Chapter four

73 4 2
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 4*

       Kiran ne ya katse bayan taji harbi har sau uku, da sauri ta fito daga ɗakinta gaba ɗaya ta rikice, Mom na falo tare da Saddeeqa dake harhaɗa kan utensils ɗin da Mom ta kammala cin abinci. "Juwairah ce Mom, ita ta kirani" Cewar Noor tana mikawa Mom wayarta. Karɓar wayar Mom tayi ganin babu alamar kira na tafiya ya saka ta faɗin "Ki kwantar da hankalin ki mana duk kin rikice" zama Noor tayi wani gumi na keto mata duk da  sanyin falon. Da kyar ta iya faɗin "Mom har harbi naji wallahi, Allah yasa kidnapper's ɗin basu kasheta ba" "harbi kuma? Cewar Mom cike da mamaki. Kai Noor ta gyaɗa alamar eh. Sai kuma ta mike tana kallon Mom ta ce, "Zan je gidan su ni da Tahir" bata jira cewar Mom ba ta nufi downstairs. "Noor! Noor!! Ki dawo ki saka hijabi! Mom ta fada tana kiranta. Noor kuwa hankalinta ya tashi ta manta cewa Nighties ne a jikinta. Kiran Tahir ta shiga yi bayan ta isa huge compound ɗin gidan. Da sauri ya fito dan dama bai nufi chan sashin su ba domin bai daɗe da dawowa daga wajen Dad ba. " Gidan su juwairah za muje " Ta faɗa tana kallon shi. Jikinta yabi da kallo yana dan shafa gashin kanshi ya ce, "A haka? "That's non of your business Tahir dauko mota" parking lot ya nufa ya dauko mota, jacket dinsa ya mika mata bayan sun shiga, bata ce komai ba ta karba ta saka, hannayenta duk sunyi sanyi zuciyarta sai tsananta bugu take... Tafiyar 30mins sukai sannan suka isa gidan su Juwairah, a compound din gidan ta tarar da Police karasawa tayi tana kallon ƙanin juwairah ta ce, "Ya ake ciki? "Juwairah ta kira she's in danger so now za'ayi tracing number " Cewar daddyn juwairah yana kallon Noor. "Nima ta kirani tana son faɗa min magana amma naji ƙarar bindiga dan Allah ku taimaka ku ceto kawata " Ta faɗa tana kallon police ɗin. "Yanzu zamu tafi batch ɗin farko already sun kusa isa wajen muna hoping kar su sauke layin kafin su karasa" Police ɗin ya faɗa yana kallon daddyn juwairah. "Zan biku" cewar Noor duk tayi wani iri. "No Noor ki koma gida in sha Allah she will be alright" daddyn juwairah ya faɗa yana dafa kafadarta. Bata ce komai ba ta fita, mota ta shiga ta na goge gumin da take. Motar police din ce ta fito da sauri ta kalli Tahir ta ce, "Bi bayansu" bai ce mata uffan ba ya tada mota yayi abinda ta ce. Tafiya sukai me tsaho kafin suga motar police din ta faka, suna tsayawa  Noor na fitowa... ɗaya daga cikin polisawan ne ya fito yana nufo motar su Noor "I'm juwairah's friend please ku taimaka ku kaini inda take dan Allah, that's why we were following you! Noor ta tare shi da sauri. Ya ganeta ita ce wadda ta shigo dazun suna magana da mahaifin victim din. "Ok amma ki tsaya cikin mota" da sauri ta ɗaga kai alamar toh. Mota ta koma tana kallon Tahir ta ce, "Muje" Sai da suka bar cikin gari sannan taga motar police ɗin ta tsaya, suna zaune cikin motar police din suka firfito, cikin ciyayin suka shiga an dau kusan 30mins Noor bata sake jin motsin kowa ba, buɗe motar tayi ta fito, shima Tahir fitowa yayi yana faɗin "koma mota Please" Bata kula shi ba ta nufi inda taga police din sunyi. Da sauri Tahir ya janyota yana faɗin "Kina so na rasa aikina? Kokarin kwatar kanta take amma ta kasa dan karfinsu ba daya ba. "How dare you touch me! Ta faɗa tana kallon shi. Sakinta yayi yana sunkuyar da kanshi ya ce, "My apology" gyara jacket dinsa tayi tana galla masa harara ta nufi cikin wajen. Fitilar wayarta take haska hanya dashi gaba daya ciyayi sun soke ta tun kafin taje ko ina. Tahir dake bayanta ya ce, "Dan Allah mu koma there is nothing you can do! Bata kula shi ba cigaba da tafiya. Karar bindinga taji da sauri ta juyo tana kallon Tahir cikinta na bada sautin kurrrrr. Kafin tayi wani move ta kuma jin ƙarar bindinga har sau biyu, a 360 tayo kan Tahir har suna neman faduwa. Ihu ta saka saboda abunda taji ya shige mata ƙafa zafin ya ratsa duk wani nerves na jikinta. Hannun Tahir ta rike, tana ƙoƙarin sake sakin wani ihun ya toshe mata baki. Ganin an hasko su da dalalleliyar fitila ya saka shi juya baya tare da Noor dake cikin azaba. Bindinga ya ciro a gefen takalmin sa getting ready to shoot at any moment. Hasken yaga ya dauke, dubansa ya mayar kan Noor dake ta zuba uban gumi. "Let's go! Ya faɗa yana jan hannunta. Wani karar ta kwallah tana ƙoƙarin faɗuwa. Fitilar wayarta ya karba yana haska ta ya ce, "What? "Na taka abu" Ta faɗa in so much pain. Kafarta ya haska, aikuwa sai jini take abunka da renon madara. Kaya ce me kauri kuwa, nunfashi ya sauke shi kam bai taɓa haɗuwa da mutum mai taurin kai irin Noor ba, da ta zauna a mota da duk wannan be faru ba. Ƙarar bindingu suka cigaba da ji, kafin ya ce wani abu Noor har ta kusa isa wajen mota, da sauri ya karasa ya buɗe mata motar ta shiga, shima shiga yayi yana yin reverse suka bar wajen a 360. Sai da suka shiga cikin gari ya tsaya yana kallonta ya ce, "Is better ki daina involving kanki a mess irin wannan! You are risking your life, stop interfering with political issues! Cike da azaba ta ce, "Cire min ƙayar dan Allah ka isheni! Ɗago masa kafar tayi tissue ya saka ya zareta da karfi, toshe bakinta tayi da sauri hawaye masu zafi na biyowa bisa kuncinta. Da tissue ɗin ya danne mata wajen zuwa minti daya sannan ya ce, "Bari muje pharmacy" bata ce komai ba shima bai ƙara magana ba, motar ya ja suka nufi pharmacy. Tare suka shiga pharmacyn saboda ayi mata dressing wajen. Sun ɓata time sosai kafin su fito, Tahir na rike da ledar maganinta. Mota ya buɗe mata ta shiga ya rufo. Window ta kallah ganin kamar Raihan ya fito daga pharmacyn shima. Ƙaramin tsaki tayi dan yanzu bata shi ma take ba, babban burinta yanzu taji halin da juwairah ke ciki.  Har suka isa gida hankalinta baya tare da ita. Tahir ne ya taimaka mata ta sakko, jacket dinshi ta cire tana faɗin "Ba sai kayi escorting dina ba thanks" da kallo ya bita har ta shige cikin entrance din da zai kaika cikin gidan, kallon jacket din hannunshi yayi kafin yayi murmushi yana barin wajen . Mom na zaune a falon ƙasa Noor ta shigo tana dingishi, da sauri ta karasa inda take tana kallon ƙafarta ta ce, "Me ya faru? Sai data taimaka mata ta zauna sannan ta ce "Ƙaya na taka, amma munje pharmacy" "Bakya jin magana ai, taurin kai ne dake kamar mahaifinki! Bazan taɓa faɗa miki magana ki saurareni ba! Nawa kike da zaki dinga involving kanki akan political issues ke ba namiji ba! Tunda bakya jin magana bari a kammala zaɓe sai kin koma wajen *FARIDA* Ɓata rai Noor tayi tana kallon mahaifiyarta ta ce, "Shikenan ni bazan dinga zama da iyayena ba? Kullum ni ce waccan ƙasar gobe waccan? Har gwanda Daddy ma akan ki, bamu da wani strong bond tsakanin mu, Ni dai babu inda zanje" ta karashe maganar tana kokarin mikewa. Mom ce ta taimaka maka suka nufi sama ta kaita ɗakinta, a gefanta ta zauna tana dafa kafadarta ta ce, " Ba wai bana so ki zauna damu bane, inaso amma nafi son lafiyarki, kwata² anan baki da tsaro kina gani dai kiri² farautar rayuwar mu ake kamar namun daji! Ga mahaifinki chan a asibiti ke ma gashi kafa ba lafiya, ki daina saka kanki cikin harkar siyasa if not abun bazai mana dad'i ba, kinyi ƙankanta kinji ko? Idanun Noor na zubar da hawaye ta ce, "Shikenan anyi kidnapping ɗin kawata sai in zauna? Na tabbatar da ni ce akai kidnapping sai in da karfin juwairah ya ƙare, toh meyasa ni bazan nemeta ba? Murmushi Mom ta danyi tana kallon ta tace, "Ok yanzu nemota kikai? Besides sai ma ciwo da kika jiyo! Lamarin sace²n nan fa yafi karfin tunaninki Noor! Just stay away from it please not for my sake for the sake of your well-being please" Kai ta gyaɗa a hankali alamar toh. "Yawwa ki sha drugs ɗin ki kwanta" da toh ta amsa sannan Mom ta tashi ta fita. Noor kuwa layin da juwairah ta kira ta dazu ta shiga kira amma aka sanar mata a kashe dole ta hakura ta kwanta.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now