26

1.3K 60 21
                                    

💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

        ✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣6️⃣
Note: Ni ba lawyer bace! Though I consulted some lawyers irin su Majal and co😍 Incase kunga mistakes no mind me, I be health personnel ejor❤️

Shiga cikin court room din sukayi hada ido yayi da Hadiza dataci gayu yanda kasan zataje gasan kyau tana sanye dawani vilisco embellish atampa maroon ta kafa daure tayi kyau gefenta kuma Zeenah ne zaune itama ta kallo Nuran, dauke kai yayi daga kallonta yawuce yazauna kusa da lawyer shi while Alhaji Musa yazauna a daya daga cikin kujeran dake row din bayansu, Hadiza itama tashi tayi tawuce tazauna kusa da lawyer ta wata attajiran mata ne haka taci glass Mrs Oyenyi Chichi Ebenezar, daidai nan Alkali ya shigo aka tashi akai introducing case din sannan aka kira Nura kanta yafito ya tsaya yayi rantsuwa Mrs Oyenyi ta mike taje gaban Nura ta tsaya tace "Mr Nura kaida Hadiza has been married for 10yrs 9month correct?" Anatse Nura yace "yes" anatse matan tace "describe relationship dinta dakai a tsawon shekarun" dan shiru Nura yayi saikuma ya kalli Hadiza dake kallonshi kyur, Mrs Oyenyi tajuya takalli abinda yake kallo tace "are you trying to blackmail my client Nura"? Dauke idanunshi yayi yace "no" Mrs Oyenyi tace "to bama kotu amsan tambayan da na maka" ahankali Nura yace "relationship dina da ita is just like relationship din any other couples, we live, we share good moments and we have arguments just like every other couples do" Mrs Oyenyi tace "babu any history of abuse ko molestation" Dasauri Lawyer Nura yace "objection my lord, mesa take sa magana abakin client dina is just kaman tariga tai concluding cewa client dina is an abuser" Alkali yace "objection overrule cigaba" Mrs Oyenyi tai murmushi tana kallon Nura tace "ina jinka Nura" Dan shiru Nura yayi sai chan yace "bantaba molesting Hadiza ba or abuse her banda ji......." Mrs Oyenyi tai blocking nashi tace "matanka tace kasha molesting nata not once or twice ko bataso tai wani abu dakai kanayi" dafe kanshi Alhaji Musa yayi cikeda rashin jin dadi, dasauri Hadiza ta waiga ta kalli Zeenah cikin whispering tace "bancema Mrs Oyenyi yana molesting dina ba what is she saying?" Cikin whispering Zeenah tace "ni nace takara dashi sabida yaji ajikinsa ai kin gayamin abinda yamiki kenan daya auro Ummi" cikeda rashin jin dadi Hadiza zatai magana Alkali yace "silent" akai shiru, Mrs Oyenyi tajuya tadawo gaban bencinta tadauki wani file ta taho ta bayar tace "mai girma mai shari'a Nura yasha yima client dina fin karfi, ihu, harma yakai yana dukanta yanzu, cikin file din nan na dauke da evidence na farko hoton fuskan Cleint dina ne Hadiza da fuskanta dazaka ga yatsu biyar na Nura sunyi jazur a fuskanta wanda har yakaita ga asibiti aka dubata takarbi pain killers, sannan auren Nura yazama babban damuwa ga client dina bata da kwanciyan hankali da peace of mind agidanshi haryakai ga just about a weeek ago tana asibiti for case na heart sabida damuwan shi duk evidence na medical history nata is there, ina mai rokon kotu ta bima Hadiza hakkinta duba da irin fighting datayı for her life a hospital for the past two weeks duka duka yaushe akai discharging nata amman harya mata kalan wannan marin what if marin yayi leading nata takara samin cardiac arrest bayan yasan clearly an fadi a asibiti bazata kara surviving ba??"
Tashi lawyer Nura yayi zaiyi magana da sauri Nura yadagamai hannu alamun baiso yayi magana yazo dashi nan ne dan kawai yamai arranging bail da sauran formalities, ahankali Nura ya kalli Alkalin dake kallonshi ganin yahana lawyer magana yace "Yallabai I am guilty!" Dasauri daga Lawyer shi har Alhaji Musa har ita Hadizan suka kalli Nura dan bata taba tunanin Nura ko lawyer shi bazasuyi gardama ba, dan shiru Nura yayi chan yace "I let my emotions get the best of me, and I sincerely apologize for that" ahankali yadaga kanshi yakalli Hadiza yace "Hadiza am sorry for slapping you and for all d pains dakikace nai causing miki" Nura zai magana Lawyer shi yatashi da sauri yace "Mai girma mai shari'a client dina ya yarda yayi laifi kuma yabada hakuri muna pleading for mercy to pay fine na domestic violence din da duka charges dinma" dan hamdala Hadiza tayi tana karkada cinyoyinta dan feets nata are so cold batason akai Nuran ta gidan yari she's just hoping ayarda ya biya fine din.
Tass Alkali yagama rubuce rubucen shi kafin yadago yace "kotu ta yaba da yanda Nura bai bawa kotu wahala ba, ya karbi laifin shi sannan yabada hakuri, duba da baida wani bad record kotu ta yanke hukuncin rike Nura harsai yabiya fine na naira dubu dari uku, 300,000!" Dasauri Alhaji Musa yace "Alhamdulillah"  Alkali yace "idan akwai wanda keda wani magana cikin parties din zasu iyayi" hannu Nura yadaga hakan yasa Alkali yace "ina jinka" tashi Nura yayi ya kalli Alkali anatse yace "inason kotu ta shaida ni Nura na saki matata Hadiza SAKI DAYA!" Wani kalan dum! Dummmm! Hadiza taji azuciyanta yayi dawani kalan sauri tadaga kanta takalli Nura hannunta na rawa rawa, Nura na kallon Alkali yace "inason kotun nan tazama shamaki tsakanina da ita, kada Hadiza tasake daga kafa ta taka gidana! Duka wani abu nata na cikin gidana daidai da cokali zan tattara nasa a mota yau ba gobe ba na aika gidan iyayenta inda na aurota, sannan kada ta daukan mini yarana! Alkali inaso kamin katanga da ita!" Hawaye Hadiza taji zasu zubo daga idanunta tarikesu gam tana fuzgar da iska da baki kirjinta kaman ana barza masara dasauri Zeenah tazo ta bayanta tana mata whispering "kada ki kuskura ki nuna kinji wani abu dan dadi zaiji, abinda yakeso yagani kenan" daurewa Hadiza tayi ta rike hawayen Alkali yagama rubuce rubuce yace "you can sit" yakalli Hadiza yace "kaman yanda kikaji mijinki ya sakeki kuma yamiki shamaki da gida wanda yake nashi, dan haka kada ki kara sa kafa agidan shi kikai haka zai iya daukaka kara akanki, zancen yara kuma dake da shi zaku iya daukaka kara kuyi case na custody yara" cikeda karfin hali Hadiza tace "no need yara nawa ne ko suna hannunshi ko suna hannun uban idan inason ganinsu zan kirashi shiya kawominsu, kuma dama koda bai sakeni ba ni zancemai ya sakeni, me akeyi da namiji mai dukan mata" wani dadi Zeenah taji hardama Hadiza tafi kasa kasa Alkali yace "kotu tazo karshe" yatashi yafice police sukazo aka wuce da Nura lawyer shi da Alhaji Musa suka bisu, court room din yarage saura su Hadiza, hawayen da Hadiza ke rikewa ne suka zubomata wlh bazamata iya describing in words how she's feeling right now ba, bata taba expecting Nura zai saketa ba sabida ta makashi a kotu, tunanin baimazo ranta ba yanzu Nura yamata saki biyu kenan, Mrs Oyenyi da bata wani san komiba ita she's just a lawyer tace "why are you crying? You should be happy a man like this dayayi inflicting so much pain in you yasake ki infact this calls for celebration ma" Zeenah tace "owooo tell her oo Mrs Oyenyi, I don't know why Hadiza base her whole life on this guy not knowing yanzu ne zaki fara cin rayuwanki da kyau dakuma tsinke, ni dayama miki biyu yacikashe" dasauri Hadiza tadago jajayen idanunta takalleta Zeenah tace "yes you should be free of this Nura for good haba yanzu kuma abin takaici kina wani zubar da precious hawayenki sabida namiji wlh tir Hadiza kinji kunya, you are a disgrace to mata damukasan ciwon kanmu, you are a disgrace to all feminist out there" hannu Hadiza tasa ta share fuskanta tass tai murmushi tace "ba ina kuka sabida Nura yasakeni bane Zeenah, kuka nayi sabida kalman saki feels somehow ajikin mata, but danya sakeni sai mene harda wani amini katanga da gidanshi tunda gidan dirhami gareshi ko gidan sarkin dubai ne dashi ko prince of Saudi useless Man gidan da I can buy like 10 of it" Zeenah tace "owooo, tashi mutafi jor let's go and celebrate book hotel and sleep today kafin gobe muje house hunting" dasauri Hadiza tace "gidan ki fa? I thought anan zan kwana"? Dan murmushin yake Zeenah tayi tace "ohh my bad ni nama manta ba matsala saiki kwana agidana, muje let's call Baraka and pick her up a hanya" tashi Mrs Oyenyi tayi sukai sallama daman sun gama biyanta suka wuce ahanya suka dauki Baraka wacce Sam bataji dadin labarin ba amman ina ruwanta, deep down Hadiza is so worried amman Zeenah taki bata room to show how worried she is kuma itama din batason suce tacika depending on a man ko she's a disgrace to feminist.
Sai bayan magrib suka tafi gidan Zeenah, babban gidane mai kyau but baimakai gidan Hadiza girma da kyau dinba dudda matar minister ce, shiga sukayi ciki, Zeenah na murmushi tace "ai you are full ko kina bukatan abinci naga munci mun koshi a inda mukaje bari nabaki ruwa kinsan ni yan aiki na basa kwana da yamma suke tafiya saisa kikaga zan baki ruwa da kaina" Gyadamata kai Hadiza tayi Zeenah tadauko ruwa taba Hadiza tace "muje na kaiki dakinki" dan kallonta Hadiza tayi saitaga kaman she's rushing ko ruwan fa bata budeba amman bata damuba ta tashi tabita sukaje sama takaita wani daki tace "to saida safe"gyadamata kai Hadiza tayi dudda she wanted su danyi hira har zuwa irin 12 din nan nadare but she guess tagaji tunda tun safe suna tare wucewa Zeena tayi agurguje ta sauko kasa ta kwashi takalmin Hadiza dake gaban kofa tashigo dasu da sauri ta wuce kitchen dinta taboye takalmin abaya shi kofa sannan tashiga kitchen agurguje fa tashiga hada girki.

MATAN?? KO MAZAN???Where stories live. Discover now