza yana bubbuga kafa akasa yana tafarfasa yana nuna musu Hadiza da hannu. Cikeda tsantsan adama da danasani Maman tace "Malam kayakuri, na amince namaka laifi, amman ka fahimce ni, iyaye maza sunada zafi barinma kai saisa zaka gani yawanci iyaye mata kan boye laifin yaransu daga mahaifan su gudun bacin rai da fushi, sa'an nan na dauka fadan damuke mata dani da Jamila zataji ta dauka basai ka shigo zancen ba, kaga kuma ada bahaka Hadizan takema komawanta jarababben shedanin garin nan ne yasa taje tahadu da shedanun ciki itama ta rikida tazama daya, amman kayakuri Malam, na dauki kuskure na hakan bazata kara faruwa ba, kayakuri Malam" "hakuri bayan kun kaso mata auren?" Baba yayi ihu yana hargowa dayasa Maman Hadiza ta runtse ido cikeda jin dacin maganan shi, Baba yace "Amadu Allah shaidane kaima shaidane yarana nabasu tarbiyan boko da islamiyya, dukkan su nan har ita Hadizan babu wacce batai sauka ba, nabasu tarbiya, sunsan Al,Qur'an, Tajweed, Tafseer, Ahalari, bulugul maram, umdatul Ahkam, zuhudu, fikihu, not to mention others, kai ni nan dakaina saida na zauna na koyar da yaran nan kap dinsu littafin siffofin mar'atul saliha, na killace su nakuma tabbatar da na aura musu mazaje nagari amman mahaifiyar su kullum boye mini zancen yarana take" Maman Hadiza tace "Malam kayakuri" dan shiru Baba yayi saikuma ya kalli Hadiza yace "kalleni ke kuma dan kaniyanki" ahankali Hadiza tadago kanta gabanta nafaduwa dum dum dum sosai takalli Baba, da hannu ya nuna kanshi yace "tunda na haifeki kin taba ganin Mahaifiyarki tamin ihu?" Girgizamai kai Hadiza tayi ahankali, cikin tsananin fada da kumfan baki Baba yace "kintaba ganin ta gasamin magana koko kin taba ganin ta rainamin wayau, ke kin taba ganin Mamanku tace nine zan muku girki yau ko na shiryaku zuwa makaranta koko kintaba ganin ta zauna tace ita tagaji da aikace aikacen gidana yau nine zanyi bani amsa" Baba yabuga hannun kujera, girgizamai kai Hadiza tayi, cikin wani kalan fushi Baba na kallon Hadizan dake girgizamai kai yawani zabura yatashi daga kan kujera kaman zai daketa yace "kin taba ganin mahaifiyarku ta daukowa Gwaggo yan sanda kafin ta rasu"? Tashi Hadiza tayi da gudu tawuce bayan Mama tariketa gam jikinta narawa gani take kaman dukanta zaiyi, akwai wani kalan haiba da kwarjini da mahaifinsu kedashi kodanshi Malami ne oho, amman baki isa ki kalli idanun Baba kiyi hayagaga agabanshi ba, babansu baida wasa ko kadan, sun taso shiba uba mai wasa da yaranshi bane saisa tsoronshi ke jikinsu tun suna yara, tsakaninsu dashi yakoya musu karatu yabasu abinda suke bukata but irin wasan nan kaman yanda Nura keyi dasu Amali ina Baban su baya wannan at all.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now