33

1.3K 52 10
                                    

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

               ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣3️⃣

Duk tafiya akayi yarage daga ita sai Mama afalon dake kallon yanda take kuka, kaman taje ta lallasheta but itama at this point she support Babanta 100 percent, yayi maganin Hadiza, ya gyarata, kuma she trust Baba Hadiza zata ladabtu, kuma zata bada nata gudunmawan ma agayarata, tashi tayi tawuce corridor dakin dake kusada nata tabude daganan tace "taho ki shiga dakinki kiyi wanka ki chanza kayan jikinki kiyi salla" ahankali Hadiza ta tashi ta taho sai kallon fuskan Mama take data hade giran sama da kasa so kawai take Mama ta lallasheta but Mama nosend hatta shige dakin dake da yar katifa yar daidai akasa dawata yar fanka asama babu AC babu POP normal silin ne asama, sai akwatinan kayan ta kakap wanda Nura ya aiko dasu duk suna dakin nan aka ijiye, shiga ciki tayi Mama tasaki labulen ta wuce taje ya debo mata abinci da ruwa da kanta tazo ta kawo dakin, ganinta azaune yasa ta daka mata tsawa. "My friend stand up kije kiyi wanka nace!" Kallon Mama Hadiza tayi saitaga kaman ba Mama dake nan nan da itaba, jiki asake ta tashi taje bayi tai wanka Mama na tsaye akanta ta shirya tai salla tasa taci abincin dole taci kusan rabin tuwon sanan tawuce tafita da plate din tadawo daki ta kwanta tayi shiru tana kallon fankan dake kadawa asama yana kara dake damun brain dinta sai kawai taji hawaye yafito daga idanunta saita tashi ta zauna ta zubama akwatinan ta ido tana kallonsu sai kawai taji hawaye yakara fito mata a fuzar da iska komi da Zeenah tamata na dawo mata fresh yanzu da gaske Nuri is done with her tunda har yana dawo da komi nata gida wani kuka yazo mata tayishi ta gode Allah tai bacci.
3 dot taji ana kiran sunanta. "Khadija Khadijah" Adan firgice tabude idanunta jin muryan Baba yana tsaye gaban dakin batare daya shigo cikiba yace "Khadija" dasauri tace "na'am Baba" strictly yace "dauro alwala kifito falo ina jiranki" ahankali tace "tom" tashi tayi tana tangadin bacci tashiga bandaki ta dauro alwala ta dauko hijabi tafito falo Baba kadai tagani ya tsareta da idanu dasauri tasauke kanta kasa dadduma biyu ya shimfida afalon daya agaba daya abaya yace "hau dadduma muyi qiyamun laili" Gyadama Baba kai tayi yatada salla yafara karanto Al qur'ani kira'an Baba dadi sai kawai Hadiza taji abun ya tsuma mata zuciya, yaune rana na farko dataji aranta lallai fa tabar Allah for a long time cus bazata iya tuna the last time ta karanta Al Qur'ani ba wlh, sai kawai taji hawaye ya gangaro mata feeling fragile, Baba bai wani ja sallan da tsayi ba sabida ita, 5 raka'a sukayi yajuyo ya kalleta anatse ya daga hannu yace "idan bawa na cikin kunci, damuwa da fitinun jarabawa, bawa dan uwansa bazai iya magance masa matsalolinsa ba Khadija, ni ko mahaifiyar ki bazamu iya magance miki duk abinda ke damunki ba Allah kadaine zai magance miki kome kikeji, shine Ubangiji mai tsarki da daukaka, mai kuma mulki, Al Awwalu, Al Akhiru Al Zahiru Al Badin kuma, duk daren duniya Allah kan sauko dakansa ya amsa bukatun bayinsa, dan haka daga hannunki sama ki gayama Allah bukatun ki kakap, sannan ki rokeshi gafara bisa laifuffukan dakikamai, ki rokeshi haske da dacewa akan rayuwa babu abinda yafi karfin Allah, so kaima Allah kukan ki Khadija" Gyadamai Baba kai Hadiza tayi kuka na zuwanmata ta hannunta sama ahankali abin namata kaman ba itaba she can't remember the last time datai salla haka ta roki Allah for anything, she's feeling guilty kan tayi neglecting bautama Allah, sai kawai tafashe da kuka tace "Allah na tuba! Allah na tuba!" Sai kuka hakan yasa ahankali Baba ya juya yayi facing gabanshi, Hadiza tai kuka zuciyanta ya sosu she's feeling kaman ma she don't deserve rahaman Allah cus tamai laifi da dama, da kyar ta iya controlling kukan tafara addu'a  azuciyanta, the first abu daya fito daga zuciyanta is Nura tanson aurenta da Nura tanason ya maidata, tanason mijinta, kawai saita shiga share hawaye, sosai tai addu'a saitaji wani imani da natsuwa na shiganta da tadade bataji ba, anan bacci yayi gaba da ita ta kwanta kan dadduman Baba tajuyo yakalleta yayi shiru idan yace bai damu da damuwa ta ba yayi karya, saisa ya kudirci anniyan zai gyarata yana kuma rokon Allah ya taimakamai yabashi iko dan idan Allah bai nufeta da shirya ba kome zaiyi abanza bazata shiryu ba, addu'oi yacigaba dayı har aka kira asuba sannan yatadata yace "taje tayo alwala tai sallan asuba" shikuma yawuce mosque.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now