Chapter eight

55 4 1
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 8*

          Noor ce kwance Mom a gefenta tana faɗin "Ai sai ki tasoni kar ki ƙara kiran Tahir kinji ko? Noor na kuka ta amsa da toh. "Yawwa, yanzu Amina zata kawo miki abinci kici ko kaɗanne sai kiyi bacci ni zan fita" da toh ta amsa sannan Mom ta fita. Bata daɗe da fita ba Aminatu ta shigo tana faɗin "Ya jikin? Noor bata ce mata komai ba. Ajiye tray ɗin tayi tana faɗin"Ki tashi kici abinci Allah ya sauwake" daga haka ta fita. Da kallo tabi kofar ɗakin Noor! Allah na gani she try her best jiya, koma dae menene Noor is at fault! "Aminatu me kike anan? Cewar mom bayan ta fito cikin shirin fita.  "Ba komai yanzu na fito ne fa, fita za ki yi ne? "Eh, za'a kawo abincin danayi ordering ki zuba a warmers kinji ko? "Yo hajiya me kuwa warmers ana zaune ƙalau" cewar Aminatu tana dariya. "Kinga bana son shirme ina nufi kuloli, bazan daɗe ba, fitar ce ma ta zama dole" da toh ta amsa sannan ta ɗora da faɗin "A dawo lahiya" ajiyar zuciya ta sauke tana ciro wayarta a kugu, a kunne ta kara sai da aka ɗauka ta ce, "Dazu ka kira ina aiki" "Ya ake ciki? Aka faɗa daga ɗayen ɓangaren. " Everything is ok" "Are You sure? Dan banyi trusting wannan guy ɗin ba" cike da takaici Aminatu ta ce, "Eh I'm sure bye za muyi magana anjima" daga haka ta katse wayar! Noor kuwa zazzaɓi ne ya rufeta me zafi. Bayan Mom ta dawo likita aka kira ya dubata ya rubuta mata magani, Tahir Mom ta bawa prescription ɗin. Baƙin Daddy Mom taje suka gaisa sannan ta saka maids suka kai musu abinci. Bayan Tahir ya dawo direct ɗakin Noor ya nufa bayan ya shiga ya saka makulli tana kwance ta rufa da bargo. Ƙarasawa yayi yana taɓa goshinta. A hankali ta buɗe idanunta. Da sauri ta matsa ganinshi  a kanta. "Sorry Noor basan haka abun zai zama ba kiyi hakuri, tashi kisha maganinki" "Tahir I feel like I'm dying! The pain is something unimaginable" gefan fuskarta ya shafa cike da tausayinta ya ce, "Za kiji sauki in sha Allah" "Bayanni ka taba having affairs da wata? Unexpected yaji ta faɗa. Da sauri ya girgiza kai ya ce, "You are my first kuma my last in sha Allah" lumshe idanunta tayi zuciyarta na bugawa. " Sorry! Ya kuma faɗa yana kallonta. "I need to see a gynecologist Tahir the pain I'm feeling I don't think I can endure it" murmushi ya ɗanyi dan ta bashi dariya. "Zaki iya ki daure, you'r to tight that's why" harara ta ɓalla masa tana gyara kwanciyarta. "I'm serious I thought I can't get in at fi..."Tahir Please! Ta faɗa tana saurin katse shi. "Get well soon please, zamu tafi wani mission Noor pray for me" da sauri ta ɗago tana kallon shi ta ce, "Mission kuma? Shi daddyn ne ya tura ka? "Eh, amma kar kiyi masa magana idan na dawo sai in sake masa maganar auren mu" kai ta girgiza tana ƙoƙarin tashi zaune. "Relax please" Kai ta girgiza tana faɗin "Idan ka mutu a chan fa? Gaskiya bazan yarda ba, menene makomata ni kuma? Kusa da ita ya dawo yana faɗin " Bazan mutu ba sai na aureki insha Allah, nan da sati daya zan wuce Please take care of yourself" bata ce masa komai ba dan tabbas sai ta samu Daddy da maganar.  "Bari na je take care" da ok ta amsa sannan ya fita, luckily ba kowa hakan ya saka ya wuce abunsa. Da daddadare Noor na zaune a falonta domin ta ɗanji daɗin jikinta Aminatu ta shigo a kusa da kafafunta ta zauna tana faɗin " Ya jikin? "Da sauki dan Allah tashi kije sai da safe karki isheni" "Ba ruwana da ke kallo zan ɗanyi na rantse bazan ce miki uffan ba" Noor bata ce mata komai ta fara latsa wayarta. Nutsuwa ta yi ta fara kallo, chan ta juyo ta kalli Noor ta ce "Kinga wannan? Na tsane shi ya iya oba actin, daa shi da wancan ne jan rigar" "ke yanzu fahimtar abinda suke cewa kike? Kinzo kin dasa mbc 2 a gaba kina kallon masu jajayen kunnuwa kamar kinsan me suke cewa? "Inason Film ɗin yaƙi! Lokacin ina gidan mijina idan yana so in masa girki yana saka min a wayarsa na kalla, wayarsa kuwa irin taki me shafawa" ta ƙarashe maganar tana washe baki. Murmushi Noor tayi tana tashi tsaye. Zaro ido Aminatu tayi tana faɗin "Hajiyata al'ada kike fa! Da sauri Noor ta kalli kujerar data zauna, stain din jini ta gani, karamin tsaki tayi tana kallon Aminatu ta ce, "Ki goge" daga haka ta wuce dakinta. Toilet ta nufa ita dai tasan lokacin dawowar jininta beyi ba. Ruwan dumi ta kuma hadawa ta shiga. Bayan ta fito wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Tahir. Bayan ya dauka ta ce, "Ko dai zamu je asibiti ina tunanin na samu tear" "Tear kuma? Sai kace mai haihuwa Noor? Haɗe rai tayi kamar yana ganinta ta ce, "I'm serious, na faɗa maka ina jin zafi sosai kuma yanzu wajen yana dan fitar da jini Please ka fito muje" da ok ya amsa sannan ta kashe wayar. Hijabi ta saka ta fito, a mota ta same shi bayan sun fito daga gidan ya kalleta ya ce, "Muje gidana in kira likita ta dubaki baxan iya kai ki asibiti ba asirin mu zai iya tonuwa"  da ok ta amsa masa. Tafiya su kayi me tsaho sannan suka isa gidan shi, buɗewa yayi ya shiga da mota sannan ta fito. A bedroom ta zauna bayan ya ɗan gyara. Bata daɗe sosai ba midwife ɗin tazo har daki yayi escorting ɗinta. Tana kallon Noor ta ce, "Kwanta" "ka fita" cewar Noor tana kallon shi. Fita yayi ya basu waje, Safa ta saka bayan Noor ta kwanta. Dubata tayi taga tear ne dan kaɗan kuma daga waje ne kana ganin wajen kasan she's in pain. "Next time don't hold up your body kinji ko? Idan kika saki jikinki bazaki ji ciwo sosai ba, saboda kin ƙanƙanme jikin ki ya saka ya raunata ki, yanzu zan ɗinke ki saboda kin yage kinji ko? "Da zafi ko? Noor ta fada hawaye na taho mata. "Eh amma kadan, idan na ɗinke ki zaki fi jin daɗi, bayan ma ɗinkin ba yawa" da toh Noor ta amsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta dinketa tas. Tashi Noor tayi tana goge hawayen azaba. "Yawwa ki dinga tsarki da ruwan dumi akai² ki dinga saka gishiri kadan a ciki, ki kula da shi sosai zan masa magana ya daga miki kafa har ki warke kinji ko? Next time ki saki jikinki zakiji banbanci akwai drugs da zan rubuta ya siyo, take care please, next week zanzo na duba idan be warke ba wani zan sake miki is better ki kula dashi" da sauri ta ɗaga kai alamar toh.  Tare suka fito da Noor dake takawa da ƙyar. "Ga wannan drugs ɗin ka siya mata ta fara sha, Please kabi yar da mutane a hankali is like you use Force on her kuma she's young bana tunanin ta wuce 20yrs and Please ka kyaleta ta huta for about a week har ɗinkin ya warke" "Ok Nagode sosai" murmushi kawai tayi ta fita. Dubansa ya mayar kan Noor ya ce, "Sannu" "Dana san abinda zai faru kenan bazan zo ba daka kirani" "kiyi haƙuri dan Allah" bata ce masa komai ba ta zauna a kan kujera da ƙyar. "Wallahi Mom ganewa zatayi ko ka manta itama tama layin Health? Shafa kanshi yayi yana janyota jikinsa ya ce, "bazata gane ba, ki dinga zama a ɗaki da zummar baki warke ba har kiji daɗin jikin ki" "Tahir" ta kira sunan shi. "Yes! Ya amsa yana kallonta. "I don't think this is what all married women experience when having their first affairs" ni kuwa nace Are you guyx married 😏. "Ko wace mace da haka ta fara but as it continues zaki dena jin zafi You will start enjoying" barin jikinshi tayi tana goge hawayenta ta ce, "Bazai cigaba ba, baxan sake bari ba ai, i regret this one ma! "Nima bana fatan mu sake, from now on mu nemi yafiyar Ubangiji so that rayuwar auren mu tayi albarka". Kai ta gyaɗa alamar toh. "Mu tafi kar a fara nemanki" shi ya taimaka mata suka nufi mota. Bayan sun isa gida tana shiga gida ta tarar da Daddy da Mom a falonta.. tana ƙarasowa Daddy ya ɗauketa da mari, wani hazo² ta fara gani kafin tayi wani motsi ya kuma ɗauketa da wani marin. "Dan ubanki mutuncina zaki zubar? Uban menene wannan? Ya fada yana nuna mata videon hannunsa. Da kyar ta iya kallon wayar, ita da Tahir ne a mota yayi kissing ɗinta just light kiss  " da sauri ta ɗauke idanunta tana tunanin ta yaya aka samu videon nan. "Irin tarbiyyar dana miki kenan Noor? Abinda zaki saka min dashi kenan? Kai ta fara girgizawa tana kuka. "Kinsan videon yana ta yawo a internet? Nayi dana sanin haifarki wallahi! Da wani ido zan kalli jama'a? "Gaskiya Noor baki kyauta ba! Kuka take sosai tana kallon iyayen nata. "Best option ka ɗaura musu aure tunda dama daga gani tana sonshi idan yaso sai suyi video su bada haƙuri su nuna su ɗin ma'aurata ne kuma wani ne ya fitar da videon" "Hauka nake zan bawa Tahir auren ƴata? "Toh ya zakayi? Ka gwammace reputation ɗinka ya lalace? "Duk ba ita ta janyo ba? Duk abinda nake yi ina yi ne dan ganin na inganta rayuwarta amma da abinda zata saka min kenan?! Daga haka ya wuce ya barsu. "Kin kyautawa kanki ta yaya zaki bari namiji ya riƙeki yayi kissing ɗinki kinsan cewa ido a kan mu yake? Noor bata iya cewa komai ba saboda kuka. Wucewa Mom tayi a nan wajen Noor ta durƙusa tana kuka sosai. Ta daɗe a wajen kafin ta nufi ɗakinta. Wanka tayi tare da shirin bacci sannan ta ɗauko wayarta... Bata buɗe ko wani saƙo ba ta shiga kiran Tahir, bugu biyu ya ɗauka yana faɗin "Ya jikin? "Baka ga abinda ya faru ba? "Na gani Noor! Wani ne ya mana wannan vdn i have no clue on it, su Daddy fa? "Sun gani they just finished scolding me! Bansan me zai faru ba yanzu" "Karki damu, ai videon ba muni yayi ba after all yanzu zan saka a sauke shi a kowani platform kiyi haƙuri" kashe wayar tayi tana ajiyewa.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now