Chapter nineteen

44 3 2
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 19*

      Emergency aka kai Hydar within 20mins of the incident. IG ne tsaye a waiting area zuciyarsa na bugawa, tsoransa daya ace Hydar ya mutu. An dau lokaci sosai kafin a fito da hydar wanda ke numfashi tare da taimakon oxygen. Da idanu IG ya bi Hydar wanda ke kwance kamar gawa. Likita ne ya kalli IG ya ce, "Ka kwantar da hankalin ka he will be ok! Muje office" daga haka yayi gaba IG yabi bayan shi. Sai da ya zauna sannan ya kalli IG ya ce, " in sha Allah zai samu lafiya, ga wannan drugs ɗin zaka siyo Allah ya bashi lafiya" da Ameen IG ya amsa, rubuce-rubuce likitan yayi a prescription sheet sannan ya bawa IG ya fita. Sai yamma liƙis Ummi taxo asibitin duk hankalinta ya tashi, kallon IG tayi tana faɗin "Amma dae zai farka ko? Murmushi ya danyi kafin ya ce, "In sha Allah, bari na wuce zan dawo ko chan anjima ne" kai ta gyaɗa kafin ta amsa da faɗin, " Na gode sosai kaji ko? Murmushi kawai yayi sannan ya fita. Wa she gari da safe aka gurfanar da General a gaban kotu da kanshi yayi confessing komai tare da wanke matarsa da cewar bata san komai a kan lamarin ba, sosai General yayi breaking heart din matarsa da ƴarsa daga nan yan sanda suka tafi dashi. Noor na kuka sosai ta riƙe mamanta. Fitowa sukayi tana kallon dad dinta ya shiga motar yan sanda aka wuce da shi. Riketa Mom tayi suka wuce a motar da suka zo da ita. Bayan sun isa gidan gwamnati kayansu Mom ta saka aka haɗa musu tas, domin kotu basu kwana goma su bar gidan gwamanti. A ranar Mom da Noor suka bar gidan. Daya daga cikin gidajen Mom suka koma da niyyar idan komai yayi settling zasu bar kasar for some months. Bangaren Hydar kuwa biki na ta matsowa and he's still un well domin aiki ma za'a sake masa saboda internal bleeding da yake samu. Ɓangaren Aminatu sai shirin biki ake dan ya sanar da ita baza'a daga ba, duk iya bakin ƙoƙarin da uba zai wa yarsa Abba yayi wa Aminatu shi tsaf Abba ya kara gyawara Hydar gidan shi ya kara dawowa sabo dal... ga shi ya sha furniture ba karya. Babu wani shagali da akai a bikin domin Hydar bai jin dadi dan two days da yin auren za'a yi masa aiki. Ranar asabar da safe aka daura auren Hydar Ammar da amaryarsa Aminatu, Abdallah da amayarsa Khairat sai Farooq da amaryarsa Khadijah... Gidan mommy aka kai Aminatu domin Hydar yana gidan. Mommy ta mata fada sosai kuma ta sanar da ita zasu zauna anan gidan kafin Hydar ya karasa jin sauki. Har dakin hydar Mommy ta kaita tana kallon su biyun ta ce, "A dai yi hakuri, Allah ya baku zaman lafiya" da Ameen Hydar ya amsa sannan ta fita. Dagowa Aminatu tayi tana kallon shi idanunta duk sun ƙanƙance saboda kuka. "Kukan fa? Ya faɗa daga kwance. Numfashi ta ja a hankali tana kallon shi ta ce, "Ya karfin jikin? "Alhamdulillah na warke tunda gaki a nan" bata iya ce masa komai ba ta sauke kanta daga kallon shi. "Ya kukai da likitan ki?  I mean your cardiologist" "Normal" ta faɗa tana mikewa tsaye. "Amina! Ya kira sunanta. Ba tare da ta kalleshi ba ta amsa da, " Ina jinka" " are you sure? Murmushi ta danyi kafin ta amsa da sure. Kofar da ta gani a buɗe wanda ya tabbatar mata da toilet ne ta shiga tana rufe kofa. Sink ta nufa tana kunna ruwa da karfi, tari ta fara yi tana fitar da jini sosai har guda² yake yi. Ta daɗe sosai kafin ya tsaya... a wajen ta zauna dan tayi week sosai. Ganin dadewar tayi yawa ya saka Hydar kiran sunanta. Da kyar ta iya amsawa tana mikewa, sink din ta wanke sannan ta fito tana dafe bango. Da idanu ya bita har ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. "Are You okay?  Kai kawai ta gyaɗa masa. Da kyar ya iya miƙewa zaune yana faɗin, "Ni fa mijinki ne Amina, ki fada min ko ma menene" kai ta girgiza tana mikewa tsaye ta ce, "Me zaka ci in karbo maka wajen Mommy?  "No ki huta za'a kawo" kafin ta amsa suka jiyo knocking.. "come in" cewar Hydar yana kallon kofar. A hankali ta shigo tana kallon Aminatu dake kallonta... "Aunty ga shi, mommy ta ce ki tabbatar ya sha drugs dinsa sannan yayi wanka" kai kawai Aminatu ta gyada tana karbar tray ɗin hannunta. Da idanu ta bi yarinyar har ta fita sannan ta juyo tana kallonsa. Ajiye tray ɗin tayi tana faɗin "Bari na zuba maka" bai ce komai ba har ta zuba masa kazar da aka yayyanka musu tare da madara me sanyi. Kusa dashi ta dawo tana faɗin " Sannu" karbar plate ɗin yayi ta ajiye drink din a bedside drawer tana sunkuyar da kai. "Ba zaki ci ba? Ya faɗa idanunsa a kanta. " No ka fara ci zan ci" "mu ci tare" ya faɗa yana kallonta. Kai ta girgiza tana ƙoƙarin miƙewa. Hannunta ya riƙo wanda yaji kamar ya riƙe ƙashi saboda siranta. Da idanu yabi tsintsiyar hannunta kafin ya sauke idanuwanshi a kanta ya ce, "Ina medications dinki? Kamar jira take ta fashe da kuka tana faɗin, "ban taba sha ba kuma bazan taba sha ba Hydar! An cuceni an cuci rayuwata" "But I'm here for you Amina! Na miki alkhawarin farinciki har abada" kai ta girgiza tana goge hawayenta ta ce, "Bazaka gane ba Hydar"....
     Amina kuwa na fita a ɗakin wajen Ummanta ta nufa a kitchen tana faɗin "Aunty! Tabdijan kinga matar Yaya kuwa? Wallahi kamar mai ƙanjamau" "bana son gulma dan Allah! Ina ruwanki? Haka ya gani yace yana so kar na kara ji na ruwanki kinji dae ko? Kai ta gyada alamar toh. Wanke² ta taya Aunty Saudah suka karasa.  Wa she gari da asuba Hydar na ƙoƙarin tashi daga kan gado ya jiyo zubar ruwa a toilet tare da amai ƙasa². Mikewa yayi yana dafe kasan cikin shi ya nufi toilet ɗin.. budewa yayi yana kallonta durƙushe a kasan toilet din tana amai me haɗe da jini. Zaro ido yayi yana faɗin, "Amina! Bata iya kallonsa ba ballantana ta iya tanka masa dan ta ta galabaita sosai. Da kyar ya iya ƙarasawa sam bashi da karfin da zai dagota sai tsugunnawa da yayi a kusa da ita yana faɗin, " Sannu" hannunsa ta rike tana jan nunfashi da ƙyar da alamar ma numfashin so yake ya dauke mata ganin yadda take fighting da shi. Aunty Saudah ce ta fara sallama jin shiru ya saka ta shigowa bedroom ɗin... "Hydar! Hydar!! "Fitowa yayi daga toilet yana riƙe ciki ya ce, " Amina ce kira mommy" "me ya sami Aminar? Cewar Aunty Saudah tana nufar toilet. A kwance ta ganta tana numfashi sama², fitowa tayi da sauri ta nufi hanyar fita, ba'a dau lokaci ba suka dawo da mommy, da kyar dai suka dauki amina zuwa mota, Mommy tayi driving Aunty Saudah da Amina a baya. Bayan sun isa asibiti aka kai Aminatu A&E.... taimakon gaggawa aka bata saboda rashin nunfashi... within 30mins of nursing mgt ta dawo dae² sai dai idanunta sunyi jaa sosai. Word aka kaita domin hutu tare da saka mata IV fluid. Drugs aka rubuta musu Mommy ta fita siyowa. Hydar ya kira Aunty Saudah yafi sau goma daga karshe ma kashe wayarta tayi ta ajiye. Bayan sallar la'asar Amina da Aunty Saudah suka wuce gida ya rage sai mommy kawai. Da idanu kawai Mommy ke bin Aminatu ganin yadda ta rame kasusuwan jikinta kana ganinsu. Taɓe baki tayi dan itakam bata san me Hydar ɗin ya gani jikinta ba har yake so! Toh ko dai taysayinta yake ne ya saka ya aureta? Wayarta ce ta fara ruri hakan yasa ta dawo daga duniyar tunanin data faɗa... dauka tayi tana karawa a kunne... Shuru tayi na yan seconds kafin ta ce, " Ok bari na muku sending address din" daga haka ta kashe wayar, sms ta turawa Abba kafin ta ajiye wayarta. Kafin sallar magariba suka iso har da Hydar dake kan wheelchair dan ba sauki yaji ba. "Me likita yace a kan condition ɗinta? Sai da Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta amsa da faɗin, "left sided heart failure and she's HIV positive I read her file" da idanu Hydar yabi Mommy. "HIV positive? Are you sure? Cewar Abba yana kallon Mommy cike da mamaki. "100% sure ma tunda na gani jikin tests din da akai mata! "Toh kai Hydar kasan she's HIV positive ka aureta? Ina ma tests din da aka ce ayi kafin auren duk bakai ba kenan? "Shi yasa ai nace kuje tare ayi har da ita amma kace You trusted him! Gashi nan ai ya baka kunya" Mommy ta karɓe zancen. "Magana fa nake maka kasan da cutar ko kuwa! Sunkuyar da kansa yayi a hankali ya ce, "Na sani" shuru ɗakin ya dauka chan Mommy ta ce, "Ashe baka da hankali bansani ba? Fada min wani abu ya shiga tsakanin ku? Shuru Hydar yayi kansa a ƙasa. "Ba magana ake maka ba!? Abba ya faɗa cikin tsawa. " Babu fa abinda zai canza na rigada na aureta Please stop creating dramas! "Ok mune ma muke creating din drama ko? Are you out of your senses ne Aliyu? Ko ka fara shaye² ne kamar ɗan uwanka? Toh wallahi sai ka saketa ai wannan auren be hallarta ba ko a Addini domin da cutarwa a cikin sa! Cewar Mommy rai a matuƙar bace. "Ni bazan iya sakin mata... be karasa ba Mommy ta dauke shi shi da mari tana faɗin "Sai dai idan bani na haifeka ba wallahi amma Allah auren nan sai an raba shi dan ubanka ko kune Romeo and Juliet wannan ai sakarci ne" "Is okay Zarah bari muje gida" cewar Abba yana ficewa. A hankali Hydar ya ɗago yana kallon Mommy ya ce, "dan Allah kiyi haƙuri wallahi Amina zata iya mutuwa and babu wanda zai iya rufa mata asiri kamar ni shiyasa na zabi na aureta" "Oh ba sonta kake ba right? Kai ya girgiza a hankali yana riƙo hannun Mommy ya ce, " Kiyi haƙuri dan Allah kar ki kara tada zancen Please mom" zame hannunta tayi cikin nashi tana faɗin "Kana sonta ko a'a? "Ina sonta! Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba. "Karya kake wallahi! Tausayinta kawai kake! Amma wallahi ka cuceni Aliyu ka cuci mahaifinka da Ammar! Yanzu kasan is hardly ace baka da ita ko? "Bani da komai Mom! Ya bata amsa yana kallon hawayen dake kuncinta. " Ta yaya kake da tabbacin hakàn? Da kyar ya iya gathering courage ya ce, "Babu abinda ya shiga tsakani na da ita" da idanu ta bishi kafin ta ce, " Toh idan hakane Allah sai ka saketa dan bazai yu ka auri yar mutane kai a wahale ita a wahale ba! "Amma Mommy idan na saki Aminatu ban mata adalci ba wallahi, zan kara saka ta cikin wani hali, wallahi tausayi take bani sosai" shuru Mom tayi dan ta rasa me zata ce masa kuma. "Kiyi haƙuri" ya faɗa a hankali. Miƙewa tayi ta fice daga dakin. Hydar kuwa ƙarasawa yayi inda Aminatu take a kwance, hawaye ya gani ta gefen idanunta. Kasa cewa komai yayi, a hankali ta buɗe idanunta a kanshi tana kallon kwayar idanunshi. "Ya jikin? Ya furta a sanyaye. "Da sauki" ta bashi amsa tana sauke idanunta daga kallon shi. "Zan sha ruwa" ta kuma faɗa a hankali. Kallon dakin yayi yaga ba ruwa. "Bari naje na siyo" da toh ta amsa tana kallonsa. Wheelchair din ya danna ya fara tafiya da kanshi sannan ya fito daga dakin... ya dau lokaci kafin ya isa canteen din cikin asibitin ruwa ya siyo cartoon daya sannan ya dawo, a entrance din shiga reception yaga cincirindon al'umma har da ma'aikatan asibitin.. bai karasa ba ya wuce, yana isa dakin da Aminatu take yaga wayam, ajiye ruwan yayi yana jira dan yayi tunanin ko ta shiga toilet ne. Ya kai 10mins a zaune Shuru, toilet ɗin ya karasa tare da yin knocking amma yaji shuru, buɗewa yayi yaga ba kowa. "Toh ina ta tafi? Ba shi da amsa hakan ya saka ya fito daga dakin yana yan kalle², a guje yaga ana tura gadon emergency wanda ya baci da jini ta ko ina har inda aka wuce da shi jini ne a kasa da idanu ya bisu, sai da suka gama wucewa sannan yaga wata nurse da sauri ya tare ta yana faɗin, "Dan Allah ko kinga patient din dake Aminity 3? " An wuce da ita A&E ta fado daga 3rd floor trying to commit suicide" daga haka tayi sauri tayi gaba. Da idanu ya bita dan bai ma wani fahimci abinda ta ce ba. Kaf ya gama bin ko ina amma bai ga Aminatu ba, sai a yanzu hankalinsa ya dawo jikinsa har ya fahimci bayanin da nurse din dazun tayi masa.... Kafin ya isa A&E din yaga Dr ya fito yana cire gloves duk jini. "Yawwa likita an shiga da patient dina ciki" da kallon likitan ya bishi sai kuma ya saki dan murmushi kaɗan ya ce, "Hydar! Ya mahaifinka? "He's fine" ya amsa a ƙage. "Wa ka kawo? Likitan ya kuma tambayar shi. "she's my wife a Aminity 3 take ance ta fado daga bene is she ok? Cike da mamaki likitan ya ce, "Your wife? Kai Hydar ya gyaɗa alamar eh. Ajiyar zuciya Dr ya sauke yana faɗin "kai kadai kazo? Kai ya daga alamar eh. "Ok she will be ok, kira min Abbanka" da sauri Hydar ya ciro wayarsa ya shiga kiran number Abba. Sai data kusa tsinkewa sannan ya dauka. Mikawa likitan yayi ba tare da yace da Abba uffan ba. "Biyoni office" cewar likitan yana kara wayar a kunnensa.  Gaban Hydar ne ya fara faduwa jin abinda likitan ya ce da Abba. Kashe wayar yayi bayan sun shiga office ɗin ya mikawa Hydar wayar yana faɗin, " Ka jira shi a anan" "Dr ka tabbatar tana lafiya? Kai ya gyaɗa alamar eh. "Ok toh muje na ganta Please" numfashi likitan ya sauke yana kallonsa da kyau ya ce, "Tana bukatar hutu" Hydar bai ƙara cewa ba yayi relaxing a jikin wheelchair dinsa bugun zuciyarsa na ƙaruwa. Sai da akai sallar magariba Abba da uncle Umar suka iso asibitin. A corridor din da zai sadaka da office ɗin likitan suka hadu da Hydar daya fito daga office din ba jimawa. Da idanu Abba ya bi shi kafin ya ce, "Ina Dr Sadeeq? Cikin office ɗin Hydar ya nuna masa ba tare da yace komai ba. Bayan sun shiga Hydar ya kalli likitan ya ce, "Ku bani dead body ɗin ya kamata ace an kaita I know she's dead! Ajiyar zuciya likitan ya sauke yana kallon Abba ya ce, " Muje" da toh Abba ya amsa ya mike suka fito daga office ɗin uncle Umar yana gefan Hydar. Ambulance aka basu aka saka gawar Aminatu sai bleeding take yi. Har suka isa gida Hydar bai kuma cewa komai ba. Ba'a kai Aminatu ba sai washe gari... sosai gidan su Hydar ya cika da jama'ar Abba da iyayen Aminatu, mahaifin Aminatu kuwa gani yake shine silar faruwar komai sosai yayi kukan rashin ƴarsa da kuma dana sanin irin abubuwan daya aikata a gareta, su kansu mommy mutuwar ta dakesu more especially yadda Hydar yayi blaming dinsu akan abinda ya faru kafin tayi committing suicide.

      *A  Year later*

       Yadda iska me sanyi take ratsawa a garden din kai kace a wata duniyar kake, slowly yake sipping lemon dake hannunsa yana latsa wayar sa. Kafarsa ya miƙe yana sauke ajiyar zuciya me sanyi. Miƙewa yayi tare da ɗaukar glass cup ɗin da yake shan lemo ya nufi cikin gidan, a zaune kwance ya ganta ta takure akan kujera bacci ya dauketa. Taɓe baki yayi ya wuce upstairs. Wanka yayi ya shirya cikin kaya marasa nauyi tare da fesa turare ya saka agogo ya sakko. Jikin kujerar da take ya fara bugawa yana kiran sunanta da ƙarfi dan yasanta da nauyin baccin jaraba. A hankali ta buɗe idanunta tana saukesu a kan shi. "Zan fita idan kinga dama ki tsaya jirana" sauke idanunta tayi daga kallonsa tana faɗin, "Yaya bana jin daɗi" "Toh waye yake jin daɗi Amina? Kowa ma baya jin daɗin ai" kamar zatayi kuka ta kuma faɗin, " Toh" har ya kai bakin kofa ya juyo yana kallonta ya ce, "Me ya dameki? Slowly ta ce, "Ciwan mara" "ke kullum baki da cuta sai Ciwan mara? Saka hijabi ki biyoni! A hankali ta mike ta nufi dakinta, bata dau lokaci ba ta dawo tana kallonsa ta ce, "Gani" bai kulata ba ya fice, bin bayansa tayi zuwa mota. Mai makon taga sun nufi Chemist ko asibiti taga sun dauki hanyar gidan Umma, ba ta ce da shi komai ba har suka isa gidan. Bude motar yayi ya fita hakan ya saka itama ta biyo shi. A falo ya tarar da mahaifiyar sa tana kallo. Ƙarasawa yayi ya zauna bayan ta amsa sallamar su. "Ina yini Umma? "Lafiya lau Raihan... ah ah shigo mana Aminatu! Umma ta ƙarashe maganar tana kallon Amina. Kuka Aminatu ta saki tana kallon Umma ta ce, "Bani da lafiya yaki sai min magani Allah ni bana son Yaya" da idanu ya bi ta yana ɓalla mata wata uwar harara kamar mace. "Waye dama yake sonki? Kwaila dake! "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Oh ni Bilki wato dae bazaka canza ba? Wai sau nawa kake so a zauna a sasanta lamarin nan ne? Idan banda ita Aminatun wace macece zata yarda ta aureka ko sana'a baka da ita? Ga kuma image dinka daka rigada kayi tarnishing? Ka ɓatawa kanka reputation? Sai yaushe zakai hankali ne Raihan? Kaifa ba yaro bane! Tashi ka bar min gida! Miƙewa yayi yana kallon Amina ya ce, "Wuce muje" "Babu inda zata je duk ranar daka san darajarta sai kazo ka ɗauketa! Da idanu yabi Umma kafin ya fice, direct gidan su ya nufa. A zaune yaga Hydar yana latsa laptop. Bai ce komai ba ya zauna yana faɗin "Ya jikin? "I'm Good! Ya amsa ba tare da ya ce uffan ba. " Ina Mommy? "Ka duba! Daga haka Hydar ya miƙe ya koma daki. Ajiyar zuciya ya sauke yana bin Hydar da kallo. Ko zama Hydar din beyi ba Raihan ya shigo yana buga kofar dakin idanun shi cikin na Hydar ya ce, "Kai baka iya fushi bane? Shekara guda ka kasa mantawa da komai?  Da idanu Hydar ya bi Raihan yana ƙoƙarin fita daga dakin. Arm dinsa Raihan ya riko yana dawo dashi ya ce, "I'm sorry! Moreover mommy batai deserving wannan fushin naka ba, after all she's your Mom! Just pray for the best kuma ka bawa Noor second chance she loves you" "Sake ni! Cewar Hydar ba tare da ya kalli Raihan ba. "Bazan sake ka ba! Naga kamar ka fara haukacewa? Ko ka samu depression ne? Wai baka da ido baka ga yadda Mommy ta zama ba? Your Mom deserves to be happy, baka san irin wahalar data sha kafin ta kawo wannan gaɓar ba! Ko baka san irin rayuwar data fara yi da Abbana ba? Yanzu kuma ka girma shine zaka fara mata hauka saboda mace? Kana da hankali kuwa Hydar? "Nifa ba saboda mace nake haka ba! Kawai haryanzu ina jin ciwan abinda ya faru da Aminatu" ajiyar zuciya Raihan ya sauke dan yaji dad'i yau ɗin da Hydar ya kula shi. "Ok inaso kaje ka samu Mommy ka bata haƙuri sannan ka daure dae ka komawa Noor! Hydar bai ce komai ba ya fice. Biyoshi Raihan yayi yaga ya fita a gidan. Shi kuwa dakin Mommy ya shiga. A kwance ya ganta tana duba littafin addu'oi. Mikewa tayi zaune tana fadada murmushinta. "Mommy ina yini? "Lafiya Lau ya ƴata? Kamar zaiyi kuka ya ce, "Umma ta kwace ta" cike da rashin fahimta ta ce, "Umma ta kwaceta kamar yaya? "Eh kamar yadda kika ji, yarinyar bata da lafiya na dauketa zan kaita asibiti sai na fara niyawa na gai da Umma shikenan Amina ta fara kuka wai tana ciwan mara na ki kaita asibiti shine Umma ta kwace ta"  "iKon Allah! Bari na kirata" cewar mommy tana daukar wayarta. Shafa kai yayi yana kallonta. A handsfree ta saka wayar bugu uku ta ɗauka tare da yin sallama....

Autarmama ce

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now