Chapter one

210 7 1
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*_Wannan labarin ƙirkirarre ne, idan yayi kama da labarin ki/ka toh coincidence ne_*

*Page 1*

*ABUJA*

7PM

         Ƙarar bindingu kawai kake ji babu ƙaƙƙautawa, titin wayam babu kowa sai victims ɗin da abun ya faru a kansu, ihu kawai take tana kiran sunan mahaifinta tare da kallon mutanen abbanta da aka kashe, da ƙyar ta fito daga motar jikinta duk jini tana kallon mutumin da yake pointing ɗinta da bindiga, "Let's go *RAIHAN*  taji an faɗa, dukkannin su fuskarsu rufe da Black mask hakan yasa idanunsa kawai ta ke iya gani. Kafin wani lokaci suka bar gurin a wata bak'ar Benz, daga ita sai gawawwaki suka bari, kuka ta fashe da shi jikinta yana rawa musanman ganin mutanen da suka mutu su biyar harda driver ɗinta her own personal driver cikin sojojin abbanta tana matukar sonshi yana da kirki da mutunci just a year da ya fara aiki da su, mutum me riƙon gaskiya da amana. Karar motocin data ji ya saka ta miƙewa tana ɗaga hannayenta sama jikinta sai rawa yake yi. Sai yanzu taji wani azabar zafi a damtsen hannunta, idanunta ta kai wajen taga alamar shafar harsashi. Sojoji ne suka fito suna nufarta kafin *SENATOR* kuma *GENERAL ALƘASIM*  ya fito ya nufi inda ƴar sa take, tana ganin mahaifinta ta nufeshi tare da faɗawa jikinshi. Riƙeta yayi suka koma mota, kuka take sosai tana ƙoƙarin yi masa bayanin abinda ya faru. "Calm down *NOOR*, just relax" bata kara cewa komai ba sai sauke numfashi da take ji bugun zuciyarta na karuwa, yau taga masifa iya masifa. Bayan sun isa katafaren gidan su wanda za'a iya kira da Manson suka firfito, suna shiga huge pallor ɗin su mahaifiyarta ta taso tana faɗin "Noor!! "Duk sun kashe su! Mom sun kashe Sadeeq! Ta faɗa tana fashewa da kuka. "Ni narasa gane me mutanen nan suke so a wajenka ne sanata! Daga motsawar zaɓe? "Kyalesu, kira Dr yazo ya duba ta, sai ta kwanta" bata ce komai ba ta mai da hankalinta kan Noor dake kuka ta ce, "Are You okay? "No Mom " ta faɗa tana kallon mamanta. Ita ta taimaka mata suka wuce upstairs, a ɗakinta ta kwantar da ita tana faɗin " Ko za ki cire kaya? "No Mom please ki zauna dani " da toh ta amsa tana hawa kan gadon, "Kinga duk kin ɓaci da jini is better kiyi wanka ko? Noor tana kuka ta kalli mamanta ta ce, "Ok" Mom ce ta taimaka mata ta cire kaya sannan suka shiga toilet dan duk a tsorace Noor ɗin take. Bayan sun fito zama tayi tare da zame bathrobe din tayi exposing hannunta dake bleeding, bandage Mom ta dauko a first-aid box ta daure mata, dryer ta dauko ta shiga busar mata da gashinta wanda ya sha kitson attachment. Kafin tace wani abu akai knocking, me aikin Noor ce ta shigo da tray sai data ajiye sannan ta sunkuyar da kanta ta ce, "Dr yazo" "kice ya shigo" Mom ta bata amsa. Da tohm ta amsa sannan ta fita. Ba'a ɗau lokaci ba ya shigo, bayan sun gaisa da mom sannan ya tambayi Noor ya take ji, drugs ya rubuta yayi dressing wound din sannan yayi excusing kanshi ya fita. "Kwanta Noor, bari na kai wa *TAHIR* ya siyo miki drugs ɗin" a hankali ta gyaɗa kai alamar ok. Lumshe idanunta tayi duk abinda ya faru ya fara dawo mata ƙwaƙwalwa, his eyes are so unique ita kam bata taɓa ganin namiji ne kyan idanun Raihan ba kamar yadda taji an kira shi dazun! Why would they attack them? Meyasa zasu kashe mutun har biyar? Me sukai musu? Har da innocent Sadeeq! Hawaye taji sun zubo mata, Guy ɗin just get married 3months ago! Ya iyalinsa zasu ji? Meyasa mutane basu da imani? Share hawayenta tayi tana gyara kwanciyar ta. Mom bata wani jima ba ta dawo tana kallonta ta ce, " Kici abinci ki sha magani I'm coming" daga haka ta fita ta wuce ɗakin Sanata. A kwance ta ganshi yana kallon News abinda ya faru recently ake haskawa ga gawawwakin victims ɗin jini ta ko ina ba kyan gani. "Haka zamu zuba ido akan abinda ke faruwa? "Kyale su Hafsat! Zaɓe yazo dole sai haƙuri" "a kyale fa kace? Rayuwar ƴata fa aka saka a haɗari? My one and only child! Kuma kace nayi haƙuri? Shekarata 15 da aure sannan na sameta kuma kace min na zuba ido bazaka ɗauki mataki ba? Yanzu da sun harbeta fa? "Ai basu harbeta ba ko? So ki kwantar da hankalin ki, nasan suna kallon duk wani move ɗin mu" zama tayi tana kallon shi cike da damuwa ta ce, " Kawai ta koma turai, idan yaso bayan zaɓe sai ta dawo" kai ya girgiza yana kallon Hafsat ya ce, "Campaign ɗin da take yi mana fa? "Amma sanata ai bazamu fifita campaign akan rayuwar yarinyarmu ɗaya tilo ba ko? "Kinsan kema bazai yu ba, babu abinda zai samu Noor ba fini sonta kikai ba, kawo min green tea" Ta shi tayi ta fita jikinta duk a sanyaye.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now