22

961 39 6
                                    

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPİSODE 2️⃣2️⃣

Hadiza na zaune kan gado wajejen 8 tana kallo a MacBook dinta da aka kawo mata su Rabi Hafsat da Mama suka shigo dakin suna shigowa wani tsalle sukayi suka rungume Hajiya Hafsat tace "barka Ya Hadiza congratulations" dasauri Hadiza da duk jikinta ke ciwo ta turesu tace "zaku karyani me kuke murna haka" cikeda jin dadi Rabi tabama Hadiza labarin komi dasauri Hadiza takalli Anty Jams tace "wai haka? Shine kikazo jiyan nan kikai shiru"? Dasauri ta kallo Mama tace "Mama da gaske wai yar aikin nan ta gudu Hajiya kuma ta tafi" hade giran sama da kasa Mama tayi tace "nidai tunda kin sami lafiya nima gaskiya tafiya zanyi yau" Rabi tace "Wlh Ya Hadiza da gaske barsu Mama da Anty Jams yan Qalallahu wa Qala Rasulu ne su, but Ummi dai tagudu kuma mijinki ne yamata wulakanci jiya yagayama mamanshi ido da ido bazaije nemanta ba ko bikinto shine Hajiya tai zuciya ya tafi yau" wani ihu Hadiza tayi ta dirko ta rungume su Rabi saita fara rawa da waka. "Jarusalema ikayalami eeeee lonolonse......." Yanda su uku ke rawan daga Mama har Anty Jams tsayawa sukayi suna kallon yan iskan yaran baki abude, Mama tace "stop celebrating other's downfall duniya juyi juyi ce yau turn dinka gobe nawani, life is like a roller coaster Hadiza, Rabi'a da Hafsatu" Hadiza tace "Mama Allah ne ke sakamin wlh ba maganan roller coaster anan karma yakama yarinyar nan cus taci amanata gashinan da kanta da dauki kafanta ta tafi, the God am serving can never shame me, ni wlh namaji na warke tas tas, tas, azo asallameni wayyyooo dadi Nuri na is all mine again, Nuri kabiyani" ta kankame Rabi cike da jin dadi Anty Jams ta tabe baki.
Wajajen 10 Nura ya shigo asibitin da sallama yashiga dakin Hadiza na kwance tana kallonshi tana murmushi cikeda so, dab da gadon yaje yasa hannu yaja hancinta yace "wannan kallon fa" murmushi tayi sosai tace "Mijina yayi kyau ne naga, ina kwana" murmushi yamata yace "close your eyes" dan zaro idanu tayi tace "menene"? Daure fuska yayi hakan yasa tarufe da sauri suma su Rabi duk kallon Nuran suke dumbfounded kofa yakalla yace "come in" Drs da Nurses na asibitin ne suka shigo da katon cake da ballons dayawa a hannunsu an rubuta Happy Birthday Didi akan cake din su Mama da Anty Jams duk murmushi sukayi gabaki daya kowa ya manta yau birthday nata har ita kanta ta manta, yakalli Hadizan yace "open your eyes now" ahankali tabude kawai aka fara waka.
"Happy birthday to you, Happy birthday to you, Happy birthday to Hadiza Happy birthday to you....." fashewa da kuka sosai Hadiza tayi tana kallon Nura kaman ta tsaga jikinshi tashige takeji karban cake din yayi yadaura akan cinyanta yana mata wani kallon soyayya yace "happy birthday Didi, oya blow you candle" blowing candle tayi akahau ihu ana tafi ta yanka cake din red valvet tace "wowww my favorite Thank you Nuri, I love you, thank you all" takalli sauran Drs da Nurses din tamusu godiya duk akacici cake din adakin aka watse Hadiza sai kallon Nura take she can't believe Allah yabata miji dake sonta haka yake kuma son yaransu juyowa yayi suka hada Ido ya harareta yace "you are 33yrs yanzu, no more tsiwa da rashin ji da stubbornness" pledging tayi tace "nadaina I promise" Mama ta tabe baki tace "Allah sa" fuskanta ya shafa yace "bari nadan leka office kinason wani abu" girgixamai kai tayi tace "saika dawo Allah tsaremin kai" lumshe mata ido yayi yace "Ameen"yafice.
Mama tace "kinyi sa'an miji Hadiza saidai kice Alhamdulillah I hope you will change for good wlh kika rasa Nura kin rasa miji har abada" Anty Jams tace "nama Majal magana nabiya kudi nama tura mata number ki zata saki group dinta na matan aure mai suna Somach dan ubanki saura kada ki natsu ki koyi abubuwa you are 33 yanzu Allah ya chanza ki, namiki order wasu kayan mata from MAMMI HAJIA, shedanun cikin magungunan ta namiki order da HQ ADDICTION, RUWAN BAGAJA da OGA MUST SALUT, gobe tace zatamin  delivery tun anan asibiti zaki farasha sabida yabi jikinki" murmushi Hadiza tayi tace "thank you Anty Jams dina don't worry this time I will make you all proud of me, dagajin sunayen magungunan nan zasu tsula tsiya" Anty Jams tace "dole Nura yaga chanji wlh"

****
Yau Hadiza ta cika one week a asibiti yau aka sallamota suka dawo gida yaranta sai murna suke gobe da sassafe yan uwanta zasu koma kano girke girke suka mata daban daban aka lollada a freezer da uban stew kusan cikin roban fenti duk wani aiki dake gidan sun mata dudda babu wani abinda ke damunta ta warke tass though tanata appointed da psychologist daya ga wata mai zuwa but she's fine sai uban kayan mata MAMMI HAJIA take sha.
After Magrib yashigo gidan duka akaci abinci tare yakara yin sallama da yan uwanta yawuce masalları sallan isha'i shida Aman.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now