Chapter Three

80 4 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 3*

         "A ina? Ya faɗa yana kafeta da idanun shi. "Abuja! Noor ta ba shi amsa idanunta cikin na shi. "Abuja a ina? Ya kuma faɗa yana kallonta. "Senator's office" murmushi ya ɗan yi yana kallon Hydar dake kallon su ya ce, "Mu tafi" "I'm not yet done! Ta faɗa tana riko hannun shi. Tsayawa yayi yana kallonta. Sakar masa hannu tayi tana sauke ajiyar zuciya ta ce, " Please tell me your identity? "I'm Raihan, what else? "Zan jiraka a mota" cewar Hydar yana nufar Mercedes ɗin da suka zo da ita. "Don't investigate too much Noor! Daga haka Raihan ya tafi ya barta. Da kallo tabi su, she wish ace da mota tazo yau da sai ta bisu taga inda Raihan yake, haka kawai taji bata yarda da Raihan ba, moreover menene relationship ɗinsa da Hydar? Ajiyar zuciya ta sauke tana nufar motar da suka zo ganin su juwairah na jiranta. Kai amarya suka tafi yi, basu dawo hotel ba sai 1 da ƴan mintuna. Wanka tayi sannan tayi sallah. Washegari da safe a matuƙar gajiye ta tashi, bayan tayi wanka tana breakfast kiran Mom ya shigo wayarta. Ɗauka tayi tare da sakawa a handsfree. "Good morning Mom" ta faɗa tana sauraren Mom. "Lafiya lau ya bikin? "Komai lafiya mun kai ta jiya". "Ma sha Allah, Allah ya basu zaman lafiya, Tahir zai zo kuje gidan su Sadeeq so ki shirya, ki miƙa musu gaisuwa na I'm quite busy I can't make it" "Ok shikenan bye " daga haka ta katse wayar. Kafin ta kammala cin abincin juwairah ta shigo tare da zama a kan couch ta ce, "Baki gama shiryawa ba? Flight ɗin 12pm ne fa! "Kuje kawai akwai inda Mom ta aikeni" "Ohk, ni kuwa Noor dama kinsan Hydar ne? Sai da Noor ta ɗago ta kalleta sannan ta bata amsa da "Ex boyfriend ɗina ne" "what? Ex boyfriend? Wayyyo Allah lallai ma Noor how can you dated such a handsome guy and broke up with him? Please how? Wallahi idan nice lallaɓa shi zan dinga yi kamar kwai" taɓa baki Noor tayi tana matsar da table ɗin gabanta tare da miƙewa tsaye idanunta a kan Juwairah ta ce, "Wallahi kwana daya kikai da Hydar sai ya ginsheki! Tabdijan kinsan waye Hydar kuwa? Ciwan zuciya kawai za ki yi wa kanki inviting in dai kika ce za ki yi dating ɗin Hydar" "Ko ma dae menene ni zan iya, if not Ina da tsayayye i could have date him" sai da Noor tayi dariya kafin ta ce, "Ke wallahi lokacinki ma bai da shi ballantana kuyi dating" "ok ke ta yaya ya ce yana sonki? "We met on Instagram yana yawan liking abubuwa na rannan naga sakonshi kinsan me ya ce? Kai juwairah ta girgiza alamar a'a. "Good job" shikenan fa! Ni kuma na masa reply da ok, yafi shekara da min wannan maganar kafin ya kuma min wata wai na turo masa account number yana son donating a orphanage ɗin da muka buɗe lokacin yana sabo, he donated 1.5m for the kids bayan nan munfi 6months lokaci² kuma yana donating wani abu a orphanage ɗin, kwatsam rannan naga voice message din shi just 6 second wai yana so mu haɗu, nayi fixing date, can you imagine yazo har Abuja just to say he likes the way I dressed! Kinga tun daga wannan he likes the way I dressed din babu abinda ya kuma cewa ya tafi to cut the long story munfi watanni a wannan kalmar kafin ya ce wai aurena yake son yi, mun fara dating da shi kamar abun arziki naga yana son sa min ciwan zuciya nace masa let's breakup da ok kawai ya amsa kwata² shifa be iya soyayya ba, magana ma baya son yi, kwanaki brother ɗin shi *ABDALLAH* yake faɗa min ya samu aiki a police, ko makiyina bana masa fatan samun mutum irin Hydar" Ta karashe maganar tana zama a kan gado. "Tab, ai shikenan, ni bari na wuce sai mun haɗu" Da ok Noor ta amsa sannan juwairah ta fita.

        Ƙarfe 1 na rana Tahir ya iso, a hotel ɗin ya sameta sannan suka wuce gidan su Sadeeq, tun da suka shigo layin gidan jikin Noor yayi sanyi, bayan Tahir yayi parking ya juyo yana kallonta ya ce, "Mun zo" da ok ta amsa tana fitowa. Kallon gidan tayi baza'a kirasu da marasa karfi ba kuma baza'a kirasu da masu kudi ba duba da yanayin gidan. Shiga soron gidan tayi tare da yin sallama. Amsawa akayi kafin ta ƙarasa. Matar dake zaune a tsakar gida ta zuba mata idanu tana faɗin "Ban shaidaki ba Hajiya" "Baki sanni ba daman, sunana Amina Alkasim yar gidan sanata wanda marigayi Sadeeq ke aiki a gidan su" "Ayya, sannu da zuwa yi haƙuri ga waje zauna" ta faɗa tana gyara mata tabarma. Zaunawa Noor tayi tana kallon matar data ke kyautata zaton maman Sadeeq ce. " Ya haƙuri? Cikin jimami matar ta amsa da "Da godiya ƴar nan, ai sanatan ma yazo da kanshi wallahi, mungode Allah ya saka da Alkhairi" "Amin Mama kuyi haƙuri duk da munsan bamu da bakin baku hakurin" cewar Noor tana kallonta. "Ba komai ƴar nan ai kowa na haka ne, kuma in sha Allah koma waye yake da hannu sai ya wulakanta" jikin Noor a sanyaye ta amsa da "In sha Allah, Mama ga wannan ni zan wuce" Ta ƙarashe maganar tana ajiye mata bandir biyu na 1k. Godiya ta dinga yi mata. Fitowa Noor tayi tana kallon Mercedes ɗin data faka yanzu a ƙofar gidan. Buɗe motar akayi Hydar ne ya fito hannunsa ɗauke da wata cute baby tana shan sweet. "Hydar! Ta kira sunan shi. Dubansa ya mayar gareta kafin ya kalli gidan data fito calmly ya ce, "Sannu" "Yawwa wannan baby girl  ɗin fa? "Cousin sister" ya faɗa yana ƙoƙarin wucewa. Bata ce dashi komai ba har ya shiga gidan su Mrgy Sadeeq. Mota ta koma tana kallon Tahir ta ce, "Zan saka wani aiki" "ok ina jinki" ya fada tare da mai da hankalin shi gareta. " Akwai wani ɗan aiken Daddy me suna Xexe inason more information on him" "Why? Cewar Tahir yana kallonta. " Kawai kayi abinda na ce" daga haka tayi relaxing a kujera. Tada motar yayi suka bar layin. Airport ya kaita sai da jirgin ta ya tashi sannan ya kamo hanyar ABUJA.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now