19

1.3K 43 25
                                    

💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

           ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣9️⃣
Ihun da Nura yayi saida yatada kowa na gidan.
Azabure Ummi tabude ido ta tashi zaune da sauri tashiga waige waige ganin Nura baya dakin, jin ihunshi for the second time yasa dawani kalan sauri ta diro daga gadon dan tasan ba lafiya ta nemi hijabinta har kasa tasaka dan ba kaya ajikinta tafito da sauri daidai Nura nafitowa daga dakin Hadiza da jallabiyanshi ajike dauke da Hadiza da kayan bacci ne kawai ajikinta komi na jikinta diddiga yake da ruwa a sheme hannuwanta na lilo daidai lokacin Meena itama na haurowa saman Aman da Amal duk sun bude kofa sun fito, mugun faduwa gaban Ummi yayi daga ita har Meena atare sukace "meya faru"? Nura baimabi takansu ba yashiga sauka kasa Amal tafashe da kuka cikin magagin bacci tana sosa ido dasauri Ummi ta dauketa tana kama hannun Aman dayace "what happen to Mom"? Bata iya bashi amsa ba takamashi sukai kasa da Hajiya Nura yaci karo dake tsaye gaban bene ganin Hadiza a hannun Nura kaman jaririn da aka haifo daga ciki yasa tace "Subhanallahi meke faruwa"? Arude Nura yace "Hajiya bansaniba abayi na sameta ahaka, dubamin ita Hajiya bata numfashi, Hajiya dubamin ita" dukawa Nura yayi rikeda Hadiza awajen dasauri Hajiya ta duka takai yatsanta kasan hancin Hadiza but shiru, saikuma dasauri tasaka karamin yatsanta cikin kunnenta takai babban yatsanta wajen sajenta tayi shiru saikuma tacire dasauri takai hannunta damanta idanunta tabude duk Nura nabin mamanshi da kallo dan Hajiya ita kewa mata dasuka rasu wanka a unguwansu akano.
Ganin yanayin idanunta yasa Hajiya tace "Innalillahi Wa Innailaihi Raji'un!" Dawani kalan sauri Nura daya gama rudewa yace "noooooo! Hadiza this is not our promise Hadiza, Hadiza" dasauri Ummi tajuya dasu Aman da Amal dake kuka sukai sama baikamata yara na ganin irin wannan abunba, Meena ta taushe bakinta jikinta na rawa, hannunshi Nura yakai yana bubbuga kuncinta yace "Hadiza wake up, wake up don't do this to me Hadiza, don't do this to me!" Yayi ihu yana jijjigata ajikinshi yace "tayaya kikeso na raini Aman and Amal ni kadai on my own without you? Don't betray me this way, I want to spend all my life dake Hadiza kitashi ban yarda ba, wake up"  ya dinga jijjigata kaman zai karya mata wuya dasauri Hajiya takama hannunshi tareda girgizamai kai tace "Nura!" Ihu yayi yace "Hajiya nooooo, tasan alkawarin mu, she can't leave me so soon, a........asibiti..." kaman wanda yatuna wani abu tashi yayi da sauri ya dauketa yafice da ita bayan yadauki key anan tray dasuke ijiye keys, bude bayan mota yayi yasata yashiga gaba yaja motan da mugun gudu bini bini yana tuki yana kallonta da kyar cikin ikon Allah yakai asibitin su babban private clinic ne.
Yana parking yawani fito ya fanfala da gudu cikin hospital din. "Doctor help me" yayi wani ihu dayasa some few nurses da Doctors suka fito, ganin Alhaji Nura dan nanne hospital nasu yasa duk sukayi wajenshi yama kasa magana waje kawai yake nuna musu yace "my.....my" sai kawai yayi waje da sauri Doctors suka bishi daya daga cikin likitocin yana sa Nurses afito da gado suna zuwa wajen motan kaman Nura zai fashe da kuka yace "she's not breathing namata CPR still batai responding ba" dasauri Dr yashiga saka stethoscope yace "minti nawa kenan yanzu da daina nunfashinta"? Cikin mugun damuwa Nura yace "I don't know I just met her abayi haka, Dr please do something please, I don't care do whatever u have to do, she can't go like this, tanada yara biyu yan kanana, please karufamin asiri and do something" daukan Hadiza akayi aka daura agado idan kaga yanda ake gudu da ita akan gadon idan kanada hawan jini zai iya tashi Nura zai bisu cikin dakin aka hanashi aka rufo kofa, tadan karamin window  kofan yake lekawa ganin ansa almakashi ana yaga rigan jikinta ana mammakala mata wasu mashina akirji gabaki daya doctors biyu da nurses hudu sun haukace ana hada defibrillator dan ayi shocking zuciyanta, hade hannu Nura yayi yakai yashafa kanshi yana juyi saikuma yasake hada hannayen duka hankalinshi atashe yace "Ya Allah karka dauki ran Hadiza yanzu please Ya Allah, nayi alkawari zanyi azumi uku kadawo min da ita, I need to tell her how much she means to me, nagayamata ina sonta haryau har gobe, and I never intend on hurting her in anyway, Hadiza is my soulmate, Maman yarana guda biyu, my life partner, Ya Allah nasan tayi kuskure da dama but please give her a second chance please give her a second chance to amend all her mistakes ya Allah ka taimakamin" wayanshi ne yashiga ringing hakan yasa ya tattaba Aljihunshi yaciro ganin Ummi ne yasa arude yadauki wayan yakai kunne cikeda tashin hankali yace "Ummi" cikeda damuwa Ummi tace "Ya jikin Anty naga ayanda kafita saisa nakira naji ko kunkai lpy, su Amal nata kuka meya sami, Mommy su bansan mezan gayamusu ba" arude Nura yace "Ummi kutaya Hadiza addu'a ki gayama su Aman suma Maman su addu'a, Ummi banson Hadiza tamutu, she means a lot to me, Maman yarana, nariga nafaro rayuwana da ita, tayaya zan cigaba da rayuwa babu ita eh Ummi?" Yanda Nura ke magana zakasan bemasan meyake fadiba cikeda so dakuma tausayin mijinta tace "in sha Allah babu abinda zai sami Anty kaji Baban Amali, Allah ubangiji yatada kafadanta, ka koma wajensu kada anemeka, kada kadamu zan kula da kowa na gida kaji Mijina" cikeda so yace "nagode Ummi ki tayani bawa Hajiya kulawa kar jininta yahau" gyadamai kai tayi tace "to Mijina zanyi, ka manta damu anan ka maida hankalinka wajen Anty tafi bukatarka, Allah yabawa Anty Lpy" ta katse wayan, komawa gaban kofan yayi daidai ana bude kofan Dr daya yafito dasauri Nura yace "doc....." anatse Doctor yace "she's alive!".

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now