Chapter nine

67 5 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 9*

         Sosai ya bada hankalin shi a kan na'ura mai ƙwaƙwalwa da yake operating, duk wasu evidence da ya haɗa a kan General yana ciki, turashi yayi zuwa Flash drive bayan ya gama shiga ya shafa kanshi hoping komai zai tafi a tsari... "Hydar! Ya ji Raihan ya kira shi da karfi. Ɗagowa yayi yana kallon sa from head to toe. " Wai kai baka da hankali ne? Kasan irin hatsarin da kake jefa rayuwar ka har da su Ummi? Sai da Hydar ya ɗanyi murmushi kafin ya ce, "Ni ya kamata na faɗa maka haka Raihan! Ka cire kanka cikin wannan issue ɗin! Idan aiki ya biyo ta kanka Allah bazan nuna na sanka ba! Zan manta da cewa kai ɗan uwa nane! "Baka da hankali! Toh bari kaji General nemanka yake kuma i pretty sure idan ya sameka you'r gone! "Why not ka daukeni ka kaini? Ba abinda ka saba yi kenan ba? Ina mamaki ace wai kayi sharing thesame blood da Abba! Rufe computer yayi yana ɗorawa da faɗin " dan Allah ka fitar min daga ɗaki" sigari Raihan ya ɗauko ya kunna yana hararar Hydar ya ce, "Idan naƙi fa? Hydar wacece Amina? Da sauri ya kalleshi ya ce, "Wace Amina? Oh ai ka fini sani tunda kana aiki da babanta" riƙoshi Raihan yayi da karfi yana faɗin " ka fi kowa sanin wace Amina nake magana! Meyasa kake involving mutane cikin mess ɗinka? Meyasa zaka saka rayuwar yar mutane a hatsari? Kana hauka ne? Da karfi Hydar ya tureshi yana faɗin "ka isheni da warin taba! "Ka ce wa yarinyar nan ta bar gidan nan na rantse maka mutuwa zatayi idan batayi wasa ba! Hydar bai kula shi ya nufi ƙofar fita. Janyoshi Raihan yayi yana faɗin "I'm serious! General ya saka nayi masa binciken wacece ita! Ya fara tantama a kanta! She seems suspicious to him! Wallahi Hydar idan na faɗa masa Wacece ita kasheta zai yi is better ka cireta cikin haukanka!  Chakumar shi Hydar yayi ransa a matuƙar bace ya ce, "Wai kai baka da zuciyar musulunci ne? Baka da tausayi? Ina imaninka! Mutane nawa zakayi sanadiyyar mutuwar su? Mutane nawa zaku saka a wahala, kuna nunawa duniya ku masu gaskiya ne bayan kuma zalintar su kuke! Mata nawa zaku kashe? Mata nawa Raihan? Baka tunanin kai ma kana da ƙanne da ƴan uwa? Me zai faru da su wataran? Ƴan mata nawa kukai raping? Saboda rashin tausayi da rashin imani ku saci yara ku fitar dasu kasar waje a farka cikin su a saka kwaya a dawo dasu a sake farka cikin su a ciro kwayar sun mutu a banza kenan? Saboda kuna da uwa a bakin murhu? Ku sace yaran mutane ku kashe duk dan suna da clue a mugayen ayyukan ku? Shigowa da makaman da yake raba muku ba komai bane a wajen shi! Ya gurɓata mana kasa kuma wai ace har da kai a ciki? Raihan me karasa? Menene Abba be baka ba a rayuwar nan? Wace iriyar tarbiyya ce mommy bata bamu ba? Waya saka ka cikin wannan harkar Raihan? Meyasa kake ƙoƙarin kashe kanka da kanka? Idanun Hydar sunyu ja sosai hakan ma na Raihan. Ƙoƙarin tureshi Raihan yayi amma HYDAR ya riƙeshi tamau, zafin zuciya na ɗibar Hydar ya tureshi da karfi yana faɗin " Wallahi duk ranar dana kamaka doka ta bani dama sai na harbeka! Murmushi Raihan yayi wanda ake kira da yafi kuka ciwo yana kallon Hydar ya ce, "Kayi duk abinda zakayi! Cikin kunar zuciya Hydar ya nufe shi ya chakumo shi kyakkyawan punch ya bashi a hanci, kan kace kwabo ya fara bleeding. Shafo jinin Raihan yayi yana kallon Hydar. "Sakeni! Ya faɗa idanunsa cikin na Hydar. "Hydar na ce ba zaka fito ba abinci har ya fara sanyi? Toh ga shinan na biyoka da sh... Tsayawa tayi ganin HYDAR rike da Raihan ga jini a hancin Raihan. Da sauri ta ajiye kwanon hanunta tana faɗin "Ƙalu innalillahi wa inna ilaihi rajiun, me zan gani haka? Me haka Hydar? Sakinshi Hydar yayi yana yarfe hannu. "Wani irin shashanci ne wannan? Me yake damunka? Ko kaima ka fara shaye²n ne Hydar? Meyasa zakai wa ɗan uwanka haka har da fitar masa da jini? "Alhaji! Alhaji! Grandma ɗinsu ta fita da sauri tana kiran mijinta. Tare suka dawo lokacin Raihan na toilet. "Me yake faruwa ne? Cewar grandpa ɗinsu yana kallon Hydar. "Dukansa yayi har da jini, ni ban taɓa ji sunyi faɗa ba wallahi, ya zaku ɓata rawar ku da tsalle? Ana yabon ku sallah ku kasa alwala? Me ya faru ne Hydar? "Ki tambaye shi" cewar hydar yana kallon Raihan daya fito falon yanzu. "Kai Raihan me ya haɗaku? Nasan kaine da neman fitina" Alhaji ya faɗa yana kallonsa. "Ai dama Hydar ne na kowa! Kowa ya tsane ni! Ganin idanunku ne ni ya daka har da jimin ciwo amma kuna blaming ɗina saboda banda gata! Daga haka ya fice ya basu waje. "Kai hydar me ya faru? Kai ya girgiza shima ya tashi ya fice. "Kar dai akan mace suke fada? Cewar grandma ɗinsu tana kallon Alhaji. "Haba ke kuwa kawai sai su kama dukan juna akan mace? "Eh fa, kasan halin yaran zamani, idan ba haka ba me zai sa suyi fada? Kowa da yasan irin shakuwar dake tsakanin su biyun, baka taɓa jin kansu tun suna yara toh me yayi zafi haka? Tunda kaga ran Hydar ya baci har ta kai shi ga dukan Raihan kasan abun babba ne, toh ko dai Mustapha zan fada wa? Kai Alhaji ya girgiza yana faɗin, " Kyalesu zasu shirya, Allah dai ya kyauta" da Amin ta amsa sannan suka fito.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now