4

1.4K 46 4
                                    

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

       ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 4️⃣
Wuraren 7:30 Hadiza tashigo gidan gabaki daya ranta amugun bace yake, Aman da Amal sai Ummi ne afalo dukansu ukun suna zaune kan dogon kujera suna kallon videos letters sound for Amal dudda Ummi bawani boko tayiba iya kanta JS3 but ta iya all this basic things na school shima sound din dan bata iyabane zamanin su da ABCD sukai karatu ba da sounds ba saisa suke koya tanan youtube yanda Amal ke koya itama haka take koya dan sabida koya musu, jin an bude kofa kai tsaye ba sallama yasa suka jujjuyo dukansu hada idanu Ummi tayi da Hadiza dake mata wani kalan kallo dayasa dasauri tamike tsaye daga kan kujeran ta duka kasa danta gane kallon me take mata cike da girmamawa tace "barka da dawowa Anty, ina yini" Hadiza da dama ta shigo da mugun bacin rai dan tun kiran da Nura yamata ashago ranta yake abace tace "ke ban gayamiki koda wasa kada duwawunki yazauna akan kujerun gidana ba, ke kinada darajan dazaki zauna inda nake zama ne yar aiki dake, ubanwa yagaya miki yan aiki nada matsayin zama akujerun gida" Ummi da kanta ke kasa ahankali tace "kiyakuri Anty mancewa nayi Amal muke koyama karatu" baki Hadiza tabude zatai magana daga Aman da Amal da duk suka tashi suna kallon Maman nasu Aman yace "stop shouting at Anty Ummi Mommy" dasauri takalli yaron ta ballamai harara, turo baki Aman yayi yace "u are always fighting and screaming Mommy our school teacher tace anger causes sickness" hararanshi Hadiza tayi bata tace "nakusan fasa bakin nan naka mara kunya kawai" turo baki yayi dan haushin Mommy shi yakeji sosai sabida yanda koda yaushe fada takema Anty Ummi su, bata sake cewa komiba tun maganan Aman tacire heels din dake kafanta awajen tawuce dinning straight taja kujera ta zauna tana sauke jakanta kan table din tace "idan kinga dama kizo kibani abinci" tashi Ummi tayi da sauri ta taho dinning din Aman kuma yakoma kan kujera yayi zamanshi yadauki IPad itakuma Amal tayi hanyar dinning din cikeda shagwaba tace "Mummy babuuuu, ki goyani zanyi bacci" cikeda masifa Hadiza ta nunata da yatsa tunkafin takarasa dinning din tace "don't even come here wuce kitafi wajen Aman kiyi karatu yanzun nan nadawo zaku fara damuna, goyon kaniyanki zan miki, jeki jira yar aikinku tazo tagoyaki, Oya go back" juyawa Amal tayi tafashe da kuka dasauri Ummi takalleta kaman tadaina serving Maman taje ta dauketa, ta tsani taga yaran na kuka wlh har cikin ranta, ahankali tawuce wajen Aman tafada jikinshi rungumeta yayi yace "stop crying Amali Anty Ummi is coming yanzun nan kinji" Gyadamata kai tayi yana share mata fuska yace "let's play game".

Tunda Ummi tafara serving tuwo a plate Hadiza ke kallonta zuciyanta na wani kalan tafarfasa kawo tray gabanta Ummi tayi ta ijiye bata idasa jaye hannunta ba Hadiza ta daga tray gabaki daya ta mike tsaye ta kwarama Ummi akai da tuwon dake a leda da miyan taushen da kwanukan da cokulan duka suka bare akanta wani kalan mahaukacin azababben mugun ihu Ummi ta kwala tafashe da kuka dayasa su Aman suka firgita dukansu suka juyo ganin Anty Ummi ta tsugunna a dinning ga miya tundaga saman dan kwalin kanta har goshinta da idanunta ta kullen gam tana ihu sosai jikinta nawani kalan rawa kaman wace ta zare tsabagen azaban zafin datakeji na miyan dakuma yajin miyan a idanunta yasa suka taho wajen da gudu Aman yace "Anty Ummi" cikeda masifa Hadiza tanunata da hannu tace "kina gidana, kinacin abinci na, nabaki makwanci, nabaki kayan sawa, nabaki sabulun wanka dana wanki, sannan ina biyanki kizo bazakimin biyayya ba, sau nawa ina gayamiki ni bancin tuwo sau nawa nake gayamiki? So kike nayi kiba nai katon ciki? Zanje sama nai wanka ki tabbata kin dafamin wani abun kin kawomin dakina kafin nagama wanka inba hakaba wlh saina koraki daga gidan nan this night" ta dauki jakanta tawuce sama fuuuuu, tsugunnawa daga Aman har Amal sukayi agaban Ummi da jikinta har bari yake sabida zafin miyan dan bata dade da gama miyanba ta juye a kulan gidan ga kulan su irin na millions din nan ne masu rike zafi kaman me, dudda Aman yaro ne amman saida yakai hannunshi yacire tuwon daga jikinta yana kuka sosai ya yar akasa yace "Anty Ummi sorry stop crying" Amal tace "Mommy is badddd mommy" sosai Ummi ke kokarin tabude idanunta takasa sai kuka take dudda kukan take na tausayin kanta tariga tai alkawari komenene zatai hakuri tana bukatan albashinta dashi Gwaggo ke zuwa asibiti dakuma shi ake tara kudin auren kanninta, dole ta jure komi itane hanyan cin abincin gidansu, so take ta mike but tama kasa hannunta Aman yakama Amal ma takama dayan yace "let's go Anty Ummi ki wanke fuskanki" gydamusu kai tayi tana tsayar da kukan datake ta yunkura zata tashi tama kasa saita kara fashewa da kuka daidai lokacin an bude kofa da sauri su Aman suka juyo ganin Baban su shima ya shigo ya tsaya chak yana kallon daga yaranshi har Ummi dake kuka sosai kaman anyi mutuwa agidan ga jikin Ummi duk miya, fuskanta ma haka takasa bude idanu yasa yayi wajensu dasauri baima cire takalmi ba yace "Subhanallahi meya faru faduwa kikayi Ummi" Tsayar da kukan tayi dasauri muryanta na rawan sheshekan kuka tace "eh" tana yunkurawa zata tashi dasauri Aman yace "is Mommy Dady, ita ta kwara mata the whole tray na abinci akai Anty Ummi has been crying" warware handky daya ciro Nura yayi daga aljihunshi baiyi wata wata ba yakai kan fuskanta cikeda damuwa ahankali yace "tsaya" batai musu ba tsayawa tayi kwashe miyan kan idanunwanta yayi tass, miyan yayi fasha fasha awajen harda gashin idanunta, sannan ya kwashe na goshinta dana kumata batare daya taba na wuyanta ba dudda baka ce but he could see yanda fatan fuskan yayi ja, ijiye handky yayi dasauri kafin ahankali yakai hannuwanshi duka biyun yakama kafadanta dagashi har ita atare duka sukaji wani iri dasauri tayi kokari fizge kanta strictly yace "stop banson gardama, tashi muje" yanda yayi maganan ba wasa hakan yasa bata kara gardama ba, yana rikeda ita haka yayi kitchen da ita su Aman suka bisu bude kofan kitchen din yayi zuwa nan backyard gaban wani tap dasuke dashi awajen, yabude tap din yajuyo yakalli Aman yace "je bayin Anty Ummi kadauko mini sabulun wankanta" "okay Dady" Aman ya amsa yajuya da gudu shikuma yabude tap din yace "tsugunna" ahankali Ummi ta tsugunna, gently yadinga tara ruwan da hannunshi yana watsa mata a fuska har saida miyan ya fiffita duka da wayanda sukenan asaman gashin idanunta daidai Aman yakawo sabulan, ga mamakinshi sabulun vivo yagani ahankali ya karbe yakama hannunta yasa sabulun aciki yace "wanke fuskan mugani da sabulu" shafa sabulun tayi ta dirdirje da kanshi yake zuba mata ruwa tana wankewa tass ta wanke fuskan, igiyan wajen ya kalla ganin wata singlet dinshi wanda yasan itane ta wanke yajawo yabata yace "share fuskanki saiki bude idanun nagani"

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now