3

1.4K 54 6
                                    

MATAN??? Ko MAZAN???💫

         ✍🏻M SHAKUR

  EPISODE 3️⃣

BONUS💃
Sosai kirjinta yabuga da sauri ta sauke hannayenta kasa tadaina rawan tasauke kanta kasa shima daga kallonshi gabanta nafaduwa dumdumdum.
Wucewa Nura yayi dasauri sama zuwa dakinshi yakasa daina ganin fuskan Ummi dana yaranshi how happy all of them were, yanda itada Aman kema Amal rawa, bayi yafada dasauri ya watso ruwa yafito yashiga shiryawa dan yafita meeting din dayake dashi is by 2, cream yadauka zai shafa saikuma ya tsaya maisa ya kalleta haka smiling ya tambayi kanshi? He was lost dayana kallonta, yar aikinsu ce fa but he was finding all abubuwan datakeyima yaranshi super cute, dan ijiyan zuciya yasauke saikuma yacigaba da shafaman.

Ummi daduk takasa natsuwa itama a kitchen ta tambayi kanta maisa yake kallonta, tun yaushe Alhaji yaganota tana rawa haka? Duk wani kalan kunya kunya da nauyi nauyi taji tanaji, IPad din Aman tadauko ta kunnamusu anan kitchen din dan bazata rabu dasu ba tashiga gyaran gidan duka tanaso tana gamawa tamusu wanka, itama taje tayi saita daura abincin dare.

Shiryawa yashigayi cikin suit dan dawasu representative na China company zai hadu dasu yanaso yabasu contract nayin titin cikin estate  dayakeyi, yana cikin daura agogo wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Sis yasa yakai hannunshi ya danna call din batare daya daga wayanba yacigaba da saka agogo daga ta dayan bangaren akace "Ya Nura ina yini" "how are you Aminatu ya jikin Hajiya kunje asibitin"? Kasa magana tayi sai bakinta yahau rawa, dasauri yasa hannunshi yadauki wayan gabanshi ya mugun fadi yakai wayan kunnenshi dasauri yace "what happen jikin Hajiya ne meya faru?" Cikin kuka tace "dazun nan tafadi abayi yanzu haka muna asibiti" bugawa kirjinshi yahauyi sosai anatse yace "Dr Tanimu ne ke ganinku"? Dasauri tace "eh shine" dan ijiyan zuciya yasauke yace "daina kuka ya isa babu abinda zai sami Hajiya kinji" kaman yana gabanta gyadamai kai tayi, cikin dan taushin murya yace "is okay, zanyi magana da Tanimu I think zan muku booking flight gobe kutaho nan Abuja taje babban asibiti anan don't cry again hankalinta zai tashi, akwai kudi awajenki"? Dasauri tace "eh akwai" ahankali yace "to stop crying bari nai magana da Dr Tanimu" nan da nan ya katse wayan yakira Dr sunyi magana da dadewa sannan ya katse wayan dakanshi yamusu booking first flight na gobe da safe sannan yasake kiran sister nashi yace zasu biyo jirgin safe gobe suzo koya ake ciki tadinga gayamai yatashi ya idasa shiryawa duk mood nashi ya chanza sannan yafito anan falo yaga Aman da Amal suna kallon cartoon a iPad nasu duk an musu wanka sunyi kyau gwanin ban sha'awa kaman ya debesu yafita dasu Amal kaman ba itane mara lafiya ba karasawa yayi inda suke ya duka yamusu peck agoshi yace "Dady zaitafi aiki" dasauri Aman yace "Dady zan bika office" shiru yayi kaman mai tunani yana shafa kansu yace "shikenan zanje daku amman sai ranan Saturday jibi kaga gobe akwai school yau bakuje ba dukanku" Dasauri Aman yace "hadda Anty Ummi zamu itama taje taga Daddy's bigggggg office" ya ware hannunshi biyu yana nuna how big office na babban shi is, dan murmushi yayi yana kallon Aman din kafin ahankali yace "yes Son hadda Anty Ummi" dasauri Aman yace "love you Dady u the best Dad ko Amali? Dadyn mu is the best" dasauri Amal yace "yeeeessssss Dady is the best" murmushi yayi yace "my princess and my Aman are the best nima" harzai tashi yace "ina take?" Aman yace "Anty Ummi"? Gyadamai kai yayi dasauri yace "itama taje tai wanka adakinta" jinjina kai yayi yamike yace "to natafi bye" bye sukamai yawuce yafice.

Wani babban shago ne girmanshi zaiyi wani super market din sama da kasa ne, kasan abayoyi ne irin na yan millions din nan designers dan babu abayan yan 100 ashagon saikuma sama asalin designers bags da shoes ne latest collection ma kuwa, zaune take cikin wani office dake nan sama babban office ne na gaske dawasu mata guda biyu suna hira, daya daga cikin matan biyu ne tadaura tissue kan idanunta tana kuka Hadiza taje tsaki tace "kodai nazo nai magana da mijin nan naki ne Baraka"? Dasauri Baraka tazare tissue dagakan idanunta takalli Hadiza idanunta sunyi jazur tace "so kike ya koreni? Not everyone is as lucky as u are kinada miji kaman Nura mai hakuri da share magana, idan nama Ubale abinda kikema Nura saiya lakadamin duka halan saiya korani gida" wacce ke kusa da itane ta tureta tace "dallachan ai gashinan saisa sai gallaza miki azaba yake waya cemiki anama maza good girl yanzu??" Dasauri Hadiza tace "ahh tohh tell her ooo my dear, tell her Zee cus good girl no dey pay again, kima miji good girl ya tattakaki yayi using naki do dambu yaje ya watsar a shadda, ai yanzu zaman Auren fire for fire ake yana baki kada kibari yakai kasa give him back gbasgbos kawai saikaga yasha jinin jikinshi yasan keba kanwar lasa bace, kinga Nura ko giyan wake yasha yasan bai isa ya tunkareni da nonsense nashi ba cus bana ma dauka ne kuma gashinan nasama ma kaina lafiya I do duk abinda naga dama duk abinda raina yaso agidana to waima tsaya idan nai aure banyi whatever naga dama agidana ba yo menene fa'idan auren? Menene banbancin gidan mijina da gidan iyayena? Abeg ke waye Ubale yana cemiki kule kicemai chass wlh zakiga kun zauna lafiya" dasauri Zee tace "Allah yasa ta dauka, itane kullum yamata ihu kaman ubanta, fita saiyaga dama yake barinta, yahanata business ya kulleta agida kullum ciki yake duramata won't you speak up kinuna mishi kefa duk lokacin dakikaga dama fita zakiyi ki kwatarma kanki yancinki, ki nunamai kedashi are equal sabida yana namiji baya nufin zai dinga juyaki, munafa zamanin feminism ke duk inda namiji yau yataka aduniya kema zaki iya takawa to akanme zaki maida kanki slave dinsa? Jibemu kawayenki yanda muke more rayuwa muncigaba ke kinachan kina bautama mijin dake hanaki fita sana'a, yakuma miki ihu" tissue takara dauka dan maganganun su nasata jin badadi datasan hakane da da Zee tazo daukanta batabita ba, tace "nidai kubarni duk randa nazo wajenku saikun sani ina feeling bad inajin kaina kaman banda sa'a aduniya, kaman I'm the unlucky one, Ubale na sona ina sonshi kuma ya isa yace nayi nayi karnayi karnayi ya is......." Mtswwwww Hadiza taja tsaki dayasa Baraka tai shiru takalleta Hadiza tace "takuraki dai baya bari kiyi yanda kikaga dama, imagine yaranki uku har yanzu kece ke komi agidanki, girki, kula da yara uku fa da sauransu ke jakace Baraka? In nice ai sai na mutu, Idan yana sonki bazai sama miki yar aiki ba haba akan mene zaki dinga shiga kitchen kina girki awan nan zamanin da masu kudi ke hiring intercontinental chef yana musu girki agida that's my next plan ma ni nadauko professional Chef daman na share zancen ne bayan na sami wannan current yar aikin nawa Ummi but still zan dauko" dan murmushi Baraka tayi tace "Allah baki sa'a, kowa nada abinda works for him, ninaji naga kuma zan iyane ne, mubar maganan please kona tashi nayi tafiya ta gida daman Zee takawoni, I don't have to be like you ladies, tundadai ba dukana ko wahalar dani mijina keyiba ko neman mata Alhamdulillah" dasauri Hadiza tace "to abar maganan amman wlh sabida kawai ke kawarmuce duk tare muka taso da tuni mun rabu dake danni banga dalilin dazaisa kene ke duka aikin gidanki ba mijinki na miki ihu kaman wata jak......." Karan da wayanta yayi yasa takasa karasa maganan takalli screen din ganin Nuri yasa tai murmushi sosai tajuyo da wayan tace "kun gani" tanuna musu screen din wayanta tace "tsakanina dashi kar tasan kar ne amman jibi yanda yake bibiyana maza fa saida hash treatment kana musu taurinkai ki nuna musu ke fire for fire ce cus sun iya raina mace kai mai sanyi irinsu Baraka" Zee tace "kwarai kuwa Aminiyata".

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now