Chapter ten

76 7 2
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 10*

        "Yallaɓai! Yallaɓai!! Bai kulata ba ya cigaba da tafiya. Da sauri ta isa gaban shi tana faɗin " Ka manta baka bani wayar ba" Hannunta ya ja zuwa wani loko yana turata ciki da karfi. Runtsa ido tayi tana riƙe hannunta. "Yallaɓai da zafi wallahi, dama wayata zaka bani ka karba kuma zaka tafi baka bani ba" ta faɗa trying hard to control her self. Tana gani ya buga wayar da kasa, tsugunnawa yayi ya ɗauka babu abinda wayar tayi saboda key pad ce kuma me kwari, buɗe wayar yayi da niyyar cire memory card ɗin yaga wayam ko layi babu. "Ina layinki da memory card ɗin ciki? Kamar zatayi kuka ta ce, "banda layi fa! "Ni zaki rainawa hankali? Kinsan wanene ni ai ba sai na miki dogon bayani ba! Kai ta girgiza da sauri tana ƙoƙarin barin wajen. Dawo da ita yayi yana hade rai sosai ya ce, "Ki faɗa min me kika ji? "Wallahi babu abinda naji dan Allah ka sakeni wallahi ni ba yar iska bace da zaka tsare ni a lungu" tureta yayi yana harararta ya ce, "Waye ɗan iska? "Kai mana" ta faɗa tana goge hawayenta. Tsaki yayi ya bar wajen. Da idanu ta bishi kafin ta ɗauki murfin wayarta ta bar wajen. Ɗakinta ta nufa da sauri ta saka memory ɗin a computer tayi copying sannan ta saka shi a Flash drive ta mayar da komai jaka, iphone 11pro ta ciro a jakarta ta kunna domin karamar wayar farfaɗiya take mata. Wayar minti ɗaya tayi kafin ta kashe ta mayar ghana must go ɗinta. Fitowa tayi, a wajen parking lot suka haɗu da Tahir da Abbas sun sha kyau cikin farar shadda. Da idanu ta bisu kamar yadda Tahir ya bita! She seems suspicious bazan manta words din da ta faɗa masa ba! Ya manta ma da babinta tunda wannan matsalar ta gifto. Nufarsa tayi da sauri tana faɗin "Yallaɓai dan Allah kayi haƙuri rannan bani da hankali ne dan Allah ka yafe min idan Hajiyata taji zata koreni" kallonsa Abbas yayi da sauri Tahir ya ce, "Sai ki kiyaye" daga haka ya wuce. Dogon tsaki taja ta nufi hanyar shiga cikin gidan. "Me ya faru ne? Cewar Abbas yana kallon Tahir. "Nothing serious shirmenta ne" Abbas bai kuma cewa komai ba har suka isa sitting room ɗin General. Noor na zaune a ɗakin Mom, step sister's ɗin Mom suna ta mata fada... "An daura! Hajiyata an daura! Yanzu naji Yallaɓai ranka ya daɗe shugaban kasar gobe ya faɗa na rantse " cewar Aminatu tana shigowa ɗakin. "Oh ni sumayya wai a ina kuka samo wannan yarinyar? Cewar yayar Mom tana kallon Mom din. " Maid ɗin Noor ce, sai haƙuri amma ai ta iya aiki" "ke dallah fita ki bawa Mutane waje! Cewar Hajiya sumayya tana harararta. Jiki a sanyaye ta fita. Ajiyar zuciya Noor ta sauke tana kwanciya a kan gado. "Toh yanzu tarewa zatayi? Naji kince shi yaron ma tafiya zaiyi? Banda ma abu irin na his Excellency ai kamata yayi ya bar shi ga sojoji dayawa sai shi za'a tura? Idan wani abu ya same shi fa? "Nima dae haka na gani" hajiya rabi ta karɓe zancen.  "Ai team ɗin su ne zasu tafi in sha Allah babu abinda zai faru" cewar Mom tana kallon su. Babu wanda ya kuma tada zancen. Sai yamma likis sannan aka shirya Noor cikin lafaya me kyau da tsadar gaske, wajen Dad aka kaita yayi mata faɗa sosai sannan suka kaita chan part ɗin Tahir an sa ke fenti, furniture komai sabo. Tare da Tahir ɗin aka haɗa su akai musu nasiha kafin su Mom su baro, sai kuka Noor take musanman idan ta tuna auren fa  be ɗauru ba. Suna fita ta cire lullubin tana kallon falon kamar ba shi ba an ƙawata shi sosai. "Anjima matar nan zata zo ta dubaki" "ka bari sai gobe idan aka ganta ace me? Gobe kuwa babu wanda zaiyi tunani me zurfi" murmushi yayi yana goge mata hawaye ya ce, "Ki daina kuka" bata kula shi ba ta mike ta nufi bedroom. Kwanciya yayi a kujera yana lumshe idanun shi. Noor kuwa alwala tayi ta zauna a sallaya ta fara jan charbi sai da akayi magariba sannan ta yi sallah ta naɗe sallayar. Wanka ta yi ta saka doguwar rigar bacci tare da hijabi akai. A gefan gado ta zauna tana tunani. Sai da akai sallar isha'i sannan Tahir ya shigo. Plate ɗin hannunshi ya mika mata sannan ya fita, da cup ya dawo wanda ke dauke da madara ya bata amsa tayi ta ajiye ba tare da ta ce komai ba. "Kici ki kwanta, ni zan kwana a falo" kai ta girgiza tana faɗin " Ni zan kwanta a falo ka kwana anan" "Bazan iya ba" ya faɗa yana kallonta. "Kaci abinci? Kai ya daga alamar eh. "Ok akwai bedsheets da duvet kayi shimfida a nan kar kaje falo" murmushi ya ɗanyi kafin ya ce, "Ok" "Gobe sai kayi ordering katifar nan da ake hurawa" kai ya gyada alamar toh. Tas ta cinye kazar ta kora da madarar Tahir kuwa har ya gama shimfidar shi ya kwanta. Brush tayo sannan ta kwanta tana kashe bedside lamp ɗin. Gaba ɗaya ta kasa bacci wani irin yanayi na daban ta fara tsintar kanta. Tun tana daurewa har ta mike zaune daga karshe ma fita tayi daga dakin,  gaba ɗaya takasa zaune ta kasa tsaye, sosai take jin feelings daya wuce tunaninta. What's wrong with her? Tsugunna tayi tana jin tsikar jikinta na tashi... Kitchen ta nufa da sauri amma sam bata ga lime ba... Kamar zatai hauka haka take ji, bata taba experiencing abu irin wannan ba... Karo sukayi da Tahir daya fito daga ɗaki ita kuma tana son komawa. Juya masa baya tayi tana girgiza kai. "Menene? Ya faɗa yana juyo da ita. Runtsa idanunta tayi da karfi ita da take neman gafar Allah? Da sauri ta kwace kanta ta nufi hanyar waje. Biyota yayi tare da kulle kofar ya jefar da makulli tana kallonta ya ce, "Ina zaki je sha biyu saura? Ki faɗa min menene? "Tahir dan Allah ka kulleni a ɗaki" daga haka ta nufi daki tare da tura kofar. Budewa yayi ya shigo yana dan murmushi ya ce, "I'm here for you faɗa min menene? Rikoshi tayi gaba daya ta fita a hayyacinta. "Noor are you ok... Bai karasa ba sakamakon kissing ɗinshi data fara yi. Raba ta yayi da jikinshi yana faɗin "Noor I'm sorry but I can't" chakumo shi tayi kamar zatayi kuka so taka tayi magana amma ta kasa. Rigar jikinta ta fara ƙoƙarin cirewa, riƙe hannunta yayi yana faɗin "Wai me yake damunki? Durkushewa tayi a wajen tana riƙe jikinta. "Noor Lafiya? Jin bata ce komai ba ya saka shi dagota. Kuka take fuskarta duk tayi ja sosai. Rumgumeta yayi shi bai san me ya sameta ba daga gani tana bukatar shi kuma he can't do anything to her Saboda yayi mata alkhawari. "P..ple.. please Tahir" ta fada tana kallon shi. "Kiyi shuru you will feel alright" har karfe 3n dare basuyi bacci ba, ƙarfin Noor gaba ɗaya ya ƙare tayi kukan har ta gaji. Sai gab da asuba bacci ya ɗauketa. Tashi Tahir yayi ya fita daga part ɗin nashi. Bangaren su Abbas yaje ya fara knocking. Abbas ne ya buɗe yana kallonsa from head to toe. "Fito dan Allah" gyara wuyan jallabiyar shi yayi sannan ya fito yana kallon Tahir ya ce, "Ban daɗe da tashi ba yanzu na idar da sallah! "Abbas baka da hankali ne? Ya mukai da kai? "No! I changed my mind!  Besides ai haka dad ɗinta yake sakawa ayi wa yaran jama'a tayi farinciki cewa kai mijinta ne! Chakumar shi Tahir yayi ya ce, "Bani na sha ita ta sha! Kasan ai bana son madara kasan be zama lallai na sha shine kaje kayi haukanka ko? Tureshi Tahir yayi yana kallonsa ransa a ɓace. "Ka ke ta wani hura hanci, sonta kake? Idan ta sha ma ina ruwanka? "Eh sonta nake! Ban aureta dan in rama abinda general yayi min ba i love her! "Kai! Baka da hankali ne? Kasan me kake cewa? Ko ka manta Jamila? Ka manta irin mutuwar da tayi duk dan saboda General? Me abun so a jikin Noor? Bayan ta gama tallan kanta a titi? Waye be sani ba? Kullum yarinya tana yawo wai da sunan tana taya babanta campaign? "Ya isheka! Wallahi ka ƙara wata maganar banza akan NOOR sai na iya harbeka! Nine mutum na farko dana fara sanin Noor kuma wallahi idan ka kara shiga harkata a gidan nan sai dai wani ba kai ba! Daga haka Tahir ya tafi ya barshi cikin mamaki. Bayan yayi sallar asuba ya kalli Noor dake bacci duk tayi wani iri. "Noor! Noor!! Ya shiga ta shinta. Buɗe idanunta da sukai mata nauyi tayi tana kallon shi. A hankali ta sauke idanunta tunowa da yesterday night. "Ki tashi kiyi sallah" bata iya ce masa komai ba ta mike, banɗaki ta shiga, sai da tayi wanka sannan tayi brush ta ɗauro alwala. Bayan ta idar da sallah kan mudubin shi ta kallah babu komai nata. Falo ta fito a kitchen ta tarar da shi. "Good morning" ya faɗa yana mata murmushi. "Ina kwana? "Lafiya lau how are you feeling? Sunkuyar da kanta tayi slowly ta ce, "Meyasa ka saka min wani abu a bin sha na jiya? Gas ya rage yana kallonta ya ce, "Idan zaki yarda dani bansa miki komai ba, i have no clue wallahi kiyi haƙuri" wani abu ta haɗiye da ƙyar tana kallon sa ta ce, " Banga kayan shafe² na ba bari naje na ɗauko" "no zauna zanje na karɓo miki" daga haka ya fita. Karasawa kitchen ɗin tayi ta bude tukunyar tana shakar ƙhamshi offals ɗin da yake bararrakowa yaji kayan ƙhamshi. Rufewa tayi ta koma ɗaki. Tana zaune taga Aminatu har cikin ɗakin.. jakar hannunta ta ajiye tana faɗin " Duka na kwaso miki komai fa! "Sannu" cewar Noor tana kallonta. "Hajiyata baki da lafiya ne? "Taso ki fita! Cewar Tahir daya shigo yanzu" da sauri ta tashi ta fice. "Ki shirya ki fito kici abinci. Bata amsa masa ba ya fita. Bayan ta gama shafe shafenta ta shirya sannan ta fito falo. Ta shi yayi yana kallonta ya ce, "Bari na zubo miki" da toh ta amsa sannan ta zauna. A bowl ya zubo mata ya hada mata shayi ya jera a tray sannan ya fito. Karɓa tayi tana kallon sa ta ce, " Na gode" numfashi ya ja yana saukewa a hankali ya ce, "Kiyi haƙuri" "ba komai" ta faɗa a sanyaye. "Jibi zan tafi akwai activities din da zamu gudanar kafin tafiyar. Spoon ɗin hannunta ta ajiye tana kallonsa. Hannunta ya riƙo yana girgiza mata kai ya ce, "Kar kiyi kuka mana" sauke idanunta tayi daga kallonsa siraran hawaye na biyowa bisa kuncinta. "Na faɗa miki ai zan dawo meyasa kike son saka ni cikin damuwa? "Allah duk wanda aka tura wannan wajen ɗai-ɗai ku ne suke dawowa meyasa Daddy zai turaka? "Na sani Noor kiyi ta yi min addu'a after all I'm serving for my country just pray for your husband to be" kuka ta fashe dashi tana ƙoƙarin tashi. Shima tashi yayi yana faɗin " Dan Allah Noor kiyi haƙuri ki daina kukan" bata ce masa komai ba ta wuce bedroom. Komawa yayi ya zauna yana kallon abincin data ajiye. Daukar tray ɗin yayi ya nufi bedroom din. A kwance ya ganta tana kuka. Kulle kofar yayi yana kunna Acn ɗakin sannan ya zauna. "Kiyi hakuri ki tashi kici abinci ko kaɗan ne" "Tahir dan Allah kar ka tafi" "shikenan naji tashi kici" goge idanunta tayi tana tashi zaune. A baki ya fara bata abinci har ta koshi. Shayin ta karɓa ta fara sha a hankali tana kallon shi. " Yaushe har kika fara sona haka? Ajiye cup ɗin tayi dan ta ƙoshi tana kallon shi ta ce, "Ni ma fa ban sani ba, abinda na sani kawai zuciyata ta yarda da kai from the exact day I saw you tun bayan dawowa ta daga Paris" "Thanks for that Noor" kai ta gyaɗa a hankali. Kusa da ita ya matso yana hugging ɗinta. Tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa. A hankali ta rufe idanunta tana sauke nunfashi a hankali. Sun daɗe a haka kafin ya saketa yana faɗin "bari nayi wanka Daddy yana son ganina" da toh ta amsa sannan ya tashi. Toilet ya shiga, tana nan zaune ya fito sanye da bathrobe. Kwanciya tayi ta juya masa baya har ya kammala shirin shi. "Tashi muje sai ku gaisa da su Mom" bata ce komai ba ta mike suka fito a tare. A falon ƙasa ya zauna ita kuma ta wuce upstairs. A last step suka haɗu da Mom. Murmushi Mom tayi tana faɗin "Ashe ba'a kai miki kayan shafe² ba" sunkuyar da kanta tayi tana faɗin "Ina kwana? "Lafiya Lau kinci abinci? "Eh" Noor ta amsa. "Toh ba dai matsala ko? Ɗagowa Noor tayi hawaye na cika gurbin idanunta ta ce, "Dan Allah kiyi wa Daddy magana ya haƙura da maganar tafiyar... "Babu abinda zai canza Noor idan ma za kiyi wa mijinki addu'a kiyi" a tare mom da Noor suke kalleshi. Gyara hular kan shi yayi yana ƙoƙarin sakkowa. Biyoshi Noor tayi tana kuka ta ce, "Dan Allah Daddy kayi haƙuri wallahi zanyi duk abinda kake so dan Allah Daddy ka soke tafiyar Tahir dan Allah" miƙewa tsaye Tahir yayi yana kallon su. "Indai kina so in soke tafiyar sai dai ya sake ki! Kuma ki koma wajen kanwar mamanki karki ƙara dawowa Sai na nemeki" tsayawa tayi tana kallonshi sannan ta kalli Tahir girgiza mata kai yayi. Goge hawayen ta tayi tana tsugunnawa a gaban daddy ta ce, "Dan Allah kaji tausayina wallahi ina son mijina Dan Allah kayi haƙuri" "Kai muje" cewar Daddy yana baxa babbar riga. Tare suka fita da Tahir. Kuka Noor ta fashe dashi zuciyarta tayi nauyi. "Tashi dan Allah kafin maids suzo su ganki a haka" "Allah mutuwa zanyi idan Daddy ya rabani da Tahir dan Allah kiyi masa magana! "Dallah chan bana son shashanci tashi muje ɗaki" da ƙyar Noor ta iya miƙewa suka nufi upstairs... "Zauna nan! Inaso ki bani hankalin ki da kunnen ki! Ba wai dan wani abu ya saka kika ga mahaifinki baya son alakarku da Tahir ba gani yake kamar zai cutar dake ne domin at first Tahir yayi tunanin mahaifinki shine silar mutuwar babansa da kanwar shi, duk ke kika jawo ai, meyasa tun farko zaki sake masa har ya kai ga ya samu damar taɓaki ballantana ta kai ga yana kissing dinki? Kin bani mamaki Noor! Kuka kawai Noor take dan ji take kamar Tahir ɗin bazai dawo ba idan ya tafi,  yanzun ma gani take da gayya Dad ɗin ya tura Tahir. "Kije ki wanko fuskarki kafin ki sake bata min rai" Ta shi tayi ta shiga bathroom. Kullewa tayi ta sha kukanta sannan ta wanko fuskarta ta fito. Bata tarar da Mom ba a ɗakin, kwanciya tayi a kan gado tana rufe idanunta. Aminatu na kitchen tana gasa breadi gaba ɗaya hankalinta baya kan abinda take yi. Ƙaurin daya ziyarci hancinta ne ya saka ta dawo daga duniyar tunanin data faɗa da sauri ta kashe socket ɗin tana bude toaster ɗin. Bread ɗin yayi baki kirin. Tsaki tayi ta cire biredin ta saka a kwadon shara. Gaba ɗaya taji apatite ɗin ya gudu. Fitowa tayi daga kitchen ɗin ta fito compound ɗin gidan. Part ɗin su na masu aiki ta nufa ta shiga ɗakinta ta kulle, wanka tayi sannan ta shirya cikin atamfa ta yafa mayafi ta fito, gate ɗin gidan ta nufa sojan dake bakin ƙofa ya kalleta ya ce, "Daga ina? "Dallah matsa ka bani waje! Kamar baka ga lokacin dana shigo ba! Daga haka ta buɗe kofar ta fice. Sakayau take jinta, fake identity ɗinta na bata wahala ga uban tusar jaki da kullum sai ta manna a kumatunta. Motar shi ta hango a chan karshen layi. Ƙarasawa tayi ta buɗe ta shiga tana sauke ajiyar zuciya me ƙarfin gaske. Reverse yayi ya bar layin.......

Autarmama ce.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now