Chapter twenty three

67 4 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 23*

          Amina ce zaune a gefan gado ta haɗe rai kamar za tayi kuka. Raihan dake goge jikin shi alamar yanzu ya fito daga wanka ya kalleta ya ce, "Na ce miki yanzu ta tafi ai, duk inda 8am tayi me aikin kwana ta tafi ga shi yanzu har kusan tara, ya kamata naje saboda Mommy ta dawo gida ko? "Ai Ummana da ummanka sun tafi tun dazu ka bari sai anjima ni bana so ku haɗu ko a hanya" murmushi yayi me kyau yana ajiye towel din hannunsa ya ƙaraso inda take ya ce, " Oh har kinsan kiyi kishin mijinki kenan? That's good" ya ƙarashe maganar yana ɗan taɓe baki.  "Ok idan na zauna a gida zaki barni inyi? Tashi tayi da sauri tana faɗin, "Me zakayi? "Bacci mana! With your dirty mind" ya ƙarashe maganar yana dariya. Riƙota yayi yana kallon cikin idanun ta ya ce, "zamu koma US idan Hydar yaji sauki, Please Amina behave yourself dear, zan saki a makaranta kuma hakan ba yana nufin cewa na baki freedom ɗin da zakiyi hanging da kowa ba, ke matar aure ce kuma nan gaba zaki zama uwa in sha Allah, kiyi abinda ya dace kinji ko? "Ni bazanje makaranta ba tunda baka so" ɗan murmusawa yayi yana jan kumatunta ya ce, "So kike Mommy ta dakeni? "A'a ni zance mata bana son zuwa" ta ƙarashe maganar tana kwanciya a jikinshi. Rungumeta yayi yana shafa bayanta. Abubuwa ne sukai ta dawo masa brain dinsa. Yaso kasancewa da late Amina ashe tashi Aminar na nan zuwa alkhairin sa. Ji tayi ya ƙara matseta. "Yaya zaka karyani" ta fada da ƙyar. "Ke dai kike son rikita ni" kin cewa komai tayi tana sauke nunfashi.

      *PARIS*

It's been some days da zuwan su Paris, suna zaune a gidan da Mom ta siya musu. Noor na kwance a bedroom ɗinta tana latsa waya, tabbas rayuwa tana juyawa a duk lokacin data so, she wish Dad ɗinta be biyewa san zuciya ba ya aikata mummunan ayyuka da yanzu family ɗinsu ya cika, tana son Dad dinta she missed him alot. Knocking ɗin kofar ɗakinta akayi. Da sauri ta tashi tana goge hawayenta kafin ta bada izinin shigowa. Mom ce ta shigo tana mata murmushi ta ce, " Wedding gown na kawo ki zaba for your wedding reception" "So soon? Ta faɗa tana kallon Mom. "why? Ko bakya sonshi ne yanzu? Kai ta girgiza tana kallon Mom ta ce, "Nima ban sani ba Mom, na kasa fahimtar kaina Tahir nake so ko Hydar" "Tahir is the best match for you dear, ni kaina yafi kwanta min akan Hydar, kinsan irin abubuwan da suka faru a baya! Just forget about him and concentrate on Tahir, he still loves you, a wannan zamanin ba ko wani namiji ne zai iya abinda Tahir yayi ba, idan da wani ne bazai yarda ya aureki ba saboda baki da daraja a idanun shi, amma saboda irin son da yake miki he's ready to accept you" Hawaye ta share tana cewa, "Shikenan mom" "Good, yanzu ki zabi wadda kike so" karbar wayar hannun Mom tayi ta fara kallon gowns din. Simple gown ta zaba sannan ta bawa Mom wayar. " Kin tabbatar tayi miki? Kai ta gyaɗa alamar eh. "Good, then the shoes" Mom ta faɗa tana miƙa mata wayar. Nan ma zabar takalmin tayi sai jewelries da purse. Fita Mom tayi ta bar Noor cikin tunani.

*Nigeria*

        Jikin hydar yayi kyau sosai kuma yaji dad'i domin wajen ɗinkin ma ya ka me. Yana kwance dan bai daɗe da dawowa daga zagaye ba. Kamar kullum Mommy ce a gefan shi. Farce take gyara masa dan yau kwanan shi goma a asibiti kuma farcensa ya dan taru. Knocking tayi sannan ta shigo. Hydar na ganinta ta hade rai yana kallon abinda Mommy ke masa. " Ya jikin naka? Ta faɗa tana kallon shi. "Yaji sauki Alhmdll har zaki tafi ne? "No aikin yamma nazo ai da wuri zan tafi shiyasa kika ganni tun 12, ana yin sallar magariba zan tafi or even before ma tunda yau mu biyu ne" "Ayya, toh Allah yayi albarka" "Amin Mama" ta amsa tana karasowa. " Ina kuwa takwarata kanwar Raihan? Sai da Mommy tayi dariya me sauti kafin ta ce, "Matarsa ce kinga yayanta nan" ta ƙarashe maganar tana nuna Hydar. "Oh, ma sha Allah, toh shima Allah ya bashi ta gari, bari na duba ɗinkin shi" ta faɗa tana saka safa. Ganin babu discharge komai yayi dai² ya saka ta rufe tana cire gloves din ta ce, "idan likita yaxo zai iya baku sallama gobe" "Toh ma sha Allah haka ake so, mungode" da bakomai ta amsa sannan ta fita. Ƙaramin tsaki yaja yana faɗin, "Ta cika surutu" 'ai yafi, anfiso nurse ta kasance so friendly to her patients and patient relatives, ni ganin nake kamar Mami ta, yanayin jikinsu mu'amalar su har da shekarun, Allah sarki Mami, Allah ya jikanta" da Amin ya amsa yana kallon Mommy. Wa she gari kamar yadda ta faɗa likita daya zo round ya basu sallama tare da rubuta musu drugs. Haɗa kaya Mommy ta fara yi tana faɗin, "Ga shi ba zamu hadu yarinyar nan ba ƴar kirki wallahi" "Sai ki jirata tazo" ya faɗa yana kallonta. "Ai kai baka san mutunci ba, wanda zai nuna yana son naka ai me sonka ne" taɓe baki yayi bai ce komai ba. Raihan ne ya fitar da kayan zuwa mota sannan ya taimakawa Hydar suka nufi motar. Suna shirin fita Maama ta shigo, tsayawa Mommy ta saka Raihan yayi ta fito daga motar tana faɗin, "Kinga kuwa an sallame mu" murmushi tayi tana leka Hydar ta window ta ce, "Allah sarki, Allah ya kara lafiya" "Amin, mungode da kulawa, yar albarka, ni kuwa nace kina da aure? Kallonsu kawai Hydar da Raihan suke yi. " A'a Mama amma next year ne bikin in sha Allah" shuru Mommy tayi na yan dakiku kafin ta ce ma ta, "Ayya toh Allah ya sanya alkhairi, kinga da ace ba kowa ai dana baki hydar wallahi" murmushi kawai tayi. "Toh shikenan Allah ya biyaki yar albarka" da Amin ta amsa sannan ta wuce. Mota Mommy ta dawo tana faɗin, "Wallahi yar albarka, da ace ba aurenta za'ayi ba wallahi na maka sha'awarta tana da hankali wallahi" "dama jira nake ki fada kawai! Tunda naga kina sake mata haka na gane abinda kike nufi, thank God data ce miki tana da wanda take so" Juyowa tayi ta kalle shi tana faɗin, "Kai nake yi wa gata ai, sa'aninka harda me ɗa dan shekara 10, ga uwanka ma har yayi aure ya barka. "Mommy auren nan fa ba farilla bane, so babu laifi dan banyi ba ai ko? "Eh ba farilla bane ba Hydar amma cikar kamalar namiji ace yana da mata, idan kai kana jin daɗin zaman ka haka toh ni bana ji, idan ka kara jin sauki zaka je gidan Waheeda tana nan a zooroad kuje dan uwanka ya rakaka akwai first daughter dinta she's 27yrs a think, itama shuru Allah bai kawo ba, sai kaje ka ganta idan tayi maka" "27 tayi girma, 16-20 ya fi ko hydar? Cewar Raihan yana kallonsa ta mudubi. "I have no choice Raihan is better nayi auren ko zasu kyaleni" "Hakane amma I'm not advising you to date that child, iyayenta sun ɓata ta da shagwaba da kuɗi, yanzu ma haka bata daɗe da dawowa daga Hong Kong ba, ita kadai fa ta tafi" "Taje business ne, ku dinga kyautata zato mana, ai tana da kirki dan baka zauna da ita bane" cewar Mommy. "Dama za kiyi depending dinta ai" Raihan ya faɗa yana maida hankali sa a kan titi. "Shikenan toh, Allah ya fito masa da ta gari" da amin suka amsa gaba ɗaya.  Bayan sun  isa gida kwanciya Hydar yayi yana lumshe idanun shi, bacci yake sonyi amma hayaniya ta hana shi saboda yan dubiya. Ƙarfe biyar na yammacin ranar bayan Raihan ya gama goge masa jiki kiran Noor ya shigo wayar shi. Sai data kusa tsinkewa kafin ya ɗauka yana kallonta kamar yadda itama kallonsa take. "Are You sick? Ta faɗa a hankali. "Yau aka sallamoni daga asibiti" zaro idanunta tayi kaɗan tana kallon shi tace, "what's going on? "I'm ok now, ya kike? Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin, " I'm good, our wedding is next week so I called to invite you" kallonta yayi na ƴan dakiku kafin ya ce, " A Paris ɗin? "In sha Allah, and we're staying here even after our marriage" Kai ya gyaɗa sannan ya ce, "Allah ya sanya Alkhairi, ina Tahir ɗin? "He's quite busy with the wedding preparations nima na ɗan kwana biyu ban ganshi ba" "Ok" ya amsa mata. "Bye, k gaishe min da Ummi" da toh ya amsa sannan sukai sallama. Raihan dake kallon shi ya ce, "Noor is gone again! Maybe you're not destined to be married, Amma idan kuwa hakane na tausaya maka wallahi, kambu! Tabdijan" "Kai Dan Allah tashi ka fita" cewar Hydar yana nuna masa hanyar fita. "Ai ko baka ce ba, gwanda naje na ɗau matata na tafi dana tsaya anan, kai daba kasan daɗin aure ba sai kayi ta zama a gwauro, Allah sarki Hydar! Ya ƙarashe maganar yana ficewa. Tsaki hydar ɗin yayi tare da lumshe idanunsa.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now